Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Littafi Mai Tsarki Bai Rube Ba
    Hasumiyar Tsaro (Na Wa’azi)—2016 | Na 4
    • ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

      Littafi Mai Tsarki Bai Ruɓe Ba

      ƘALUBALE: Fata da takardar ganye ne asalin abubuwan da marubuta da kuma mutanen da suka kofe Littafi Mai Tsarki suka yi amfani da su. (2 Timotawus 4:13) Ta yaya fata da kuma takardar ganye suka sa adana rubutun Littafi Mai Tsarki ya zama da wuya?

      Takardar ganye tana saurin yagewa ko kuma koɗewa. Wasu ’yan bincike a ƙasar Masar, Richard Parkinson da Stephen Quirke sun ce: “Takardar da aka yi da ganye za ta iya ruɓewa kuma ta zama zare-zare ko kuma gari-gari. Idan aka adana ta, za ta iya kumbura ko ta jiƙe ko kuma ƙwari da ɓeraye su cinye ta. Idan aka binne takardar kuma, gara suna iya yin kaca-kaca da ita.” Wasu littattafan da aka samo sun lalace ba tare da ɓata lokaci ba domin rana ko danshi sun yi musu yawa.

      Fata kuma ta fi takarda da aka yi da ganye jurewa, amma shi ma yana iya lalacewa idan aka bar shi a rana ko a wurare masu danshi ko kuma wuri mai zafi sosai.a Ƙwari suna son cin fata. Shi ya sa aka kasa adana littattafai da dama na dā. Da a ce Littafi Mai Tsarki ya ruɓe kamar sauran littattafai, da ba mu san saƙon da ke cikinsa ba.

      YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA TSIRA: Dokar da aka ba Yahudawa ta ce kowane sarki ya “sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki,” wato littattafai biyar da Musa ya rubuta. (Kubawar Shari’a 17:18, Littafi Mai Tsarki) Amma ƙwararrun marubuta da yawa sun kofe Littafi Mai Tsarki sau da yawa har ya zama cewa a ƙarni na farko, akwai nassosi a dukan majami’u a Isra’ila da Makidoniya. (Luka 4:16, 17; Ayyukan Manzanni 17:11) Yaya aka yi waɗannan tsofaffin littattafan suka tsira har wa yau?

      1. Wani tulu; 2. Wani sashen littafi da aka samo a Tekun Gishiri

      An adana Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri ƙarnuka da dama a cikin tuluna a kogon dutse marar danshi

      Wani kogo da aka samo wasu littattafan Littafi Mai Tsarki

      Wani masanin Littattafan Sabon Alkawari mai suna Philip W. Comfort ya ce: “Yahudawa suna yawan saka irin waɗannan littattafan ne a cikin tuluna don kada su lalace.” Hakan ma Kiristoci suka ci gaba da adana su. An samo wasu littattafai na Littafi Mai Tsarki na dā a cikin tuluna da ƙananan ɗakuna da kogon dutse da kuma wuraren da babu danshi.

      SAKAMAKO: Hakan ya sa dubban littattafai na Littafi Mai Tsarki na dā sun tsira har wa yau, wato kusan shekara 2,000 ke nan. Babu wani littafi da ya jure kamar Littafi Mai Tsarki.

      a Alal misali, an rubuta littafin nan U.S. Declaration of Independence (Wa’adin Samun ’Yanci na Ƙasar Amurka) a fata shekaru 250 da suka shige. Amma yanzu, littafin ya koɗe sosai har ma da ƙyar ake iya gane abin da aka rubuta a ciki.

  • ’Yan Hamayya Sun Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro (Na Wa’azi)—2016 | Na 4
    • ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

      ’Yan Hamayya Sun Kasa Halaka Littafi Mai Tsarki

      ƘALUBALE: ’Yan siyasa da kuma malaman addinai da yawa sun yi abubuwan da suka saɓa wa saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Sau da yawa, sun yi amfani da ikonsu wajen neman su hana mutane kasancewa da Littafi Mai Tsarki da buga shi ko kuma fassara shi. Ka yi la’akari da misalai biyu:

      • A Wajen Shekara ta 167 Kafin Haihuwar Yesu: Sarki Antiochus Epiphanes, wanda ya nemi ya sa Yahudawa su bi addinin Helenawa ƙarfi da yaji ya sa a halaka dukan kofofin Nassosin Ibrananci. Wani ɗan tarihi mai suna Heinrich Graetz ya ce: “Bayin Sarki Epiphanes sun ƙona dukan nassosin da suka gani kuma sun kashe duk wani mutumin da bai ba su haɗin kai ba ko kuma ya kai ƙara.”

