Ƙarin Bayani
a Akwai miliyoyin maza da mata da yara da suke yin wa’azin Mulkin Allah da ƙwazo. Kana cikinsu? Idan haka ne, kana bin ja-gorancin Ubangijinmu Yesu Kristi. A wannan talifin, za mu ga abin da ya tabbatar mana cewa Yesu yana yi mana ja-goranci a wa’azin da muke yi a yau. Yin tunani a kan abin da za mu tattauna zai taimaka mana mu ƙuduri niyyar ci gaba da bauta wa Jehobah a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu.