Ƙarin Bayani
b BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa matashi mai suna Dan, ya ga yadda dattawa biyu suka kawo wa babansa ziyara a asibiti. Ƙaunar da dattawan suka nuna wa baban Dan ya sa Dan ya nemi hanyoyin taimaka ma ’yan’uwa a cikin ikilisiya. Wani ɗan’uwa matashi mai suna Ben kuma ya ga yadda Dan yake kula da ’yan’uwa a ikilisiya. Misalin Dan ya sa Ben ya soma taimakawa ta wajen yin shara a Majami’ar Mulki.