Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/1 p. 8
  • Wane Ne Ya Yi Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wane Ne Ya Yi Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Allah yana da mafari kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Za Mu Iya Yin Rayuwa Har Abada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Mahalicci da Ya Cancanci Mu Yabe Shi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Wane ne Allah?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/1 p. 8

MASU KARATU SUN YI TAMBAYA . . .

Wane ne ya yi Allah?

A ce wani mahaifi yana magana da ɗansa mai shekara bakwai. Mahaifin ya ce, “Shekaru aru-aru da suka gabata, Allah ya halicci duniya da abubuwan da ke cikinta da rana da wata da kuma taurari.” Da yaron ya ɗan yi tunani sai ya yi tambaya, “Baba, wane ne ya yi Allah?”

Mahaifin ya amsa cewa: “Babu wanda ya yi Allah, domin Allah ba shi da mafari da kuma ƙarshe.” Wannan amsar ta gamsar da yaron a lokacin. Amma yayin da yaron yake girma, wannan tambayar ta ci gaba da damunsa. Ya kasa fahimtar abin da ya sa za a ce wani ba shi da mafari, domin sararin samaniya ma yana da mafari. Hakan ya sa yaron ya riƙa tunani, ‘Daga ina ne Allah ya fito?’

Me amsar Littafi Mai Tsarki a kan wannan tambayar? Amsar ɗaya ce da wadda mahaifin nan ya ba ɗansa. Musa ya rubuta cewa: ‘Ya Ubangiji, . . . Kafin a kafa tuddai, kafin kuma ka sa duniya ta kasance, kai Allah ne, madawwami.’ (Zabura 90:1, 2, Littafi Mai Tsarki) Hakazalika, annabi Ishaya ya ce: ‘Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya’! (Ishaya 40:28, LMT) Hakazalika, wasiƙar Yahuda ta ce Allah ya wanzu “tun gaban zamanai duka.”—Yahuda 25.

Waɗannan nassosin sun nuna cewa Allah ne “Sārkin zamanai [‘madawwanin sarki,’ New World Translation],” kamar yadda manzo Bulus ya kwatanta shi. (1 Timotawus 1:17) Ma’ana, babu lokacin da Allah bai wanzu ba, kuma ba zai daina wanzuwa ba. (Ru’ya ta Yohanna 1:8) Saboda haka, irin wanzuwarsa tana ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa shi ya zama Maɗaukaki.

Me ya sa wannan batun yake da wuyan fahimta? Domin ba za mu iya fahimtar batun lokaci kamar Jehobah ba, da yake muna da ƙanƙantar tsawon rayuwa. Allah madawwami ne, saboda haka shekara dubu kamar kwana guda ne a gare shi. (2 Bitrus 3:8) Alal misali, ƙwaro da ke rayuwa kwanaki 50 kawai zai iya fahimtar tsawon ran ɗan Adam na shekaru 70 ko 80? A’a. Ga shi Littafi Mai Tsarki ya ce idan aka kwatanta mu da Mahaliccinmu, muna kama da ƙwari ne. Kuma idan aka gwada fahiminmu da nasa, ko kusa ba zai yi ba. (Ishaya 40:22; 55:8, 9, LMT) Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa akwai wasu abubuwa game da Jehobah da ɗan Adam ba zai iya fahimta ba.

Ko da yake ba za mu iya fahimtar irin wanzuwar Allah ba, wannan koyarwar ta yi daidai. Idan wani ne ya halicci Allah, to shi ɗin ne zai zama Mahalicci. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ne ya “halicci dukan abu.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Ƙari ga haka, mun san cewa akwai lokacin da sararin samaniya bai wanzu ba. (Farawa 1:1, 2) Daga ina ya fito? Kafin a iya halittarsa, wajibi ne Mahaliccinsa ya wanzu kafin shi ma ya wanzu. Ƙari ga haka, wannan Mahaliccin ya wanzu kafin sauran halittu kamar mala’iku da kuma Ɗansa tilo. (Ayuba 38:4, 7; Kolosiyawa 1:15) Hakika, Allah ya wanzu kafin kome. Ba a halicce shi ba, babu abin da ya wanzu kafin shi da zai halicce shi.

Wanzuwarmu da kuma na sararin samaniya ya nuna cewa akwai Allah madawwami. Hakika, Wanda ya kafa sararin samaniya da kuma abin da ke sarrafa ta, ya wanzu a kowane lokaci. Saboda haka, shi kaɗai ne zai iya ba da rai ga dukan abubuwa.—Ayuba 33:4.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba