Ƙarin Bayani
a Ko da mun yi shekaru muna bauta wa Jehobah, muna so mu ci gaba da manyanta da kuma inganta ibadarmu. Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci cewa kada su yi sanyin gwiwa! Wasiƙar da ya rubuta wa ’yan’uwan da ke Filibi tana ɗauke da abubuwan da za su ƙarfafa mu don mu ci gaba da jimrewa yayin da muke yin tseren nan na samun rai. Wannan talifin zai nuna mana yadda za mu bi shawarar Bulus.