WAƘA TA 76
Yin Wa’azi Yana Sa Mu Murna
(Ibraniyawa 13:15)
1. Yaya kuke ji ne
in kun je yin wa’azi
Kuma da ƙwazo kuka
yi shelar Mulkinsa?
Ku yi ƙoƙarinku,
Allah zai taimake ku
Don shi ya san mutanen
da suke ƙaunar sa.
(AMSHI)
Idan muka yi wa’azi
yana sa mu murna sosai.
Bari mu riƙa yabon sa
kullum har abada.
2. Yaya kuke ji ne
in waɗanda suke jin
Tsoron Allah suna jin
daɗin wa’azinku?
Wasu za su ƙi ji,
wasu za su bijire.
Duk da haka ba za mu
daina wa’azi ba.
(AMSHI)
Idan muka yi wa’azi
yana sa mu murna sosai.
Bari mu riƙa yabon sa
kullum har abada.
3. Yaya kuke ji ne
idan kun tuna cewa
Allah na tare da ku
don ku yi aikinsa?
In muna wa’azi
mu ƙoƙarta mu ratsa
Zuciyar mutanen da
muke wa wa’azi.
(AMSHI)
Idan muka yi wa’azi
yana sa mu murna sosai.
Bari mu riƙa yabon sa
kullum har abada.
(Ka kuma duba A. M. 13:48; 1 Tas. 2:4; 1 Tim. 1:11.)