Darussan Littafi Mai-Tsarki Don Mahawwara
1. Abin Tuni, Mass
A. Yin bikin Abincin Maraice na Ubangiji
Ana kiyaye shi sau ɗaya cikin shekara a kwanan wata na Faska. Lu 22:1, 17-20; Fit 12:14
Ana tuna da mutuwar hadaya na Kristi. 1Ko 11:26; Mt 26:28
Waɗanda ke da bege na samaniya suna ci. Lu 22:29, 30; 12:32, 37
Yadda mutum yake sani cewa yana da irin begen nan. Ro 8:15-17
B. Mass ba bisa nassi ba ne
Gafartawan zunubai yana bukatar zub da jini. Ibr 9:22
Kristi shine Masakaici mai-girma na sabuwar alkawari. 1Ti 2:5, 6; Yo 14:6
Kristi cikin sama yake; ba wani firist ne ya sauƙad da shi ba. Ay Ma 3:20, 21
Ba a bukatar maimaita hadayar Kristi kuma. Ibr 9:24-26; 10:11-14
2. Addini
A. Addini na gaskiya ɗaya ne kaɗai
Bege ɗaya, imani ɗaya, baftisma ɗaya. Afi 4:5, 13
An ba su aikin almajirtadwa. Mt 28:19; Ay Ma 8:12; 14:21
Za a gane ta ta wurin halinta. Mt 7:19, 20; Lu 6:43, 44; Yo 15:8
Ƙauna, jiyayya tsakanin mambobi. Yo 13:35; 1Ko 1:10; 1Yo 4:20
B. An hukunta koyaswan ƙarya sarai
Yesu ya hukunta koyaswan ƙarya. Mt 23:15, 23, 24; 15:4-9
Ya yi haka domin ya kare waɗanda aka makantar. Mt 15:14
Gaskiya ya ’yantar da su don zama almajiran Yesu. Yo 8:31, 32
C. Canja addinin mutum zai dace idan an gano ba daidai ba ne
Gaskiya yana ’yantarwa; yana nuna cewa mutane da yawa ba daidai suke ba. Yo 8:31, 32
Israilawa, wasu, sun bar sujadarsu na dā. Jos 24:15; 2Sar 5:17
Kiristoci na farko sun canja ra’ayoyinsu. Ga 1:13, 14; Ay Ma 3:17, 19
Bulus ya canja addininsa. Ay Ma 26:4-6
An ruɗas da dukan duniya; tilas ne a sake azanci. R. Yo 12:9; Ro 12:2
D. Cewa da alamar “dukan addinai suna da kyau” ba tabbacin amincewar Allah ba ne
Allah ya kafa mizani don sujada. Yo 4:23, 24; Yaƙ 1:27
Ba shi da kyau idan ba yadda Allah ya nufa ba ne. Ro 10:2, 3
Za a iya ƙi da “ayuka masu-kyau.” Mt 7:21-23
Ana gane su ta wurin hali. Mt 7:20
3. Addu’a
A. Addu’o’i da Allah ke amsawa
Allah yana saurarawa ga addu’o’in mutane. Za 145:18; 1Bi 3:12
Ba ya saurara ga marasa adilci sai dai sun canja hanyarsu. Ish 1:15-17
Tilas ne mu yi addu’a cikin sunan Yesu. Yo 14:13, 14; 2Ko 1:20
Tilas ne mu yi addu’a cikin jituwa da nufin Allah. 1Yo 5:14, 15
Bangaskiya muhimmi ne. Yaƙ 1:6-8
B. Maimaitawan banza, addu’o’i ga Maryamu ko kuma “waliyai” wofi ne
Tilas ne mu yi addu’a ga Allah cikin sunan Yesu. Yo 14:6, 14; 16:23, 24
Ba za a saurara ga kalmomin da ake maimaitawa ba. Mt 6:7
4. Annabawan Ƙarya
A. An annabta game da annabawan ƙarya; sun wanzu a kwanan manzanni
Sarauta zai nuna waɗanda ke annabawan ƙarya. K. Sha 18:20-22; Lu 6:26
An annabta zuwansu; za a san su ta wurin ayukansu. Mt 24:23-26; 7:15-23
5. Armageddon
A. Yaƙin Allah don kawo ƙarshe ga mugunta
An tattara al’ummai zuwa Armageddon. R. Yo 16:14, 16
Allah yana faɗā, yana amfani da Ɗa da kuma mala’iku. 2Ta 1:6-9; R. Yo 19:11-16
Yadda za mu iya tsira. Zep 2:2, 3; R. Yo 7:14
B. Ba a ɓāta ƙaunar Allah ba
