Me Ya Sa Za Mu Bincika Littafi Mai Tsarki?
Ka san Littafi Mai Tsarki kuwa? A tarihi, babu littafin da aka raba a dukan duniya kamar Littafi Mai Tsarki. Mutane daga dukan al’adu sun gane cewa saƙonsa yana ƙarfafawa kuma yana ba da bege, shawararsa tana da amfani a rayuwa ta yau da kullum. Duk da haka, yawancin mutane a yau ba su san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. Ko kana son addini ko a’a, wataƙila kana son ka san abin da ke cikinsa. An tsara wannan mujallar ce don ka san ainihin abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
KAFIN ka soma karanta Littafi Mai Tsarki, zai dace ka san wasu abubuwa game da yadda aka tsara wannan mujallar. Littafi Mai Tsarki da mutane suke kira Nassosi Masu Tsarki, yana ɗauke da littattafai ko sashe 66, ya soma da Farawa ya kuma kammala da Ru’ya ta Yohanna, ko Wahayi.
Wanene mawallafin Littafi Mai Tsarki? Wannan tambaya ce mai ban mamaki. Gaskiyar ita ce, maza arba’in ne suka rubuta Nassosi a cikin shekaru 1,600. Abin sha’awa shi ne, waɗannan maza ba su yi da’awar cewa su ne mawallafan Littafi Mai Tsarki ba. Ɗaya daga cikin marubutan ya rubuta cewa: “Kowane nassi hurarre daga wurin Allah” ne. (2 Timotawus 3:16) Wani kuma cikin marubutan ya ce: “Ruhun Ubangiji ya yi zance da ni, Maganatasa kuma tana bisa harshena.” (2 Sama’ila 23:2) Marubutan sun faɗi cewa Jehobah Allah, Sarki Mafi Girma a sararin samaniya, shi ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki. Marubutan sun bayyana cewa, Allah yana son mutane su kusace shi.
Akwai wani abu mai muhimmanci da ake bukata don a fahimci Littafi Mai Tsarki. Nassosi suna da jigo guda: kunita ikon Allah na yin sarauta bisa ’yan adam ta hanyar Mulkinsa ta samaniya. A shafuffukan da ke gaba, za ka ga yadda wannan jigon yake a kowane sashe daga Farawa zuwa Ru’ya ta Yohanna.
Da waɗannan batutuwan a zuciyarka, yanzu ka duba saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki, littafin da aka fi sani a duniya.
a Akwai hanyoyi dabam-dabam na rubuta kwanan wata. A wannan mujallar, A.Z. tana nufin “A Zamaninmu” kuma K.Z. tana nufin “Kafin Zamaninmu.” Za ka ga kwatancin hakan a shekarun da aka rubuta a ƙarƙashin shafuffukan.