-
Mecece Ranar Shari’a?Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
-
-
ne na Allah. Domin su rayu har abada waɗanda suka tsira daga Armageddon da waɗanda aka tashe su daga matattu dole ne su bi umurnin Allah, haɗe da dukan wani umurni da za a bayyana a cikin shekara dubun. Saboda haka, mutane za a yi musu hukunci ne bisa abin da suka yi cikin Ranar Shari’a.
Ranar Shari’a za ta ba miliyoyin mutane zarafinsu na farko su koyi game da nufin Allah kuma su bi shi. Wannan yana nufin cewa za a yi aikin koyarwa mai yawa. Hakika, ‘mazaunan duniya za su koyi adalci.’ (Ishaya 26:9) Amma, ba duka ba ne za su so su yi nufin Allah. Ishaya 26:10 ta ce: “Ko an nuna ma mugu alheri, ba za ya koyi adilci ba: a cikin ƙasa mai-gaskiya za ya aika mugunta, ba kuwa za shi ga ɗaukakar Ubangiji ba.” Za a halaka miyagu har abada a Ranar Shari’a.—Ishaya 65:20.
A ƙarshen Ranar Shari’a, mutane da suka tsira za su “rayu” su zama mutane kamilai. (Ru’ya ta Yohanna 20:5) Saboda haka, a Ranar Shari’a za a mai da mutane kamar yadda suke tun farko. (1 Korinthiyawa 15:24-28) Daga nan, sai gwaji na ƙarshe ya biyo baya. Za a saki Shaiɗan daga kurkuku kuma a ƙyale shi ya yi ruɗi na ƙarshe ga mutane. (Ru’ya ta Yohanna 20:3, 7-10) Waɗanda suka guje shi za su more cikar alkawarin Littafi Mai Tsarki: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Hakika, Ranar Shari’a za ta kasance albarka ga dukan ’yan adam masu aminci!
-
-
1914—Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai TsarkiMenene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
-
-
RATAYE
1914—Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai Tsarki
ƊALIBAN Littafi Mai Tsarki sun yi shelar cewa abubuwa masu muhimmanci za su faru a shekara ta 1914 na kusan shekara 40. Menene waɗannan abubuwa masu muhimmanci, kuma wane tabbaci ne ya nuna cewa shekara ta 1914 shekara ce mai muhimmanci?
Kamar yadda yake rubuce a Luka 21:24, Yesu ya ce: “Al’ummai za su tattake Urushalima kuma har zamanan Al’ummai sun cika.” Urushalima ita ce babbar birnin al’ummar Yahudawa—mazaunin gadon sarautar sarakuna daga zuriyar Dawuda. (Zabura 48:1, 2) Amma, waɗannan sarakuna sun bambanta da sarakunan wasu al’ummai. Suna zama ne bisa “kursiyin Ubangiji” suna wakiltan Allah kansa. (1 Labarbaru 29:23) Saboda haka Urushalima alama ce ta sarautar Jehobah.
Yaushe kuma ta yaya al’ummai suka fara “tattake” sarautar Allah? Wannan ya faru ne a shekara ta 607 K.Z., sa’ad da Babiloniyawa suka ci Urushalima a yaƙi. “Kursiyin Ubangiji” ya kasance babu kowa a kai, kuma aka taɓa zuriyar sarakuna da ta samo asali daga Dawuda. (2 Sarakuna 25:1-26) Wannan ‘tattakewa’ za ta ci gaba ne har abada? A’a, domin annabcin Ezekiel ya ce sarkin ƙarshe na Urushalima, Zedekiah: Ya “kawarda rawani, [kuma] tuɓe ƙambi: . . . har lokacin da wannan ya zo wanda wajibinsa ne, ni ma im ba shi.” (Ezekiel 21:26, 27) Wanda “wajibinsa” ne ƙambin zuriyar Dawuda Yesu Kristi ne. (Luka 1:32, 33) Saboda haka ‘tattakewa’ za ta ƙare sa’ad da Yesu ya zama Sarki.
Yaushe ne wannan babban abu zai faru? Yesu ya nuna cewa ’yan al’ummai za su yi sarauta na wani tabbataccen lokaci. Batun da ke cikin sura 4 na Daniel ya ƙunshi mabuɗin sanin tsawon wannan lokaci. Ya ba da labarin mafarki da Sarki Nebuchadnezzar na Babila ya yi. Ya ga wani babban itace da aka sare. Gindin sawayensa ba zai iya girma ba domin an ɗaure shi da ƙarfe da jangaci. Mala’ika ya sanar: ‘A bar wokatai guda bakwai kuma su bi ta bisa kansa.’—Daniel 4:10-16.
