Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 16 pp. 158-167
  • “Ka Yi Adalci” Wajen Tafiya da Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Yi Adalci” Wajen Tafiya da Allah
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bin ‘Hakikanin Adalci’
  • Bisharar da Kuma Shari’ar Allah
  • Yadda Muke Bi da Wasu
  • Dattawa Suna Hidima “da Gaskiya”
  • “Dukan Hanyoyinsa Gaskiya Ne”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Yesu “Ya Kafa Yin Gaskiya a Duniya”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Yadda Ake Nuna Kauna da Adalci a Cikin Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • ‘Jehobah Za Ya Rama Masu’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 16 pp. 158-167
Dattawa biyu sun ziyarci wata ’yar’uwa da yaranta biyu a gidansu. Sun saurareta sosai yayin da take magana.

BABI NA 16

“Ka Yi Adalci” Wajen Tafiya da Allah

1-3. (a) Me ya sa muka ci albarkacin Jehobah? (b) Mene ne Macecinmu mai ƙauna yake bukata a gare mu?

KA YI tunanin ka kamu a cikin jirgin ruwa da yake nutsewa. Sa’ad da kake jin babu taimako, sai ga maceci ya zo ya cece ka. Za ka yi murna kuwa idan macecinka ya cire ka daga haɗarin, ya ce: “Yanzu ka tsira”! Ba za ka yi wa wannan mutumin godiya ba? Hakika, domin albarkacinsa ka samu rai.

2 A wani hali, wannan ya kwatanta abin da Jehobah ya yi mana. Hakika, mun ci albarkacinsa. Tun da ya yi mana tanadin fansa, ya sa cetonmu ya yiwu daga hannun zunubi da mutuwa. Muna jin mun tsira, domin mun sani cewa idan muka nuna bangaskiya ga wannan hadaya mai tamani, an gafarta mana zunubinmu, kuma rayuwarmu ta har abada ba ta cikin haɗari. (1 Yohanna 1:7; 4:9) Kamar yadda muka gani a Babi na 14, fansa nuna ƙauna ce da shari’a mafi girma na Jehobah. Yaya ya kamata mu amsa?

3 Ya dace mu yi la’akari da abin da Macecinmu mai ƙauna yake bukata a gare mu. Jehobah ya ce ta bakin annabi Mika: “Ya faɗa maka abin da yake nema daga gare ka. Abin da yake nema shi ne ka yi adalci, ka ƙaunaci yin jin ƙai, ka yi tafiyarka da Allahnka cikin sauƙin kai.” (Mika 6:8) Ka lura cewa ɗaya cikin abubuwan da Jehobah yake bukata a gare mu shi ne mu yi “aikin gaskiya.” Ta yaya za mu yi haka?

Bin ‘Hakikanin Adalci’

4. Ta yaya muka sani cewa Jehobah yana son mu yi rayuwa cikin jituwa da mizanansa na adalci?

4 Jehobah ya bukace mu mu bi mizanansa na nagarta da mugunta. Tun da mizanansa nagargaru ne kuma masu adalci, muna bin shari’a da adalci sa’ad da muka bi su. “Ku koyi yin abin da yake daidai. Sai ku aikata gaskiya,” in ji Ishaya 1:17. Kalmar Allah ta yi mana gargaɗi mu “nemi adalci.” (Zafaniya 2:3) Kuma ta aririce mu mu “ɗauki sabon halin nan da Allah ya halitta bisa ga kamannin kansa. Halin nan kuwa, ya bayyana cikin adalci.” (Afisawa 4:24) Hakikanin adalci—hakikanin shari’a—suna guje wa nuna ƙarfi, rashin tsabta, da kuma rashin ɗabi’a, domin waɗannan suna saɓa wa abin da yake mai tsarki.—Zabura 11:5; Afisawa 5:3-5.

5, 6. (a) Me ya sa ba nauyaya ba ce a gare mu mu yi ayyuka da suka jitu da mizanan Jehobah? (b) Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa biɗan adalci abu ne mai ci gaba?

5 Nauyaya ce a gare mu mu bi mizanan adalci na Jehobah? A’a. Zuciya da ta motsa wurin Jehobah ba ta fushi da bukatunsa. Domin muna ƙaunar Allahnmu da kuma yadda yake, muna so mu rayu a hanyar da za ta faranta masa rai. (1 Yohanna 5:3) Ka tuna cewa Jehobah “yana ƙaunar ayyukan adalci.” (Zabura 11:7) Idan da gaske za mu yi koyi da shari’ar Allah, ko kuma adalci, to dole ne mu ƙaunaci abin da Jehobah yake ƙauna kuma mu guji abin da yake ƙyama.—Zabura 97:10.

6 Yana da wuya ga mutane ajizai su biɗi adalci. Dole ne mu tuɓe tsohon halinmu da ayyukansa na zunubi mu yafa sabo. Littafi Mai Tsarki ya ce ta wajen cikakken ilimi “ake sabonta” sabon halin. (Kolosiyawa 3:9, 10) Kalmomin nan “ake sabonta” suna nuna cewa yafa sabon halin abu ne da ke ci gaba, abu ne da ke bukatar ƙoƙari sosai. Ko yaya muke ƙoƙarin mu yi abin da yake daidai, akwai lokatai da ajizancinmu yake sa mu yi kuskure a magana ko kuma a ayyuka.—Romawa 7:14-20; Yakub 3:2.

7. Ta yaya ya kamata mu ɗauki tangarɗa a ƙoƙarinmu na biɗan adalci?

7 Ta yaya za mu ɗauki tangarɗa a ƙoƙarinmu na biɗan adalci? Hakika, ba za mu so mu rage tsananin zunubi ba. A haka kuma, kada mu kasala, mu ji cewa kurakuranmu sun sa ba mu dace da bauta wa Jehobah ba. Allahnmu mai alheri ya yi tanadin tagomashinsa ga waɗanda suka tuba da gaske. Ka tuna da kalmomi masu tabbatarwa na manzo Yohanna: “Waɗannan abu ni ke rubuta muku domin kada ku yi zunubi.” Sai kuma ya daɗa wannan zancen gaskiya: “Amma in har wani ya yi zunubi, [domin ajizanci da aka gada], to, muna da mai tsaya mana a gaban Uba, wato Yesu Almasihu.” (1 Yohanna 2:1) Hakika, Jehobah ya yi tanadin hadayar fansa ta Yesu saboda mu bauta masa yadda zai karɓa duk da ajizancinmu. Wannan bai motsa mu mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu faranta wa Jehobah rai ba?

Bisharar da Kuma Shari’ar Allah

8, 9. Ta yaya shelar bishara ta nuna shari’ar Jehobah?

8 Za mu iya yin shari’a—hakika, za mu iya yin koyi da shari’ar Allah—ta wajen saka hannu sosai a wa’azin bisharar Mulkin Allah ga wasu. Wace nasaba take tsakanin shari’ar Jehobah da kuma bisharar?

9 Jehobah ba zai kawo ƙarshen wannan zamanin ba ba tare da ya sa an yi gargaɗi ba da farko. A annabcinsa game da abin da zai faru a zamanin ƙarshe, Yesu ya ce: “Amma kafin ƙarshe ya zo, dole ne a yi wa dukan al’ummai shelar labarin nan mai daɗi.” (Markus 13:10; Matiyu 24:3) Amfani da kalmar nan “kafin” yana nufi cewa wasu abubuwa za su biyo bayan wa’azi ga dukan duniya. Waɗannan abubuwa sun haɗa da ƙunci mai tsanani, wanda zai nufa halaka ga miyagu kuma ya bayar da hanya ga sabuwar duniya ta adalci. (Matiyu 24:14, 21, 22) Hakika, babu wanda zai tuhumi Jehobah da yin rashin adalci ga miyagu. Ta wajen gargaɗi da aka yi, ya bayar da isashen zarafi ga waɗannan su yi canji kuma saboda haka su tsira daga halaka.—Yona 3:1-10.

10, 11. Ta yaya saka hannunmu cikin wa’azin bishara ke nuna shari’a ta Allah?

10 Ta yaya wa’azin bishara ya nuna shari’a ta Allah? Da farko, daidai ne mu yi abin da yake nagari da za mu iya mu taimaki wasu su samu ceto. Ka sake yin la’akari da misalin an cece ka daga jirgin ruwa da yake nutsewa. Bayan ka tsira kana cikin kwalekwale, hakika za ka so ka taimaki wasu da har ila suke cikin ruwan. Hakazalika, muna da hakki ga waɗanda har yanzu suna ƙoƙari a cikin “ruwa” na wannan muguwar duniya. Hakika, da yawa suna ƙin saƙonmu. Amma muddin Jehobah ya ci gaba da haƙuri, muna da hakkin mu ba su zarafi su “tuba” domin su shigo hanyar ceto.—2 Bitrus 3:9.

11 Ta wajen yin wa’azi ga dukan waɗanda muka sadu da su, muna nuna shari’a a wata muhimmiyar hanya: Muna nuna rashin son zuciya. Ka tuna cewa “Allah ba ya nuna bambanci, amma yana karɓar duk mai tsoronsa da kuma mai aikata adalci a kowace al’umma.” (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Idan za mu yi biyayya da Shari’arsa, to, dole ne kada mu hukunta mutane. Maimakon haka, ya kamata mu yi musu bisharar ko yaya launin fatarsu, matsayinsu, ko kuma arzikinsu. Ta haka muna bai wa dukan waɗanda za su saurara zarafin su ji kuma su yi na’am da bisharar.—Romawa 10:11-13.

Yadda Muke Bi da Wasu

12, 13. (a) Me ya sa ba za mu yi hanzarin hukunta wasu ba? (b) Mene ne ma’anar gargaɗin Yesu cewa “kada ku yanke wa kowa hukunci” da kuma “kada ku shari’anta kowa”? (Duba hasiya.)

12 Za mu kuma nuna shari’a ta wajen bi da wasu kamar yadda Jehobah yake bi da mu. Ba shi da wuya mu hukunta wasu, muna kushe musu muna tuhumar halayensu. Amma wanene a tsakaninmu zai so Jehobah ya bincika dalilin abin da ya sa yake abu, ko kuma bincika kurakuransa babu jinƙai? Ba haka Jehobah yake bi da mu ba. Mai Zabura ya lura cewa: “Ya Ubangiji, idan kana lissafa laifofi, wa zai tsaya?” (Zabura 130:3) Ba ma godiya ne cewa Allahnmu mai adalci mai jinƙai ba ya mai da hankali ga kurakuranmu? (Zabura 103:8-10) To, yaya ya kamata mu bi da wasu?

13 Idan mun fahimci jinƙai na shari’ar Allah, ba za mu yi hanzarin hukunta wasu ba a al’amuran da ba su shafe mu ba ko kuma waɗanda ba su da muhimmanci sosai. A Huɗubarsa Bisa Dutse, Yesu ya yi gargaɗi: “Kada ku yanke wa kowa hukunci, domin kada a yanke muku.” (Matiyu 7:1) In ji labarin Luka, Yesu ya daɗa cewa: “Kada ku shari’anta kowa, ku kuma ba za a yi muku ba.”a (Luka 6:37) Yesu ya nuna yana sane da cewa mutane ajizai suna da halin hukuntawa. Kowanne cikin masu sauraronsa waɗanda suke da halin hukunta wasu da tsanani ya kamata su daina haka.

Wata ’yar’uwa tana yi ma wani tsoho marar lafiya wa’azi da kuma wata budurwa.

