Ƙarin Bayani
e BAYANI A KAN HOTO: John yana zarce lokaci a wurin aiki. Yana so ya burge ogansa a wurin aiki. Don haka, a duk lokacin da ogansa ya ce masa ya yi aiki har dare, yakan yarda da hakan. A yammar, Tom wanda bawa mai hidima ne, ya ziyarci wata ’yar’uwa tare da wani dattijo don su ƙarfafa ta. Tun dā ma, Tom ya gaya wa ogansa a wurin aiki cewa ba zai riƙa yin aiki da yamma a wasu ranaku ba domin yana amfani da lokacin ya yi ayyukan ibada.