Ƙarin Bayani
a Da yake mu ajizai ne, za mu iya faɗa ko yi abin da zai ɓata wa ’yan’uwanmu rai. Me ya kamata ka yi idan hakan ya faru? Kana yin iya ƙoƙarinka don ka sasanta da wanda ya ɓata maka rai? Kana neman gafararsa ba tare da ɓata lokaci ba? Idan wani yana fushi da kai, za ka ce hakan ruwansa ne? Idan kuma kana saurin fushi fa? Kana ba da hujja ta wajen cewa haka kake? Ko kuma ka fahimci cewa kana bukatar ka canja halinka?