Ƙarin Bayani
a A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da Jehobah yake taimaka wa bayinsa su iya jimre matsaloli da farin ciki. Za mu ga hanyoyin nan da Jehobah yake taimaka mana ta wajen bincika littafin Ishaya 30. Yayin da muke tattauna wannan surar, za mu ga muhimmancin yin adduꞌa ga Jehobah da yin nazarin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki, da kuma yin bimbini a kan albarkun da Allah ya ba mu a yanzu da waɗanda za mu samu a nan gaba.