Duniya ta lalace ƙwarai da gaske. 2Ti 3:1-5
Allah yana da haƙuri, amma shari’a tana bukatar aikawa. 2Bi 3:9, 15; Lu 18:7, 8
Tilas ne miyagu su ɓace don adilai su ni’imta. Mis 21:18; R. Yo 11:18
6. Asabaci
A. Ba a bukaci Kiristoci su kiyaye asabaci ba
An kau da dokar ta wurin mutuwar Yesu. Afi 2:15
Ba a bukatar Kiristoci su kiyaye asabaci. Kol 2:16, 17; Ro 14:5, 10
An tsauta ma masu kiyaye Asabaci, da kuma sauransu. Ga 4:9-11; Ro 10:2-4
Shiga cikin hutun Allah ta wurin bangaskiya da kuma biyayya. Ibr 4:9-11
B. Israila ta dā ce kaɗai aka bukace su su kiyaye Asabaci
An soma kiyaye Asabaci bayan Fitowa ne. Fit 16:26, 27, 29, 30
Babban abu ne ga Israila ta jiki kamar alama. Fit 31:16, 17; Za 147:19, 20
An kuma bukaci shekaru na Asabaci ƙarƙashin Doka. Fit 23:10, 11; Le 25:3, 4
Asabaci ba wani abu ne da ke da muhimmanci ga Kiristoci ba. Ro 14:5, 10; Ga 4:9-11
C. Asabaci na hutun Allah (rana ta 7 na “makon” halitta)
Ya soma a gamawar halitta na duniya. Fa 2:2, 3; Ibr 4:3-5
Ya ci gaba har ya wuce rayuwar Yesu a duniya. Ibr 4:6-8; Za 95:7-9, 11
Kiristoci suna hutawa daga ayuka don son rai ne. Ibr 4:9, 10
Zai ƙare lokacinda Mulkin ya gama aiki cikin duniya. 1Ko 15:24, 28
7. Aure
A. Tilas ne gamin aure ya zama da daraja
An kamanta shi da Kristi da kuma amarya. Afi 5:22, 23
Tilas ne gadon aure ya zama mara ƙazanta. Ibr 13:4
An gargaɗe aurarru kada su rabu da juna. 1Ko 7:10-16
Por·neiʹa ne kaɗai dalilin Nassi na kisan aure. Mt 19:9
B. Tilas ne Kiristoci su yi biyayya da ƙa’idar kan-gida
Tilas ne mijin kamar kai ya ƙaunaci, lura da iyalin. Afi 5:23-31
Mata, ta sarayad da kai, ƙaunaci, yi biyayya ga miji. 1Bi 3:1-7; Afi 5:22
Tilas ne yara su yi biyayya. Afi 6:1-3; Kol 3:20
C. Nawayar iyaye Kirista ga yara
Tilas ne su nuna ƙauna, bada lokaci, kulawa. Tit 2:4
Kada su cakune su. Kol 3:21
Su tanadar, duk da abubuwa na ruhaniya. 2Ko 12:14; 1Ti 5:8
Su koyad da su don rayuwa. Afi 6:4; Mis 22:6, 15; 23:13, 14
D. Ya kamata Kiristoci su auri Kiristoci ne kaɗai
Yi aure “cikin Ubangiji” kaɗai. 1Ko 7:39; K. Sha 7:3, 4; Ne 13:26
E. Auren mata fiye da ɗaya ba bisa Nassi ba ne
Tun asali dai ya kamata mutum ya kasance da mata ɗaya kawai. Fa 2:18, 22-25
Yesu ya kafa wani mizani ga Kiristoci. Mt 19:3-9
Kiristoci na farko ba sua aure abokin aure fiye da ɗaya ba. 1Ko 7:2, 12-16; Afi 5:28-31
8. Bada Shaida
A. Tilas ne dukan Kiristoci su bada shaida, faɗi bishara
Tilas ne su nuna yarda da Yesu a gaban mutane kafin a amince da su. Mt 10:32
Tilas ne su zama masu-aika Kalmar, su nuna bangaskiya. Yaƙ 1:22-24; 2:24
Ya kamata sabobbi, ma, su zama masu koyaswa. Mt 28:19, 20
Bada shela a fili yana kawo ceto. Ro 10:10
B. Akwai bukatar sake ziyara, cin gaba da bada shaida
Tilas ne a bada faɗaka game da ƙarshe. Mt 24:14
Irmiya ya yi shelar ƙarshen Urushalima cikin shekaru da yawa. Irm 25:3
Kamar Kiristoci na farko fa, ba za mu dena ba. Ay Ma 4:18-20; 5:28, 29
