Ƙarin Bayani
b A lokacin, Ɗanꞌuwa J. F. Rutherford ne yake ja-gorantar Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin. Kuma ana kiransa Judge Rutherford. Me ya sa ake kiransa “Judge”? Domin kafin ya soma hidima a Bethel, ya taɓa yin aiki a matsayin alƙali na musamman a wani kotu da ake kira Eighth Judicial Circuit Court of Missouri.