WAƘA TA 88
Ka Koya Mini Hanyoyinka
Hoto
	(Zabura 25:4)
- 1. Mun zo gare ka, Ya Jehobah Allah, - Domin kai ne ka gayyato mu. - Maganarka tana sa mu ga hanya, - Tana sa mu san dokokinka. - (AMSHI) - Ka koya min domin in fahimta, - Ka sa na riƙa bin umurninka. - Ka taimaka min in yi nagarta, - Kuma in so dokokinka sosai. 
- 2. Hikimar Jehobah babu iyaka, - Hukuncinka babu kuskure. - Duk dokokinka na taimaka mana, - Kalmarka tana ƙarfafa mu. - (AMSHI) - Ka koya min domin in fahimta, - Ka sa na riƙa bin umurninka. - Ka taimaka min in yi nagarta, - Kuma in so dokokinka sosai. 
(Ka kuma duba Fit. 33:13; Zab. 1:2; 119:27, 35, 73, 105.)