Ƙarin Bayani
a A zamanin dā, Jehobah ya yi tanadin hanya ta musamman da Isra’ilawa za su sami ’yanci. Kiristoci ba sa bin dokar da Allah ya ba Isra’ilawa, amma za mu iya koyan darasi daga bikin samun ’yanci da suka yi. A wannan talifin, za mu ga yadda bikin samun ’yanci da Isra’ilawa suka yi zai tuna mana tanadin da Jehobah ya yi da kuma yadda za mu amfana daga tanadin.