Ƙarin Bayani
a Mutanen da aka ci zarafinsu sa’ad da suke yara suna iya fuskantar ƙalubale sosai bayan shekaru da yawa. Wannan talifin zai taimaka mana mu fahimci dalilin. Za mu san irin mutanen da za su iya ƙarfafa su. Za mu kuma tattauna hanyoyin da za mu iya yin hakan.