      • Bayan Zamanin Manzanni: Wasu limaman Katolika sun yi fushi cewa mutanen da ba limamai ba suna koyar da Littafi Mai Tsarki maimakon koyarwar cocin Katolika. Don haka, suka hana su kasancewa da Littafi Mai Tsarki, sai dai littafin Zabura kawai na yaren Latin. A wani babban taro da limaman coci suka yi, sun ba da umurni cewa a riƙa bi gida-gida da sako-sako don a tabbatar da cewa ana bin wannan dokar kuma a ƙona duk wani gidan da aka ga waɗannan littattafan a ciki.

      Da a ce maƙiyan Littafi Mai Tsarki sun yi nasara wajen halaka shi, da a yau ba mu san saƙon da ke cikinsa ba.

      Wani shafi daga Littafi Mai Tsarki da William Tyndale ya fassara zuwa Turanci

      Littafi Mai Tsarki da William Tyndale ya juya zuwa Turanci ya tsira duk da cewa an sa masa takunkumi, an ƙona wasu, kuma an kashe Tyndale a shekara ta 1536

      YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA TSIRA: Sarki Antiochus ya fi tsananta harinsa a ƙasar Isra’ila, amma Yahudawa da yawa sun riga sun ƙaura zuwa wasu ƙasashe. Masana sun ce sama da kashi sittin na Yahudawa suna zama a wasu ƙasashe a ƙarni na farko bayan haihuwar Yesu. Yahudawa sun ajiye Nassosi a majami’u kuma waɗannan Nassosin ne Kiristoci da kuma mutanen da suka rayu bayan wannan zamanin suka yi amfani da su.—Ayyukan Manzanni 15:21.

      Bayan zamanin manzannin Yesu, mutanen da suke son Littafi Mai Tsarki sun ci gaba da fassara da kuma kofe Nassosi duk da hamayya. An riga an fassara littattafai dabam-dabam na Littafi Mai Tsarki zuwa harsuna talatin da uku kafin tsakiyar ƙarni na 15 da aka soma ƙera na’urorin buga littattafai. Bayan haka, an fassara da kuma buga Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba a taɓa yi ba.

      SAKAMAKO: Duk da hamayya daga sarakuna da kuma wasu limamai, Littafi Mai Tsarki ne littafin da aka fi karantawa da kuma fassarawa a duniya. Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya inganta dokoki da kuma yaren wasu ƙasashe kuma yana gyara rayuwar miliyoyin mutane.

  • An Kasa Canja Sakon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro (Na Wa’azi)—2016 | Na 4
    • Wani mutum yana kofe Littafi Mai Tsarki

      ʼYan Masoretes sun mai da hankali sosai wajen kofe Nassosi

      ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA AKA KĀRE LITTAFI MAI TSARKI

      An Kasa Canja Saƙon da Ke Cikin Littafi Mai Tsarki

      ƘALUBALE: Littafi Mai Tsarki bai ruɓe ba kuma ’yan hamayya sun kasa halaka shi. Duk da haka, wasu mafassara da masu kofe Littafi Mai Tsarki sun nemi su canja saƙon da ke cikinsa. A wasu lokuta, sun yi ƙoƙarin yin hakan don ya jitu da koyarwarsu. Ka yi la’akari da wasu misalai:

      • Wuraren ibada: A tsakanin ƙarni na huɗu zuwa ƙarni na biyu kafin zamanin Yesu, mafassaran juyin Samaritan Pentateuch sun saka furucin nan “a Tudun Gerizim ne za ka gina bagadi,” a ƙarshen Fitowa 20:17. Samariyawa sun yi wannan ƙarin gishirin ne don ya goyi bayan haikalin da suke so su gina a Tudun Gerizim.

      • Koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya: Ƙasa da shekara 300 bayan da aka kammala rubutun Littafi Mai Tsarki, wani marubuci da ya amince da koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya ya ƙara gishiri a littafin 1 Yohanna 5:7. Ya ce: “A cikin sama, akwai Uba da Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki: kuma su ukun ɗaya ne.” Amma babu wannan furucin a cikin rubutun Littafi Mai Tsarki na farko. Wani marubuci mai suna Bruce Metzger ya ce: “An fara samun waɗannan furucin a kofofin Littafi Mai Tsarki na Old Latin da [Latin] Vulgate daga ƙarni na shida.”

