Ƙarin Bayani
a Sulemanu da Yesu sun kasance da hikima sosai. Allahnmu Jehobah ne ya ba su hikimar. A wannan talifin, za mu tattauna darussan da za mu iya koya daga shawarwari da Sulemanu da Yesu suka bayar a kan yadda za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi da aikinmu da kuma kanmu. Za mu kuma ga yadda ’yan’uwanmu suka amfana domin sun bi shawarar Littafi Mai Tsarki a fannonin nan.