Ƙarin Bayani
a Jigon da aka zaɓa na shekara ta 2023 zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Jigon shi ne: “Tushen maganarka gaskiya ne.” (Zab. 119:160, New World Translation) Babu shakka ka gaskata da maganar nan. Amma mutane da yawa ba su gaskata da Littafi Mai Tsarki ba, kuma ba su yarda cewa zai iya ba mu shawarwari masu kyau ba. A wannan talifin, za mu bincika dalilai uku da za mu iya amfani da su don mu tabbatar wa masu zuciyar kirki cewa za su iya gaskata da Littafi Mai Tsarki da shawarar da ke cikinsa.