Ƙarin Bayani
a Muna ƙaunar Jehobah sosai, kuma muna so mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimar da muke masa. Shi ya sa da yawa a cikinmu suna so su daɗa yin ƙwazo a wa’azi, ko kuma su sami ƙarin ayyuka a ikilisiya. Amma idan mun kasa cim ma wasu maƙasudai duk da cewa mun yi iya ƙoƙarinmu fa? Ta yaya za mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu kuma mu yi farin ciki? Za mu sami amsar a kwatancin kuɗin zinariya da Yesu ya bayar.