A Littafi Mai Tsarki, a wani lokaci ana amfani da itace wajen wakiltan sarauta. (Ezekiel 17:22-24; 31:2-5) Saboda haka sare wannan itace na alama yana nuna yadda za a taɓa sarakuna a Urushalima waɗanda suke wakiltan sarautar Allah. Wahayin kuma ya ba da gargaɗi za a “tattake Urushalima” na ɗan lokaci—“wokatai bakwai.” Yaya tsawon wannan lokaci yake?
Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14 ta nuna cewa lokatai uku da raɓi sun yi daidai da “kwana dubu da metin da sattin.” Saboda haka, “wokatai bakwai” zai ninka tsawon wannan, ko kuma kwanaki 2,520. Amma Al’ummai ba su daina tattake sarautar Allah ba bayan kwanaki 2,520 bayan faɗuwar Urushalima. A bayyane yake cewa lokaci na wannan annabci ya fi haka tsawo. Bisa ga abin da ke Littafin Lissafi 14:34 da kuma Ezekiel 4:6, waɗanda suka yi maganar “rana guda domin shekara guda,” “wokatai bakwai” zai kasance shekara 2,520.
Shekara 2,520 ya fara a watan Oktoba shekara ta 607 K.Z., sa’ad da Babiloniyawa suka ci Urushalima aka tunɓuke sarautar zuriyar Dauda daga kursiyinsa. Wannan lokaci ya ƙare a shekara ta 1914. A wannan lokaci, “zamanan al’ummai” ya ƙare, kuma aka naɗa Yesu Kristi ya zama Sarkin Mulkin Allah na samaniya.a—Zabura 2:1-6; Daniel 7:13, 14.
Kamar yadda Yesu ya annabta, ‘bayyanuwarsa’ Sarki a samaniya ya zo da aukuwa masu ban mamaki—yaƙi, yunwa, girgizar ƙasa, annoba. (Matta 24:3-8; Luka 21:11) Waɗannan aukuwa sun ba da tabbaci cewa shekara ta 1914 mafari ce ta Mulkin Allah kuma mafari ce ta “kwanaki na ƙarshe” na wannan mugun zamani.—2 Timothawus 3:1-5
a Daga Oktoba na shekara ta 607 K.Z., zuwa 1 ga Oktoba K.Z., shekaru 606 ne. Tun da babu shekara ta sifiri, daga 1 ga Oktoba shekara ta 1 K.Z., zuwa Oktoba shekara ta 1914 shekaru 1,914 ne. Idan aka haɗa shekara 606 da shekara 1,914, sai mu sami shekaru 2,520. Domin bayani game da faɗuwar Urushalima a shekara ta 607 K.Z., ka dubi talifin nan “Chronology” (Tsarin Shekaru) a Littafin nan Insight on the Scriptures, da Shaidun Jehobah suka wallafa.
-
-
Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
-
-
RATAYE
Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?
HALITTAR ruhu da ake kira Mika’ilu ba a ambace shi sau da yawa ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, dukan lokacin da aka yi maganarsa yana yin wani abu. A cikin Littafin Daniel, Mika’ilu yana yaƙan miyagun ruhohi; a cikin wasiƙar Yahuda, yana jayayya da Shaiɗan; a Ru’ya ta Yohanna kuma, yana yaƙi da Iblis da kuma aljanunsa. Ta wajen kāre sarautar Jehobah da kuma yaƙan abokan gaban Allah, Mika’ilu ya ci sunansa wanda yake nufin—“Waye kamar Allah?” Amma wanene Mika’ilu?
Wasu mutane suna da suna fiye da ɗaya. Alal misali, an san Yaƙub da Isra’ila, manzo Bitrus kuma, Siman. (Farawa 49:1, 2; Matta 10:2) Haka nan kuma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mika’ilu wani suna ne na Yesu Kristi, kafin ya rayu a duniya da kuma bayan ya rayu a duniya. Bari mu bincika wasu dalilai na Nassi da ya sa muka ce haka.
Babban Mala’ika. Kalmar Allah ta kira Mika’ilu “shugaban Mala’ika.” (Yahuda 9) Ka lura cewa an kira Mika’ilu shugaban mala’iku. Wannan ya nuna cewa mala’ikan guda ɗaya ne. Hakika, furcin nan “shugaban mala’ika” ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki a kaɗaici ne ba a jam’i ba. Bugu da ƙari, Yesu yana da alaƙa da ofishin shugaban mala’iku. Game da Ubangiji Yesu Kristi da aka ta da daga matattu, 1 Tassalunikawa 4:16 ta ce: “Ubangiji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai-ƙarfi, da muryar sarkin mala’iku.” Saboda haka an kwatanta muryar
-