Muna nuna shari’a ta Allah sa’ad da muke gaya wa wasu bishara ba tare da son zuciya ba

14. Domin waɗanne dalilai dole mu daina “shari’anta” wasu?

14 Me ya sa za ‘mu daina shari’anta’ wasu? Domin abu ɗaya shi ne, ikonmu yana da iyaka. Almajiri Yakub ya tunasar da mu: “Allah ne kaɗai mai ba da Koyarwa, shi ne kuma mai yin shari’a.” Saboda haka, Yakub ya yi tambayar kai tsaye: “Wane ne kai da har ka isa ka ɗora wa ɗan’uwanka laifi?” (Yakub 4:12; Romawa 14:1-4) Bugu da ƙari, ajizancinmu ba wuya zai sa hukuncinmu ya kasance da kuskure. Halaye da yawa da kuma dalilan da suka sa muka yi haka—haɗe da son zuciya, fahariya, kishi, da kuma adalcin-ƙa—za su iya ɓata yadda muke ɗaukan ’yan’uwanmu mutane. Muna da ƙarin iyaka, kuma yin bimbini bisa waɗannan ya kamata ya hana mu hanzarin kushe wa wasu. Ba ma iya ganin zuciya ba; ba ma kuma iya sanin dukan yanayin wasu ba. To, wanene mu da za mu ɗora wa ’yan’uwanmu masu bi laifi ko kuma mu kushe ƙoƙarinsu a bautar Allah? Ya fi kyau mu yi koyi da Jehobah ta wajen ganin abin da ke nagari cikin ’yan’uwanmu maza da mata maimakon mai da hankali ga kurakuransu!

15. Waɗanne kalmomi ne da kuma bi da mutane ba su da wuri tsakanin masu bauta wa Allah, me ya sa?

15 To, yaya batun hukunta waɗanda suke cikin iyalinmu? Abin baƙin ciki, a duniya ta yau wasu cikin hukunci mafiya tsanani an yi su ne a inda ya kamata ya zama mazaunin salama—gida. Ba abu ba ne mai wuya ka ji game da magidanta azzalumai, mata, da kuma iyaye waɗanda suke yi wa iyalansu “hukuncin” zagi da dūka kullayaumin. Amma, batsa, zagi, da kuma zalunci ba su da waje tsakanin masu bauta wa Allah. (Afisawa 4:29, 31; 5:33; 6:4) Gargaɗin Yesu “kada ku shari’anta” da kuma “kada ku hukunta” bai daina aiki ba yayin da muke gida. Ka tuna cewa yin shari’a ya ƙunshi bi da wasu kamar yadda Jehobah yake bi da mu. Kuma Allah ba ya tsananta mana a hanyar da yake bi da mu. Maimakon haka, yana “yawan tausayi” a kan waɗanda suke ƙaunarsa. (Yakub 5:11) Misali ne mai ban sha’awa da ya kamata mu yi koyi da shi!

Dattawa Suna Hidima “da Gaskiya”

16, 17. (a) Mene ne Jehobah yake bukata daga dattawa? (b) Mene ne dole a yi idan mai zunubi ya ƙi ya nuna ya tuba da gaske, kuma me ya sa?

16 Dukanmu muna da hakkin mu yi shari’a, amma dattawa musamman a ikilisiyar Kirista suke da wannan hakki. Ka lura da kwatanci na annabci na “shugabanni,” ko kuma dattawa, da ke rubuce a Ishaya: “Duba, za a yi wani sarki, sarkin da zai yi mulki cikin adalci, sauran shugabanni za su yi mulki da gaskiya.” (Ishaya 32:1) Hakika, Jehobah yana bukatar dattawa su yi hidima cikin shari’a. Ta yaya za su yi haka?

17 Waɗannan mutane da suka ƙware a ruhaniya sun sani cewa ana bukatar shari’a, ko kuma adalci, a tsabtace ikilisiya. A wasu lokatai, ya wajaba dattawa su yi hukunci bisa laifi mai tsanani. Sa’ad da suke haka, suna tuna cewa shari’a ta Allah tana biɗan ta yi jinƙai idan hakan zai yiwu. Saboda haka, suna ƙoƙarin su kai mai zunubin ga tuba. Amma idan mai zunubin ya ƙi ya nuna ya tuba da gaske bayan dukan ƙoƙarinsu su taimake shi fa? A kamiltacciyar shari’a, Kalmar Allah ta umurci a ɗauki ƙaƙƙarfar mataki: “Ku kawar da mugun nan daga cikinku.” Wannan yana nufin korar mutumin daga ikilisiya. (1 Korintiyawa 5:11-13; 2 Yohanna 9-11) Yana baƙanta wa dattawan rai su ɗauki irin wannan matsayi, amma sun fahimci cewa dole ne domin su kāre tsabta ta ɗabi’a da kuma ta ruhaniya ta ikilisiyar. Duk da haka, suna begen cewa wata rana wannan mai zunubi zai dawo hankalinsa ya komo ikilisiya.—Luka 15:17, 18.

18. Mene ne dattawa suke tunawa da shi sa’ad da suke ba da gargaɗi daga Littafi Mai Tsarki ga wasu?

18 Yin hidima domin shari’a kuma ya ƙunshi yin gargaɗi daga Littafi Mai Tsarki idan ana bukatar haka. Hakika, dattawa ba sa neman laifi daga wasu. Ba kuma suna amfani da kowane zarafi su yi gargaɗi ba. Amma ɗan’uwa mai bi zai iya yin wani “laifi.” Tuna cewa shari’a ta Allah ba azzaluma ba ce ko kuma marar tausayi za ta motsa dattawa su komo da shi kan hanya, kuma za su “yi haka da halin tawali’u, a hankali kuma.” (Galatiyawa 6:1) Saboda haka, dattawa ba za su yi gargaɗi cikin fushi ba ko kuma da baƙar magana. Maimakon haka, gargaɗi da aka yi cikin ƙauna yana ƙarfafa wanda ake yi wa. Har sa’ad da ake tsautawa ta kai tsaye—ana lissafa sakamakon tafarki marar hikima kai tsaye—dattawa suna tuna cewa ɗan’uwa mai bi da ya yi laifi yana cikin tumakin garken Jehobah.b (Luka 15:7) Sa’ad da gargaɗi ko kuma tsautawar ƙauna ce ta motsa shi, kuma aka yi shi cikin ƙauna, zai fi komowa da mai laifin.

19. Wace shawara wani lokaci dattawa suke yankewa, kuma dole ne su yanke shawararsu bisa mene ne?

19 Sau da yawa, dole dattawa su yanke shawara da za ta shafi ’yan’uwansu masu bi. Alal misali, jifa-jifa dattawa suna taruwa su duba ko wasu ’yan’uwa maza a cikin ikilisiya sun kai a naɗa su su zama dattawa ko kuma bayi masu hidima. Dattawan sun san muhimmancin kasancewa marasa son zuciya. Suna bin farillan Allah na yin wannan naɗin ya yi musu ja-gora a shawararsu, ba sa dogara bisa yadda suke ji. Saboda haka, suna yin abu ‘ban da nuna bambanci ko nuna cewa sun fi son wani fiye da sauran.’—1 Timoti 5:21.

20, 21. (a) Mene ne dattawa suke ƙoƙarin su yi, kuma me ya sa? (b) Mene ne dattawa za su yi domin su taimaki “waɗanda ba su da ƙarfin zuciya”?

20 Dattawa suna yin shari’a ta Allah a wasu hanyoyi ma. Bayan ya annabta cewa dattawa za su yi hidima cikin “gaskiya,” Ishaya ya ci gaba da cewa: “Kowannensu zai zama kamar mafaka daga iska, kamar wurin ɓuya daga ruwan ƙanƙara, kamar ’yan rafuffuka cikin dajin yashi, ko inuwar babban dutse a ƙasa mai zafi.” (Ishaya 32:2) Saboda haka, dattawa suna ƙoƙari su zama tushen ƙarfafa da kuma na wartsakewa ga ’yan’uwansu masu bi.

