Ƙarin Bayani
a Namiji yana zama shugaban iyali sa’ad da ya yi aure. A wannan talifin, za mu tattauna abin da zama shugaba yake nufi, da dalilin da ya sa Jehobah ya kafa wannan tsarin da kuma abin da mazaje za su koya daga misalin Jehobah da Yesu. A talifi na biyu a wannan jerin talifofin, za mu tattauna abin da mata da miji za su iya koya daga misalin Yesu da kuma wasu bayin Allah. A talifi na ƙarshe kuma, za mu tattauna game da shugabanci a ikilisiya.