WAƘA TA 129
Za Mu Riƙa Jimrewa
Hoto
	- 1. Me zai taimaka - Mu jimre da matsaloli? - Yesu ya jimre, - Ya kafa mana misali. - Jehobah, Allah ne - Ya taimaka masa. - (AMSHI) - Sai mu riƙa jimrewa, - Mu riƙe aminci. - Jehobah na ƙaunar mu, - Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe. 
- 2. Duniyar Shaiɗan - Tana baƙanta zucinmu, - Amma nan gaba - Za mu ji daɗin aljanna. - Zama a cikinta - Ne muke ɗokin yi. - (AMSHI) - Sai mu riƙa jimrewa, - Mu riƙe aminci. - Jehobah na ƙaunar mu, - Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe. 
- 3. Shakka ko tsoro - Ba zai sa mu bar Allah ba. - Za mu ci gaba - Har sai ranar Allah ta zo. - Mu riƙa jimrewa - Domin ƙarshe ya zo. - (AMSHI) - Sai mu riƙa jimrewa, - Mu riƙe aminci. - Jehobah na ƙaunar mu, - Za mu riƙa jimrewa har ƙarshe. 
(Ka kuma duba A. M. 20:19, 20; Yaƙ. 1:12; 1 Bit. 4:12-14.)