Ƙarin Bayani
c Littafin Linjila yana ɗauke da muꞌujizai fiye da 30 da Yesu ya yi. Yesu ya yi ƙarin wasu muꞌujizai da yawa, amma Littafi Mai Tsarki ya ambace su tare maimakon ɗaya bayan ɗaya. Akwai wani lokacin da “dukan mutanen garin” suka zo wurin sa kuma “ya warkar da marasa lafiya da yawa.”—Mar. 1:32-34.