Ƙarin Bayani
a A littafin 1 Tasalonikawa sura 5, an yi kwantanci dabam-dabam da suke koya mana game da ranar Jehobah da za ta zo a nan gaba. Me ake nufi da “ranar,” kuma ta yaya za ta zo? Su wane ne za su tsira? Su wane ne ba za su tsira ba? Ta yaya za mu zauna da shiri don wannan ranar? Za mu bincika abin da manzo Bulus ya faɗa kuma mu amsa tambayoyin nan.