Ƙarin Bayani
a Timoti ya ƙware sosai a yin wa’azin Mulkin Allah. Duk da haka, manzo Bulus ya ƙarfafa shi ya ci gaba da kyautata yadda yake bauta wa Jehobah. Da yake Timoti ya bi shawarar Bulus, Jehobah ya daɗa amfani da shi kuma Timoti ya iya taimaka ma ’yan’uwansa Kiristoci sosai. Shin kai ma kana so ka bauta ma Jehobah da kyau kuma ka taimaka ma ’yan’uwanka kamar Timoti? Babu shakka, kana so ka yi hakan. Waɗanne maƙasudai ne za su iya taimaka maka ka yi hakan? Kuma me kake bukatar ka yi don ka iya kafa da kuma cim ma maƙasudan?