BABI NA 23
“Ya Fara Ƙaunace Mu”
1-3. Waɗanne yanayi ne suka mai da mutuwar Yesu ba kamar wasu ba a tarihi?
A WATA rana a kaka kusan shekara 2,000 da ta shige, an yi wa wani mutum marar laifi hukunci, aka kama shi da laifin da bai yi ba, sai kuma aka gana masa azaba har ya mutu. Ba shi ne mugun kisa na rashin gaskiya na farko ba a tarihi; kuma abin baƙin ciki, ba shi ne zai kasance na ƙarshe ba. Amma, mutuwarsa ba kamar ta wasu ba ce.
2 Yayin da mutumin ya wahala cikin awoyin azaba na ƙarshe, sama kanta ta nuna cewa wannan aukuwar tana da muhimmanci. Ko da yake da tsakar rana ce, farat ɗaya duhu ya rufe ƙasar. In ji wani ɗan tarihi, “rana ta daina haske.” (Luka 23:44, 45) Kafin ya numfasa numfashinsa na ƙarshe, ya faɗi waɗannan kalmomi da ba za a taɓa manta da su ba: “An gama”! Hakika, ta wajen ba da ransa, ya cika wani abu mai ban mamaki. Hadayarsa ita ce nuna ƙauna mafi girma da mutum ya taɓa yi.—Yohanna 15:13; 19:30.
3 Wannan mutumin, hakika, Yesu Kristi ne. Azabarsa da kuma mutuwa a wannan rana mai duhu, ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., sananniya ce ƙwarai. Amma, sau da yawa ana ƙyale wata gaskiya mai muhimmanci. Ko da yake Yesu ya wahala ƙwarai, wani ya wahala ma fiye da haka. Hakika, wani ya ba da hadaya wadda ta fi ma a wannan ranar—nuna ƙauna mafi girma da aka taɓa yi a cikin dukan sararin sama. Wane hali ke nan wannan? Amsar ta ba da gabatarwa ga batu mafi muhimmanci: ƙaunar Jehobah.
Nuna Ƙauna Mafi Girma
4. Ta yaya wani sojan Roma ya ga cewa Yesu ba mutum ba ne kawai, kuma mene ne wannan sojan ya ce?
4 Wani sojan Roma da ya ja-goranci kashe Yesu ya yi mamaki domin duhu da kuma girgizar ƙasa da suka biyo bayan mutuwar Yesu. “Lallai wannan Ɗan Allah ne,” in ji shi. (Matiyu 27:54) Babu shakka, Yesu ba mutum ba ne kawai. Sojan ya taimaka a kashe Ɗa makaɗaici na Allah Maɗaukaki! Yaya tamanin wannan Ɗa wurin Ubansa?
5. Ta yaya za a iya kwatanta yawan lokaci da Jehobah da Ɗansa suke a sama tare?
5 Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “Ɗan fari gaban dukan halitta.” (Kolosiyawa 1:15) Ka yi tunani—Ɗan Jehobah yana raye kafin a halicci duniya ta zahiri. To, tun yaushe Uba da Ɗan suke tare? Wasu masana kimiyya suka kimanta cewa sararin sama tana da shekaru biliyan 13. Kana iya ma nuna yawan wannan lokacin? Don a taimaki mutane su fahimci shekarun sararin sama yadda ’yan kimiyya suka kimanta, wata na’ura ta zana taswirar lokaci mai tsawon ƙafa 360. Yayin da baƙi suke tafiya a wajen wannan taswira, dukan taku da suka yi yana wakiltan shekaru miliyan 75 na rayuwar sararin sama. A ƙarshen taswirar ta lokaci, maki guda ne mai ƙibar gashi ƙwaya ɗaya take wakiltar dukan tarihin ’yan Adam! Duk da haka, ko idan wannan kimantawar daidai ce, dukan taswirar lokacin ba za ta iya wakiltan tsawon rayuwar Ɗan Jehobah ba! Wane aiki yake yi a dukan tsawon wannan lokaci?
6. (a) Mene ne Ɗan Jehobah yake yi a lokacin rayuwarsa kafin ya zo duniya? (b) Wace irin nasaba ce ta kasance tsakanin Jehobah da Ɗansa?