      • Sunan Allah: Mafassara da yawa sun cire sunan Allah daga Littafi Mai Tsarki cikin jituwa da dokar da Yahudawa suka kafa. Sun sauya sunan da laƙabi kamar su “Allah” da “Ubangiji.” Hakan bai dace ba domin ba Mahaliccinmu kaɗai ake kira da waɗannan laƙabin ba, amma ana kiran wasu mutane da allolin ƙarya, har ma da Shaiɗan da waɗannan laƙabin.—Yohanna 10:34, 35; 1 Korintiyawa 8:5, 6; 2 Korintiyawa 4:4.a

      YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA TSIRA: Da farko, ko da yake wasu mutanen da suka kofe Littafi Mai Tsarki ba su mai da hankali sosai ba ko kuma sun ɗan ƙara gishiri, amma da yawa daga cikinsu sun mai da hankali sosai. Wasu marubuta a tsakanin ƙarni na shida da goma bayan haihuwar Yesu sun kofe Nassosin Ibrananci, kuma aikin da suka yi ne ake kira juyin Masoretic a yau. Tarihi ya nuna cewa waɗannan mutanen sun ƙirga kalmomi da kuma harufan da ke cikin Littafi Mai Tsarki don su tabbatar da cewa ba su yi wani kuskure ba. A duk inda suka ga cewa akwai kuskure a ainihin littafin da suke kofewa, suna ambata hakan a gefen littafin. Waɗannan mutanen sun ƙi su ƙara gishiri a cikin Littafi Mai Tsarki. Wani Farfesa mai suna Moshe Goshen-Gottstein ya ce: “Waɗannan mutanen sun gaskata cewa canja wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki da gangan, laifi ne mafi girma.”

      Na biyu, kofofin Littafi Mai Tsarki da yawa da muke da su a yau suna taimaka wa masana su gano kura-kuran da aka yi. Alal misali, limamai sun daɗe suna koyar da cewa juyin Littafi Mai Tsarki na yaren Latin ne na ƙwarai. Saboda haka, sai suka saka kalmomin nan da ba daidai ba da ke 1 Yohanna 5:7 da muka ambata ɗazun. Wannan ƙarin gishirin ya ma bayyana a juyin King James Version na Turanci. Amma mene ne aka lura sa’ad da aka gano wasu littattafai na Littafi Mai Tsarki? Bruce Metzger ya ce: “Kalmomin [da ke 1 Yohanna 5:7] sun bayyana a na Latin kawai, ba su bayyana a juyin (Syriac da Coptic da Armenian da Ethiopic da Arabic da kuma Slavonic) ba.” A sakamakon haka, juyin King James Version da aka buga kwana-kwanan nan ba ya ɗauke da waɗannan kalmomin.

      Chester Beatty shafi na 46, wani littafin ganye daga kusan shekara 200 B.H.Y.

      Chester Beatty shafi na 46, Littafi Mai Tsarki da aka rubuta a takardar ganye a wajen shekara ta 200 B.H.Y.

      Shin littattafai na dā na Littafi Mai Tsarki sun ba da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba? Saʼad da aka gano Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri a shekara ta 1947, masana sun sami zarafin gwada juyin Masoretic na Ibrananci da kuma wasu tsofaffin littattafai da aka kofa fiye da shekara dubu kafin lokacin. Wani cikin mutanen da suka yi bincike a kan Naɗaɗɗun Littattafai na Tekun Gishiri ya ce littafi guda “ya ba da tabbaci cewa Yahudawan da suka yi sama da shekara dubu ɗaya suna kofe Littafi Mai Tsarki, sun yi aiki mai kyau sosai kuma ba su ƙara gishiri ba.”

      Laburaren nan Chester Beatty da ke birnin Dublin, a ƙasar Ireland yana ɗauke da littattafan ganye na kusan dukan littattafan Nassosin Helenanci, har da waɗanda aka rubuta a ƙarni na biyu bayan haihuwar Yesu, wato wajen shekara 100 bayan da aka kammala rubutun Littafi Mai Tsarki. Wani ƙamus mai suna The Anchor Bible Dictionary ya ce: ‘Ko da yake littattafan suna ɗauke da wasu sababbin bayanai game da Littafi Mai Tsarki, amma sun sa mun kasance da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba.ʼ

      “Littafi Mai Tsarki ne kaɗai littafi na zamanin dā da za mu iya furtawa da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba”

      SAKAMAKO: Kofofi da yawa na Littafi Mai Tsarki da kuma yadda suka daɗe sun inganta saƙon da ke cikinsa maimakon su ɓata shi. Wani mai suna Sir Frederic Kenyon ya ce game da Nassosin Helenanci: “A cikin dukan littattafan da aka taɓa wallafawa, Littafi Mai Tsarki ne littafin da ya fi kasancewa da bayanan da suka nuna cewa saƙon da ke cikinsa gaskiya ne, kuma babu mutumin da zai iya cewa an canja saƙon da ke cikinsa.” William Henry Green kuma ya ce game da Nassosin Ibrananci: “Littafi Mai Tsarki ne kaɗai littafi na zamanin dā da za mu iya furtawa da tabbaci cewa ba a canja saƙon da ke cikinsa ba.”

      a Don ƙarin bayani ka duba sashe na 1 da 2 na ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah. Za ka iya samunsa a www.pr418.com/ha.

Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba