Ƙarin Bayani
a A jigon shekara ta 2019, an ba da dalilai uku da za su taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai a lokacin da munanan abubuwa suke faruwa a duniya ko kuma sa’ad da muke fuskantar matsaloli. A wannan talifin, za mu tattauna waɗannan dalilan kuma za su taimaka mana mu rage yin alhini. Ƙari ga haka, za su sa mu dogara ga Jehobah sosai. Ku riƙa yin bimbini a kan jigon. Ku yi ƙoƙari ku haddace shi. Zai ƙarfafa ku don matsalolin da za ku fuskanta a nan gaba.