Ƙarin Bayani
a Jehobah ya yi alkawari a cikin Kalmarsa cewa zai ƙarfafa mu, kuma zai kāre mu daga kowane abu da zai iya ɓata dangantakarmu da shi da kuma jawo mana lahani na dindindin. Za mu amsa tambayoyin nan a wannan talifin: Me ya sa muke bukatar Jehobah ya kāre mu? Ta yaya Jehobah yake kāre mu? Me ya wajaba mu yi don Jehobah ya kāre mu?