Ƙarin Bayani
a Muna jin daɗin karanta game da muꞌujizan da Yesu ya yi. Alal misali, ya dakatar da guguwa mai ƙarfi, ya warkar da marasa lafiya, har ya ta da matattu. An rubuta waɗannan labaran a Littafi Mai Tsarki ba don su nishaɗantar da mu ba amma don su koya mana darussa. Yayin da muke bincika su, za mu koyi darussa masu ban ƙarfafa game da Jehobah da Yesu da kuma halaye masu kyau da ya kamata mu kasance da su.