21 A yau, da dukan matsaloli da suke kawo kasala, mutane da yawa suna bukatar ƙarfafa. Dattawa, mene ne za ku yi ku taimaki “waɗanda ba su da ƙarfin zuciya”? (1 Tasalonikawa 5:14) Ku saurare su da tausayi. (Yakub 1:19) Wataƙila su nemi su gaya wa wani da suka amince da shi ‘damuwa’ da take zuciyarsu. (Karin Magana 12:25) Ku tabbatar musu cewa ana bukatarsu, suna da tamani, kuma ana ƙaunarsu—hakika, Jehobah da kuma ’yan’uwansu maza da mata. (1 Bitrus 1:22; 5:6, 7) Bugu da ƙari, za ka iya yin addu’a domin waɗannan kuma tare da su. Saurarar dattijo ya yi addu’a daga zuci dominsu yana da ban ƙarfafa ƙwarai. (Yakub 5:14, 15) Ƙoƙarinku cikin ƙauna domin ku taimake masu raunannun zukata ba zai faɗi banza ba daga Allah na shari’a.

Dattawa suna nuna shari’a ta Jehobah sa’ad da suka ƙarfafa waɗanda suka karaya a zukata

22. A waɗanne hanyoyi ne za mu yi koyi da shari’a ta Jehobah, kuma mene ne sakamakon haka?

22 Hakika, muna kusantar Jehobah ƙwarai ta wajen koyi da shari’arsa! Sa’ad da muka ɗaukaka mizanansa na adalci, sa’ad da muka yi wa wasu bishara mai ceton rai, da kuma sa’ad da muka zaɓi mu mai da hankali bisa halaye masu kyau na ’yan’uwanmu maimakon kushe musu, muna nuna shari’a da ke ta Allah. Dattawa, sa’ad da kuka kāre tsabtar ikilisiya, sa’ad da kuka yi gargaɗi daga Nassosi mai ginawa, da kuma sa’ad da kuka ƙarfafa waɗanda suka karaya a zuci, kuna nuna shari’a ta Allah. Kai, zai faranta wa Jehobah rai idan ya dubo daga sama kuma ya ga cewa mutanensa suna iyakar ƙoƙarinsu su yi “aikin gaskiya” wajen tafiya da Allahnsu!

a Fassarar nan “kada ku yanke wa kowa hukunci” da kuma “kada ku shari’anta kowa,” na nufin “kada ku fara yanke” da kuma “kada ku fara shari’anta.” Duk da haka, marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi amfani ne da umurni a lamirin lokaci mai ci (mai ci gaba). Saboda haka ayyuka da aka kwatanta na kan faruwa tukuna amma za a daina su.

b A 2 Timoti 4:2, Littafi Mai Tsarki ya ce, dattawa dole ne a wasu lokatai su ‘tsauta, su kwaɓe, su yi gargaɗi.’ Kalmar Helenanci da aka fassara “gargaɗar” (pa·ra·ka·leʹo) tana iya nufin “a ƙarfafa.” ’Yar’uwar kalmar Helenancin, pa·raʹkle·tos, tana iya nufin mai roƙo a batun doka. Saboda haka, har sa’ad da dattawa suka tsauta, ya kamata su zama mataimakan waɗanda suke bukatar taimako na ruhaniya.

Tambayoyi don Bimbini

  • Maimaitawar Shari’a 1:16, 17 Mene ne Jehobah yake bukata daga alƙalai a Isra’ila, kuma Mene ne dattawa za su koya daga wannan?

  • Irmiya 22:13-17 Jehobah ya yi gargaɗi game da waɗanne ayyuka na rashin gaskiya ne, kuma me ya sa yin koyi da shari’arsa yake da muhimmanci?

  • Matiyu 7:2-5 Me ya sa ba za mu yi hanzarin kushe wa ’yan’uwanmu masu bi ba?

  • Yakub 2:1-9 Yaya Jehobah yake ɗaukar nuna son zuciya, kuma ta yaya za mu yi amfani da wannan gargaɗin a sha’ani da muke yi da wasu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba