Ƙarin Bayani
a Sashe na biyu na littafin Korintiyawa na 1 sura 15 yana ɗauke da bayanai game da yadda za a ta da matattu, musamman ma shafaffun Kiristoci. Amma abin da Bulus ya rubuta yana da muhimmanci ga waɗansu tumaki. Wannan talifi zai nuna yadda begen tashin matattu zai shafe mu yanzu da kuma yadda zai taimaka mana mu yi farin ciki a nan gaba.