WAƘA TA 84
Yin Hidima a Inda Akwai Bukata
Hoto
1. Jehobah ya san mu sosai,
Yana so mu riƙa murna.
Yana nuna mana yadda
Za mu bi da rayuwarmu.
(AMSHI)
Muna yi wa Allah
hidima kullum.
A dukan wurare, za mu je
mu yi wa’azi.
2. Akwai aiki a ko’ina,
Muna zuwa mu taimaka.
Ta yin hakan, muna nuna
Cewa muna son su sosai.
(AMSHI)
Muna yi wa Allah
hidima kullum.
A dukan wurare, za mu je
mu yi wa’azi.
3. A birane da ƙauyuka
Muna zuwa yin wa’azi.
Muna koyan sabon yare
Domin mu yi wa’azi nan.
(AMSHI)
Muna yi wa Allah
hidima kullum.
A dukan wurare, za mu je
mu yi wa’azi.
(Ka kuma duba Yoh. 4:35; A. M. 2:8; Rom. 10:14.)