6 Ɗan ya yi farin cikin zama ‘gwanin mai-aiki’ na Ubansa. (Karin Magana 8:30) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu wani abu a cikin dukan halittar da aka yi wadda ba tare da [Ɗan] aka yi ba.” (Yohanna 1:3) Saboda haka, Jehobah da Ɗansa suka yi aiki tare suka halicci dukan wasu abubuwa. Hakika sun kasance tare cikin farin ciki! Babu shakka, mutane da yawa za su yarda cewa ƙauna tsakanin iyaye da yara tana da ƙarfi ƙwarai. Kuma ƙauna “ce take ɗaura dukan kome cikin cikakkiyar ɗayantaka.” (Kolosiyawa 3:14) Saboda haka, waye a tsakaninmu zai fara gwada ƙarfin gami da ya kasance tsakaninsu a cikin wannan lokaci mai yawa sosai? Babu shakka, Jehobah Allah da Ɗansa sun nasabtu cikin gami mafi ƙarfi da ya taɓa faruwa.
7. Sa’ad da Yesu ya yi baftisma, yaya Jehobah ya furta yadda yake ji game da Ɗansa?
7 Duk da haka, Uban ya aiko Ɗansa zuwa duniya a haife shi jariri ɗan mutum. Yin haka na wasu shekaru yana nufin Jehobah dole ya mance da hulɗa ta kurkusa da Ɗansa da yake ƙauna a sama. Da ƙauna mai yawa, ya lura daga sama yayin da Yesu yake girma ya zama cikakken mutum. Sa’ad da yake kimanin shekara 30 da haihuwa, Yesu ya yi baftisma. Ba sai mun yi zaton yadda Jehobah ya ji ba. Uban ya yi magana da kansa daga sama: “Wannan shi ne Ɗana da nake ƙauna, wanda nake jin daɗinsa ƙwarai.” (Matiyu 3:17) Tun da Yesu ya yi dukan abin da aka riga aka annabta, dukan abin da aka umurce shi, Ubansa ya yi farin ciki sosai!—Yohanna 5:36; 17:4.
8, 9. (a) Mene ne aka yi wa Yesu a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., kuma yaya wannan ya shafi Ubansa a sama? (b) Me ya sa Jehobah ya ƙyale Ɗansa ya wahala kuma ya mutu?
8 Amma, yadda Jehobah ya ji a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z. fa? Yaya ya ji sa’ad da aka ci amanar Yesu kuma taron mutane suka kama shi daddare? Abokanan Yesu suka guje shi kuma aka yi masa hukunci marar gaskiya? Da aka yi masa ba’a, aka tufa masa yawu, kuma aka naushe shi? Da aka yi masa bulala, bayansa ya tsatsage? Da aka buga masa ƙusa hannu da ƙafa, bisa dogon gungume aka rataye shi sa’ilin da mutane suke zaginsa? Yaya Uban ya ji yayin da Ɗansa da yake ƙauna ya yi kuka domin ƙunar azaba? Yaya Jehobah ya ji yayin da Yesu ya numfasa numfashi na ƙarshe, kuma lokaci na farko tun daga farkon halitta da Ɗan ba ya raye?—Matiyu 26:14-16, 46, 47, 56, 59, 67; 27:38-44, 46; Yohanna 19:1.
9 Ba magana. Tun da Jehobah yana da motsin rai, azaba da ya sha domin mutuwar Ɗansa ta fi ƙarfin kalma ta bayyana. Abin da za a iya yin bayani a kai shi ne dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale hakan ya faru. Me ya sa Uban ya ƙyale kansa ya sha irin wannan azabar? Dalilin yana rubuce cikin aya ta Littafi Mai Tsarki da aka kira ƙaramar Linjila. Yohanna 3:16 ta ce: “Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin dukan wanda ya ba da gaskiya gare shi kada ya halaka, amma ya sami rai na har abada.” Saboda haka, dalilin Jehobah shi ne: ƙauna. Kyauta ta Jehobah—aiko da Ɗansa ya wahala kuma ya mutu dominmu—shi ne nuni na ƙauna mafi girma da aka taɓa yi.
“Allah . . . ya ba da makaɗaicin Ɗansa”
Ma’anar Ƙaunar Allah
10. Ɗan Adam yana da wace bukata, kuma mene ne ya faru da ma’anar kalmar nan “ƙauna”?
10 Mece ce ma’anar wannan kalmar “ƙauna”? An ce ƙauna ita ce bukata mafi girma da ’yan Adam suke da ita. A dukan rayuwar mutum, mutane suna neman ƙauna, suna rayu saboda ita, su galabaita su mutu saboda rashinta. Abin mamaki, tana da wuyar ma’ana. Hakika, mutane suna yawan magana a kanta. Da akwai littattafai, waƙoƙi rubutattu da na baƙa game da ita a kai a kai. Sakamakon ba ko yaushe yake bayyana ma’anar ƙauna ba. Hakika, kalmar an fiye amfani da ita har ma’anarta ta kasance da wuya.
11, 12. (a) A ina za mu koyi abubuwa da yawa game da ƙauna, kuma me ya sa a nan ne? (b) Waɗanne irin ƙauna ne aka bayyana a cikin harshe na dā na Helenanci, kuma wace kalma ce ta ƙauna aka yi amfani da ita sau da yawa a cikin Nassosin Helenanci na Kirista? (Ka kuma ga hasiya.) (c) Mece ce a·gaʹpe a cikin Littafi Mai Tsarki?
11 Amma, Littafi Mai Tsarki ya koyar da bayani game da ƙauna. Expository Dictionary of New Testament Words na Vine ya lura: “Za a san ƙauna daga aikin da ta motsa ne kawai.” Tarihin Littafi Mai Tsarki game da ayyukan Jehobah ya koyar da mu sosai game da ƙaunarsa—nagarin so da yake da shi ga halittunsa. Alal misali, mene ne zai bayyana game da wannan halin sosai idan ba nuna ƙauna mai zurfi na Jehobah ba da aka kwatanta a baya? A babobi da za su biyo baya, za mu ga wasu misalai masu yawa na ƙaunar Jehobah. Bugu da ƙari, za mu samu fahimi daga asalin kalma ta “ƙauna” da aka yi amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki. A harshen dā na Helenanci, da akwai kalmomi huɗu na “ƙauna.”a Tsakanin waɗannan, wadda aka fi amfani da ita a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci ita ce a·gaʹpe. Wani ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya kira ta “kalma mafi ƙarfi na ƙauna da za a taɓa tunaninta.” Me ya sa?
12 A cikin Littafi Mai Tsarki, A·gaʹpe tana nufin ƙauna da mizani yake yi mata ja-gora. Saboda haka, ta fice sakamako na motsin rai ga abin da wani ya ce ko ya yi. Ta fi faɗi a ma’anarta, ta fi tunani da sani a tushenta. Fiye da kome, ƙauna ta Kirista ba ta da son kai. Alal misali, ka sake duba Yohanna 3:16. Wacce ce “duniya” da Allah yake ƙauna sarai da har ya ba da Ɗansa makaɗaici? Duniya ce ta mutane da za a iya cetonsu. Wannan ya haɗa da mutane da yawa da suke bin tafarkin zunubi. Jehobah yana ƙaunar kowanne kamar abokinsa, kamar yadda ya ƙaunaci mai aminci Ibrahim? (Yakub 2:23) A’a, amma cikin ƙauna Jehobah ya yi wa duka kirki, babban hasara ga kansa. Yana son kowa ya tuba kuma ya canja tafarkinsa. (2 Bitrus 3:9) Mutane da yawa sun yi haka. Waɗannan ya karɓe su da farin ciki a matsayin abokansa.
13, 14. Mene ne ya nuna cewa ƙauna ta Kirista sau da yawa tana haɗe da soyayya?
13 Duk da haka, wasu suna da mummunan ra’ayi game da yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta a·gaʹpe. Suna tunanin cewa tana nufin ƙauna ce marar himma, irinta ilimi. Amma a hakikanin gaskiya ita ce, ƙauna ta Kirista sau da yawa ta haɗa da soyayya mai kyau. Alal misali, sa’ad da Yesu ya ce, “Uban yana ƙaunar Ɗan,” an yi amfani da wata irin kalmar a·gaʹpe. Wannan ƙaunar ba ta da soyayya ce? Ka lura cewa Yesu kuma ya ce, “Uban yana ƙaunar Ɗan,” an yi amfani da wata irin kalmar phi·leʹo. (Yohanna 3:35; 5:20) Ƙaunar Jehobah sau da yawa tana haɗe da soyayya. Duk da haka, ƙauna motsin rai ba ya taɓa rinjayarta. Ko da yaushe mizaninsa na hikima da adalci ne yake yi mata ja-gora.
14 Kamar yadda muka gani, dukan halayen Jehobah masu kyau ne, kamilai, masu ban sha’awa. Amma ƙauna ta fi duka ban sha’awa. Babu abin da yake sa mu matsa kusa da Jehobah haka. Abin farin ciki, ƙauna ita ce halinsa mafi yawa. Ta yaya muka san da haka?
“Allah Ƙauna Ne”
15. Wane furuci Littafi Mai Tsarki ya yi game da halin Jehobah na ƙauna, kuma a wace hanya ce wannan furuci ya kasance farda? (Duba kuma hasiya.)
15 Littafi Mai tsarki ya faɗi wani abu game da ƙauna da ba a taɓa faɗa ba game da wasu shahararrun halaye na Jehobah. Nassosi ba su ce Allah iko ba ne ko kuma cewa Allah shari’a ko kuma ma su ce Allah hikima ne. Yana da waɗannan halaye, shi ne Tushen waɗannan, kuma ba shi da na biyu a dukan waɗannan uku. Amma game da hali na huɗun, an faɗi wani abu mafi zurfi: “Allah ƙauna ne.”b (1 Yohanna 4:8) Mene ne wannan yake nufi?
16-18. (a) Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce “Allah ƙauna ne”? (b) A dukan halittun da suke duniya me ya sa mutum ne alama da ta dace na halin Jehobah na ƙauna?
16 “Allah ƙauna ne” ba abu ba ne mai sauƙi, kamar a ce, “Allah ya yi daidai da ƙauna.” Ba zai dace ba kuma mu juya furucin mu ce “ƙauna Allah ne.” Jehobah ya wuce hali da ba a gani. Shi wani ne mai motsin rai dabam dabam da kuma halaye ƙari ga ƙauna. Ƙauna ce ta cika Jehobah. Saboda haka wani littafin neman bayani ya ce game da ayar: “Ainihin Allah ko kuma yanayinsa ƙauna ne.” Za mu iya tunaninsa a wannan hanyar: Ikon Jehobah yana sa shi ya yi abu. Shari’arsa da hikima suna ja-gorarsa a hanyar da yake aikata abubuwa. Amma ƙaunar Jehobah take motsa shi ya yi abu. Kuma ƙaunarsa tana kasancewa a cikin dukan hanyar da ya yi amfani da wasu halayensa.
17 Sau da yawa ana cewa Jehobah shi ne ƙauna aini. Saboda haka, idan muna so mu koyi game da ƙauna ta ƙa’ida, dole ne mu koyi game da Jehobah. Hakika, za mu ga wannan kyakkyawan hali a mutane ma. Amma me ya sa akwai shi? A lokacin halitta, Jehobah ya yi wannan maganar, a bayyane, ga Ɗansa ne: “Bari mu yi mutum a kamanninmu da kuma siffarmu.” (Farawa 1:26) A dukan halittu da suke cikin duniya, maza ne da mata kawai za su iya zaɓa su ƙaunaci Ubansu na sama kuma su yi koyi da shi. Ka tuna cewa Jehobah ya yi amfani da halittu dabam dabam ya alamta halayensa na musamman. Duk da haka, Jehobah ya zaɓi wannan halitta mafi matsayi na duniya, mutum, ya alamta Halinsa mafi girma, ƙauna.—Ezekiyel 1:10.
18 Sa’ad da muka yi ƙauna a hanya marar son kai, na ƙa’ida, muna nuna hali mafi girma na Jehobah ne. Kamar yadda manzo Yohanna ya rubuta ne: “Muna ƙauna gama Allah ne ya fara ƙaunace mu.” (1 Yohanna 4:19) Amma a waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya ƙaunace mu da farko?
Jehobah Ya Ɗauki Mataki
19. Me ya sa za a ce ƙauna muhimmiya ce a aikin halitta na Jehobah?
19 Ƙauna ba sabuwar aba ba ce. To, mene ne ya motsa Jehobah ya fara halitta? Ba domin kewa ba ne saboda haka ya nemi abokin zama ba. Jehobah cikakke ne kuma mai wadatar zuci, bai rasa kome ba da wani zai ba shi. Amma ƙaunarsa, hali mai ƙarfi, ya motsa shi ya so ya more rayuwa da halittu masu hankali waɗanda za su yi godiya ga irin wannan kyautar. ‘Farkon halittar Allah,’ shi ne Ɗansa makaɗaici. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 3:14) Sai Jehobah ya yi amfani da gwanin aikinsa ya sa wasu abubuwa suka wanzu, na farko mala’iku. (Ayuba 38:4, 7; Kolosiyawa 1:16) An albarkace su da ’yanci, fahimi, da kuma motsin rai, waɗannan manyan ruhohi suna da zarafin kafa dangantaka tasu da junansu—da wasu, fiye da haka kuma, da Jehobah Allah. (2 Korintiyawa 3:17) Saboda haka, sun yi ƙauna domin an ƙaunace su ne da farko.
20, 21. Adamu da Hauwa’u suna da wane tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunarsu, duk da haka, mene ne suka yi?
