Jumma’a, 18 ga Yuli
Ya mai da mu mu zama masu mulki da firistoci masu hidimar Allah Ubansa.—R. Yar. 1:6.
An shafe wasu mabiyan Yesu Kristi da ruhu mai tsarki, kuma suna da dangantaka ta musamman da Jehobah. Waɗannan shafaffu guda 144,000 za su yi hidima a matsayin firistoci tare da Yesu a sama. (R. Yar. 14:1) Wuri Mai Tsarki da ke cikin mazaunin yana wakiltar matsayinsu na ꞌyaꞌyan Allah ko da yake suna duniya. (Rom. 8:15-17) Wuri Mafi Tsarki kuma yana wakiltar sama inda Jehobah yake. “Labulen” da ya raba tsakanin wuri Mai Tsarki da Mafi Tsarki yana wakiltar jikin Yesu. Saꞌad da yake duniya, da yake yana da jiki irin na ꞌyan Adam, ba zai iya zuwa sama don ya yi hidima a matsayin Babban Firist a haikalin Jehobah ba. Da ya mutu, ya ba da jikinsa a matsayin hadaya, kuma hakan ya buɗe wa shafaffu hanyar zuwa sama. Amma kafin su iya zuwa sama, wajibi ne su ma su rabu da jikinsu na ꞌyan Adam.—Ibran. 10:19, 20; 1 Kor. 15:50. w23.10 28 sakin layi na 13
Asabar, 19 ga Yuli
Ba ni da zarafi in yi zance a kan Gideyon.—Ibran. 11:32.
Gideyon bai yi fushi ba da mutanen Ifrayim suka kushe shi. (Alƙa. 8:1-3) Ya amsa musu a hankali. Yadda ya saurare su ya nuna cewa shi mai tawaliꞌu ne, kuma ya yi maganar da za ta kwantar musu da hankali. Dattawa masu hikima suna bin halin Gideyon. Sukan saurari mutum da kyau, kuma idan aka kushe su, sukan faɗi alheri. (Yak. 3:13) Ta yin hakan, suna ƙara sa ikilisiya ta zauna lafiya. Da aka yabi Gideyon don nasarar da ya yi a kan mutanen Midiyan, ya miƙa yabon ga Jehobah. (Alƙa. 8:22, 23) Ta yaya dattawa za su bi halin Gideyon? Idan aka yabe su don wani abin da suka yi, zai dace su miƙa yabon ga Jehobah. (1 Kor. 4:6, 7) Misali, idan aka yabi dattijo don yadda yake koyarwa, zai iya cewa abin da ya koyar daga Kalmar Allah ne, kuma koyawar da muke samu daga ƙungiyar Jehobah ce take taimaka wa dukanmu. Wani lokaci, zai dace dattawa su yi tunani ko suna yin abubuwa don su jawo hankalin mutane gare su. w23.06 4 sakin layi na 7-8
Lahadi, 20 ga Yuli
Tunanina ba kamar tunaninku ba ne.—Isha. 55:8.
Idan ba mu samu abin da muka roƙa ba, zai dace mu tambayi kanmu cewa, ‘Abin da nake adduꞌa a kai ya dace kuwa?’ A yawancin lokuta, mukan ɗauka cewa mun san abin da ya dace da mu. Amma mai yiwuwa abubuwan da muka roƙa ba su ne za su amfane mu ba. Idan muna fuskantar matsala, mai yiwuwa ba abin da muka roƙi Jehobah ya yi mana ne zai warware matsalar ba. Kuma ƙila wasu abubuwan da muka roƙa ba su jitu da nufin Jehobah ba. (1 Yoh. 5:14) Alal misali, a ce iyaye sun roƙi Jehobah ya sa yaronsu ya ci-gaba da bauta masa. Za mu iya ganin cewa roƙo mai kyau ne suka yi. Amma Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Yana so dukanmu har da yaranmu mu bauta masa da son ranmu. (M. Sha. 10:12, 13; 30:19, 20) Don haka, abin da ya kamata iyayen su roƙa shi ne, Jehobah ya taimaka musu su iya ratsa zuciyar yaronsu don ya ƙaunace Shi kuma ya bauta masa.—K. Mag. 22:6; Afis. 6:4. w23.11 21 sakin layi na 5; 23 sakin layi na 12