Ƙarin Bayani
b MA’ANAR WASU KALMOMI: Cin zarafin yara shi ne sa’ad da wani babba ya yi amfani da yara don ya gamsar da sha’awarsa na yin jima’i. Hakan ya ƙunshi yin jima’i kai tsaye, ko yin jima’i ta baki ko ta dubura, ko tattaɓa al’aura ko mama ko kuma ɗuwawu da dai sauransu. Ko da yake an fi cin zarafin yara mata, amma ana cin zarafin yara maza da yawa ma. Maza sun fi cin zarafin yara, amma wasu mata ma suna cin zarafin yara.