Ƙarin Bayani
d BAYANI A KAN HOTUNA: Taro a Majami’ar Mulki yana ba mu zarafin yin cuɗanya da ’yan’uwa. Mun ga (1) wani dattijo yana magana da wani matashi da mahaifiyarsa, (2) wani mahaifi da ’yarsa suna taimaka ma wata ’yar’uwa tsohuwa ta shiga mota, kuma (3) dattawa biyu suna saurarar wata ’yar’uwa da take neman taimako.