Ƙarin Bayani
a Tuban gaske ya wuci mutum ya ba da haƙuri don laifin da ya yi. A wannan talifin, za a tattauna misalin Sarki Ahab da Sarki Manasse da ɗa mubazzari na kwatancin Yesu, don a taimaka mana mu fahimci abin da tuban gaske yake nufi. Za mu kuma ga abubuwan da dattawa za su yi la’akari da su don su san ko wanda ya yi zunubi ya tuba da gaske.