Ƙarin Bayani
a A littattafan Linjila da ma wasu littattafai, an yi magana game da lokacin da Yesu ya bayyana ga mutane dabam-dabam. Alal misali: Maryamu Magadaliya (Yoh. 20:11-18); wasu mata (Mat. 28:8-10; Luk. 24:8-11); almajiransa 2 (Luk. 24:13-15); Bitrus (Luk. 24:34); almajiransa ban da Toma (Yoh. 20:19-24); almajiransa tare da Toma (Yoh. 20:26); almajiransa 7 (Yoh. 21:1, 2); almajiransa fiye da 500 (Mat. 28:16; 1 Kor. 15:6); ɗanꞌuwansa Yaƙub (1 Kor. 15:7); dukan manzaninsa (A. M. 1:4); manzaninsa kusa da Betani. (Luk. 24:50-52) Wataƙila ma ba a rubuta wasu wuraren da ya bayyana ba.—Yoh. 21:25.