Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bh pp. 3-7
  • Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan?
  • Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ƙananan Jigo
  • GA ABIN DA ALLAH YA NUFA ZAI YI GA DUNIYA KAMAR YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA KOYAR.
  • KA AMFANA DAGA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA
Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
bh pp. 3-7

Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan?

KA KARANTA kowace jarida. Ka kalli telibijin ko kuma ka saurari rediyo. A cike suke da labarai na yin laifi, yaƙi, da ta’addanci. Ka yi tunanin naka matsalolin. Wataƙila ciwo ko kuma mutuwar wanda kake ƙauna yana tada maka hankali. Za ka ji kamar yadda mutumin arziki Ayuba ya ji, wanda ya ce “ina baƙin ciki ƙwarai.”—Ayuba 10:15.

Ka tambayi kanka:

  • Abin da Allah ya nufa mini da sauran ’yan Adam ke nan?

  • A ina zan sami taimako domin in jimre wa matsalolina?

  • Da begen za mu taɓa samun salama kuwa a duniya?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyi.

GA ABIN DA ALLAH YA NUFA ZAI YI GA DUNIYA KAMAR YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA KOYAR.

“Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna

“Gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa.”—Ishaya 35:5, 6.

“Za a buɗe idanun makafi.”—Ishaya 35:5.

“Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su . . .fito.”—Yohanna 5:28, 29.

“Ba wanda zai . . . ƙara yin kukan yana ciwo.”—Ishaya 33:24.

“Za a yi albarkar hatsi a ƙasa.”—Zabura 72:16.

Duniya ta canja kamar yadda Allah ya fada: Tsofaffi sun zama matasa, marasa lafiya makafi sun warke, an ta da matattu, akwai yalwar abinci

KA AMFANA DAGA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA

Kada ka yi tunanin abin da aka gabatar a shafuffuka na baya kamar kyakkyawan zato ne kawai. Allah ya yi alkawarin zai yi waɗannan abubuwa, kuma Littafi Mai Tsarki ya yi bayani game da yadda zai yi hakan.

Mutane biyu suna nazari da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki zai taimake mu a hanyoyi masu yawa. Mabuɗi ne na hanyar samun rayuwa mai gamsarwa da gaske har a yanzu. Ka ɗan yi tunani game da damuwanka da kuma matsalolinka. Wataƙila sun haɗa da matsalar kuɗi, matsala ta iyali, rashin lafiya, ko kuma rasuwar wanda kake ƙauna. Littafi Mai Tsarki zai iya taimakonka ka magance matsalolinka a yau, kuma zai iya kwantar maka da hankali ta wajen amsa tambayoyi irin su:

  • Me ya sa muke wahala?

  • Ta yaya za mu jimre wa damuwa na rayuwa?

  • Ta yaya za mu kyautata farin cikin iyalinmu?

  • Menene yake samun mu sa’ad da muka mutu?

  • Za mu sake ganin ’yan’uwanmu da suka rasu kuwa?

  • Ta yaya za mu tabbata cewa Allah zai cika waɗannan alkawuransa game da rayuwa ta nan gaba?

Ganin cewa kana karanta wannan littafin ya nuna cewa kana so ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Wannan littafin zai taimake ka. Ka kula cewa kowane sakin layi yana da nasa tambaya a ƙasan shafin. Miliyoyin mutane sun ji daɗin wannan salon nazari na tambayoyi da amsoshi wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Muna fatan kai ma za ka ji daɗinsa. Allah ya yi maka albarka sa’ad da kake fahimtar abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa!

KA SAN LITTAFINKA MAI TSARKI

LITTATTAFAI da wasiƙu 66 ne suke cikin Littafi Mai Tsarki. Waɗannan an rarraba su zuwa surori da ayoyi domin sauƙin karatu. Sa’ad da aka ja aya a wannan littafin, lamba ta farko bayan sunan yana nufin sura na littafi na Littafi Mai Tsarki ko kuma wasiƙa, bayan kuma yana nufin aya. Alal misali, “2 Timothawus 3:16” yana nufin wasiƙa ta biyu ga Timothawus, sura 3, aya 16.

Ba da daɗewa ba za ka saba da Littafi Mai Tsarki ta wajen bincika nassosi da aka ja a wannan littafin. Kuma me ya sa ba za ka kafa tsarin karatun Littafi Mai Tsarki kullum ba? Ta wajen karanta sura biyu ko uku kowace rana, za ka karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya a cikin shekara ɗaya.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba