WAƘA TA 118
Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”
Hoto
1. Domin ajizancinmu, Ya Jehobah,
Muna yawan karya dokokinka.
Abin da ke yawan jawo zunubi
Shi ne rashin nuna bangaskiya.
(AMSHI)
Ƙarfafa bangaskiyarmu, Ya Allah.
Taimake mu muna bukatar ta.
Ƙarfafa bangaskiyarmu Jehobah
Don mu riƙa yin nufinka kullum.
2. Sai da bangaskiya za mu bauta ma.
Mun san za ka yi mana albarka.
Ya Allahnmu, muna son taimakonka
Don mu riƙa jimrewa har ƙarshe.
(AMSHI)
Ƙarfafa bangaskiyarmu, Ya Allah.
Taimake mu muna bukatar ta.
Ƙarfafa bangaskiyarmu Jehobah
Don mu riƙa yin nufinka kullum.
(Ka kuma duba Far. 8:21; Ibran. 11:6; 12:1.)