20 Haka yake da ’yan Adam ma. Da farko, Adamu da Hauwa’u suna cike da ƙauna. Dukan inda suka juya a cikin gidansu Aljanna a Adnin, suna ganin tabbacin ƙaunar Ubansu. Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh Allah ya shuka gona a gabas mai suna Eden, ya sa mutumin da ya siffata a cikinta.” (Farawa 2:8) Ka taɓa zuwa lambu wanda yake da kyaun gaske? Mene ne ya faranta maka rai ƙwarai? Haske da yake zuwa daga bayan ganyaye? Launi dabam dabam na furanni? Kukan tsuntsaye da kuma ƙarar ƙwari? Yaya kuma ƙamshin itatuwa, ’ya’yan itatuwa, da kuma furanni? Ko yaya dai, babu wani lambu da za a gwada da na Adnin. Me ya sa?
21 Wancan lambun Jehobah ne kansa ya kafa shi! Dole ne ya kasance marar kwatanci domin kyaunsa. Dukan itace mai ban sha’awa don kyau ko kuma mai ɗanɗano ya kasance a wurin. Lambun yana samun ban ruwa da kyau, yana da fili, kuma yana cike da dabbobi iri dabam dabam. Adamu da Hauwa’u suna da dukan abin da zai sa rayuwarsu ta kasance da farin ciki da kuma gamsuwa, haɗe da aiki mai gamsarwa da kuma abokin zama kamiltacciya. Jehobah ya ƙaunace su da farko, kuma suna da dalilai masu yawa su yi ƙaunarsa. Amma sun kasa yin haka. Maimakon su yi biyayya da Ubansa na sama cikin ƙauna, suka yi masa tawaye domin son kai.—Farawa, sura 2.
22. Ta yaya yadda Jehobah ya aikata ga tawaye na Adnin ya ba da tabbacin cewa ‘ƙaunarsa ba ta ƙarewa’?
22 Lalle wannan zai yi wa Jehobah ciwo! Amma wannan tawayen ya ɓata zuciyarsa mai ƙauna ne? A’a! “Ƙaunarsa marar canjawa ta har abada ce.” (Zabura 136:1) Saboda haka, babu ɓata lokaci ya ƙudura ya yi tanadi cikin ƙauna ya ceci ’ya’yan Adamu da Hauwa’u masu zuciyar kirki. Kamar yadda muka gani, waɗannan tanadin sun haɗa da hadaya ta fansa na Ɗansa wanda yake ƙauna, wanda ya shafi Ubansa ƙwarai.—1 Yohanna 4:10.
23. Mene ne dalili ɗaya da ya sa Jehobah ‘Allah ne mai farin ciki,’ kuma wace tambaya ce mai muhimmanci za a bincika a babi na gaba?
23 Hakika, daga farko Jehobah ya ɗauki mataki ya nuna ƙauna ga mutane. A hanyoyi marasa iyaka, ‘ya ƙaunace mu da farko.’ Ƙauna tana ɗaukaka jituwa da farin ciki, saboda haka ba abin mamaki ba ne da aka kwatanta Jehobah da cewa ‘Allah mai farin ciki.’ (1 Timoti 1:11) Amma, tambaya mai muhimmanci ta taso. Jehobah yana ƙaunar kowannenmu ne? Babi na gaba zai bincika wannan batun.
a Kalmar aikatau phi·leʹo, mai nufin “ka so wani, ka yi muradin wani, ka so (kamar yadda wani zai ji game da aboki na kud da kud ko kuma ɗan’uwa),” an yi amfani da ita sau da yawa a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci. ’Yar’uwar kalmar stor·geʹ, ko kuma ƙauna ta iyali, an yi amfani da ita a 2 Timoti 3:3 na nuna cewa irin wannan ƙaunar ba za ta kasance ba a kwanaki na ƙarshe. Eʹros, ƙauna ta soyayya tsakanin jinsi, ba a yi amfani da ita ba cikin Nassosin Helenanci na Kirista, ko da yake irin wannan ƙauna an yi maganar ta cikin Littafi Mai tsarki.—Karin Magana 5:15-20.
b Furuci biyu na Nassi suna da irin tsari ɗaya: “Allah haske ne” da “Allahnmu wuta ne mai cinyewa.” (1 Yohanna 1:5; Ibraniyawa 12:29) Amma waɗannan dole ne a fahimce su kwalliya ce ta magana, domin sun kamanta Jehobah da abubuwa na zahiri. Jehobah kamar haske yake, domin shi mai tsarki ne kuma mai adalci. Babu “duhu,” ko ƙazanta, a gare shi. Kuma za a kwatanta shi da wuta domin amfani da ikonsa na halaka.