Ƙarin Bayani
a Za mu riƙe aminci ga Jehobah kuwa ko za mu yarda Shaiɗan ya yaudare mu? Amsar tambayar nan ba ta dangana ga irin jarrabawar da muke fuskanta ba, amma ta dangana da yadda muke kiyaye zuciyarmu. Mene ne kalmar nan “zuciya” take nufi? Ta yaya Shaiɗan yake nema ya gurɓata zuciyarmu? Kuma ta yaya za mu iya kiyaye ta? Za a amsa tambayoyin nan a wannan talifin.