Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 3/1 pp. 8-9
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 3/1 pp. 8-9

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Suna so in gano wa kaina gaskiyar Littafi Mai Tsarki”

Luis Alifonso ne ya ba da labarin

  • SHEKARAR HAIHUWA: 1982

  • ƘASAR DA AKA HAIFE SHI: DOMINICAN REPUBLIC

  • TARIHI: ƊAN ADDININ MORMON A DĀ

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni ne a Santo Domingo, babban birnin ƙasar Dominican Republic. Mu yara huɗu ne a gidanmu kuma ni ne ɗan auta. Iyayena masu ilimi ne da suka so su yi rainon ’ya’yansu cikin mutane masu kirki. Shekaru huɗu kafin haihuwata iyayena suka haɗu da ’yan mishan na addinin Mormon. Sa’ad da suka lura da yadda samari ’yan mishan ɗin suka yi ado da kyau kuma suka nuna ladabi, sai iyayena suka yanke shawarar zama mabiya cocin Mormon, wato, Church of Jesus Christ of Latter-day Saints. Iyalinmu ne suka fara zama ’yan Mormon a birnin.

Yayin da nake girma, na ji daɗin yadda ake shaƙatawa a cocin kuma na so yadda addinin Mormon yake mai da hankali ga rayuwar iyali da kuma tarbiyya. Na yi farin ciki cewa ni ɗan addinin Mormon ne kuma na yanke shawarar zama ɗan mishan.

Sa’ad da nake ɗan shekara 18, sai muka ƙaura zuwa Amirka don iyayena suna son in ci gaba da karatu a jami’a mai kyau. Shekara ɗaya bayan haka, ƙanwar mahaifiyata da mijinta waɗanda Shaidun Jehobah ne, suka kawo mana ziyara a Florida. Sai suka gayyace mu zuwa wani babban taro inda ake koyar da Littafi Mai Tsarki. A wurin taron, na lura cewa kowa yana karanta Littafi Mai Tsarki sa’ad da aka ambata wani nassi kuma suna rubuta abin da mai jawabin yake faɗa. Saboda haka, na nemi ’yar takarda da biro kuma na soma rubutu.

Bayan taron, ƙanwar mahaifiyata da mijinta suka ce za su koya mini Littafi Mai Tsarki tun da ina son in zama ɗan mishan. Sai na yarda don a lokacin, ban san Littafi Mai Tsarki sosai kamar yadda na san Littafin Mormon ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

A lokatan da muke tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki ta waya, ƙanwar mahaifiyata da mijinta suna yawan gaya min cewa in bincika ko abubuwan da na gaskata sun jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki. Suna so in gano wa kaina gaskiyar Littafi Mai Tsarki.

Akwai abubuwa da yawa game da addinin Mormon da na gaskata da su, amma ban tabbata ko sun jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Ƙanwar mahaifiyata ta aika min mujallar Awake! na 8 ga Nuwamba 1995, wanda Shaidun Jehobah suka wallafa. Wannan mujallar tana ɗauke da wasu talifofi game da koyarwar addinin Mormon. Da na karanta, na sha mamaki cewa akwai wasu koyarwa da yawa na addinin Mormon da ban sani ba. Wannan abin ya sa na yi bincike a dandalin intane na addinin Mormon game da bayanin da ke Awake! ɗin. Sai na tarar cewa gaskiya ne, kuma na ƙara tabbatar da hakan sa’ad da na ziyarci gidajen kayayyakin tarihin addinin Mormon da ke jihar Utah.

A dā, na ɗauka cewa abin da ke cikin Littafin Mormon da na Littafi Mai Tsarki ɗaya ne. Amma, da na fara karanta Littafi Mai Tsarki cikin natsuwa, sai na ga cewa koyarwar addinin Mormon sun saɓa wa wasu abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Alal misali, littafin Ezekiyel 18:4 ya ce kurwa tana mutuwa. Amma Alma 42:9 da ke Littafin Mormon ya ce: “Kurwa ba ta taɓa mutuwa.”

Ban da waɗannan koyarwar da suka saɓa wa Littafi Mai Tsarki, addinin Mormon yana goyon bayan kishin ƙasa kuma ban ji daɗin hakan ba. Alal misali, ana koya wa ’yan addinin Mormon cewa a dā lambun Adnin yana garin Jackson County da ke jihar Missouri ne, a ƙasar Amirka. Kuma shugabannin cocin suna koya wa mabiyansu cewa sa’ad da Mulkin Allah ta soma sarautar duniya, zai yi hakan ne ta gwamnatin ƙasar Amirka.

Sai na fara tunani cewa idan hakan gaskiya ne, me zai faru da sauran ƙasashe, har da ƙasar haihuwata? Sa’ad da wani matashi ɗan addinin Mormon da yake son ya zama ɗan mishan ya kira ni a waya wata rana, sai na ta da zancen. Na fito ɓaro-ɓaro na tambaye shi ko zai yarda ya yaƙi ’yan’uwansa, wato, ’yan addinin Mormon da ke wata ƙasa idan ƙasarsa tana yaƙi da su. Na sha mamaki sa’ad da ya ce, E! Sai na ƙara bincika koyarwar addinina kuma na yi wa manyan shugabannin addinin Mormon tambayoyi. Sun gaya mini cewa abin da nake son in sani gaibi ne kuma ba zan iya samun cikakken bayani game da shi yanzu ba.

Wannan bayanin ya kashe min jiki, sai na sake yin tunani a kan ainihin dalilin da ya sa nake son na zama ɗan mishan. Na gano cewa ina son in zama ɗan mishan domin in taimaka wa mutane. Wani dalili kuma da ya sa nake sha’awar zama ɗan mishan shi ne domin mutane su girmama ni. Amma a gaskiya ban san Allah yadda ya kamata ba. Ko da yake na karanta Littafi Mai Tsarki sau da yawa a dā, ban ɗauke shi da muhimmanci ba. Ban san kome game da nufin Allah ga duniya ko ’yan Adam ba.

YADDA NA AMFANA:

Ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, na gane sunan Allah, abin da ke faruwa sa’ad da muka mutu, matsayin Yesu a cikar nufin Allah, da dai sauran su. Na soma fahimtar abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma na ji daɗin gaya wa mutane abin da nake koya. Tun da daɗewa na san cewa Allah ya wanzu, amma ban ɗauke shi a matsayin aboki na kud da kud da zan tattauna da shi ba. Amma yanzu ina magana da shi cikin addu’a kamar Aminina. Na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah a rana ta 12 ga Yuli, 2004, bayan wata shida, na soma wa’azi na cikakken lokaci.

Na yi hidima na tsawon shekaru biyar a hedkwatar Shaidun Jehobah a Brooklyn na birnin New York. Na ji daɗin taimakawa wajen buga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da miliyoyin mutane a faɗin duniya suna amfana daga karanta su. Kuma har wa yau, ina taimaka wa mutane su koya game da Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba