WAƘA TA 32
Mu Kasance da Aminci ga Jehobah!
(Fitowa 32:26)
- 1. Muna yabon ka Jehobah Allah, - Don yanzu muna biyayya da kai. - Mun sami ʼyanci da kuma ceto, - Daga Babila Babba. - (AMSHI) - Mu bauta wa Allah, Allah Jehobah. - Zai taimaka mana Mu bi haskensa. - Mu gaya wa kowa Bisharar ’yanci. - Mulkin Yesu Kristi, Za ya dawwama. 
- 2. Muna goyon bayan Mulkin Allah. - Muna bishara a duk duniya. - Yanzu ne lokaci na yin zaɓi, - Zaɓin bauta wa Allah. - (AMSHI) - Mu bauta wa Allah, Allah Jehobah. - Zai taimaka mana Mu bi haskensa. - Mu gaya wa kowa Bisharar ’yanci. - Mulkin Yesu Kristi, Za ya dawwama. 
- 3. Ba ma jin tsoron dabarun Shaiɗan, - Domin Jehobah zai kiyaye mu. - Ko da maƙiya sun fi mu yawa, - Mun dogara ga Allah. - (AMSHI) - Mu bauta wa Allah, Allah Jehobah. - Zai taimaka mana Mu bi haskensa. - Mu gaya wa kowa Bisharar ’yanci. - Mulkin Yesu Kristi, Za ya dawwama. 
(Ka kuma duba Zab. 94:14; Mis. 3:5, 6; Ibran. 13:5.)