C. Tilas ne mu bada shaida don zama a ’yance daga alhakin jini
Tilas ne mu faɗakad game da ƙarshe da ke zuwa. Eze 33:7; Mt 24:14
Ƙin yin haka yana jawo alhakin jini. Eze 33:8, 9; 3:18, 19
Bulus a ’yance yake daga alhakin jini; ya yi shelar gaskiya sosai. Ay Ma 20:26, 27; 1Ko 9:16
Yana cetas da mai-bada shaidar da kuma wanda ke saurarawa. 1Ti 4:16; 1Ko 9:22
9. Baftisma
A. Farilla ce na zama Kirista
Yesu ya kafa misalin. Mt 3:13-15; Ibr 10:7
Alamar ƙi da ko kuwa keɓewar kai. Mt 16:24; 1Bi 3:21
Ga waɗanda sun isa a koyad da su ne kawai. Mt 28:19, 20; Ay Ma 2:41
Nutsawa cikin ruwa ita ce hanyar da ta dace. Ay Ma 8:38, 39; Yo 3:23
B. Baya wanke zunubai
Ba a yi ma Yesu baftisma don a wanke zunubai ba. 1Bi 2:22; 3:18
Jinin Yesu yana wanke zunubai. 1Yo 1:7
10. Bautar Kakanni
A. Bauta ma kakanni wofi ne
Kakanni matattu ne, marasa-rai. Mai-Wa 9:5, 10
Kakanni na farko basu cancanci a bauta masu ba. Ro 5:12, 14; 1Ti 2:14
Allah ya haramta irin bautar nan. Fit 34:14; Mt 4:10
B. Za a iya girmama yan-Adam, amma Allah ne kaɗai za a bauta ma
Ya kamata matasa su girmama tsofaffin mutane. 1Ti 5:1, 2, 17; Afi 6:1-3
Amma Allah ne kaɗai za a bauta ma. Ay Ma 10:25, 26; R. Yo 22:8, 9
11. Bauta ma Maryamu
A. Maryamu uwar Yesu ce, ba “uwar Allah” ba ce
Allah ba shi da masomi. Za 90:2; 1Ti 1:17
Maryamu uwar Ɗan Allah ce, cikin zamansa na duniya. Lu 1:35
Allah ba shi da masomi. Za 90:2; 1Ti 1:17
B. Maryamu ba ta ci gaba da zama “budurwa” ba
Ta auri Yusufu. Mt 1:19, 20, 24, 25
Ta haifi wasu yara kuma ban da Yesu. Mt 13:55, 56; Lu 8:19-21
Waɗannan a lokacin ba “yan’uwansa na ruhaniya” ba ne. Yo 7:3, 5
12. Ceto
A. Ceto daga Allah ne ta wurin hadayar fansar Yesu
Rai kyautar Allah ne ta wurin Ɗansa. 1Yo 4:9, 14; Ro 6:23
Ceto yana yiwuwa ta wurin hadayar Yesu ne kaɗai. Ay Ma 4:12
Aiki ba shi yiwuwa cikin “tuba a bakin mutuwa.” Yaƙ 2:14, 26
Tilas ne a yi aiki sosai don a samu. Lu 13:23, 24; 1Ti 4:10
B. “Ceto sau ɗaya shi kenan” ba bisa Nassi yake ba
Waɗanda suke da ruhu mai-tsarki sukan faɗi. Ibr 6:4, 6; 1Ko 9:27
Israilawa da yawa sun hallaka ko da shike an cetas da su daga Masar. Yah 5
Ceto baya zuwa hakanan kawai ba. Fib 2:12; 3:12-14; Mt 10:22
Waɗanda suke juya baya sukan fi dā muni. 2Bi 2:20, 21
C. “Ceto ga kowa” ba bisa nassi yake ba
Wasu ba za su iya tuba ba. Ibr 6:4-6
Allah ba ya jin daɗin mutuwar miyagu. Eze 33:11; 18:32
Amma ƙauna ba ta yarda ma rashin adilci. Ibr 1:9
Za a hallaka miyagu. Ibr 10:26-29; R. Yo 20:7-15
13. Coci
A. Coci na ruhaniya, an gina shi bisa Kristi
Allah baya zama cikin haikalai da mutane suka gina. Ay Ma 17:24, 25; 7:48
Coci na gaskiya haikali ne na ruhaniya na rayayyen duwatsu. 1Bi 2:5, 6
Kristi, dutse na ƙusurwa; manzanni, tushe na biyu. Afi 2:20
Za a bauta ma Allah cikin ruhu da gaskiya. Yo 4:24
B. Ba a gina coci bisa Bitrus ba
Yesu baya ce an gina coci bisa Bitrus ba. Mt 16:18
An nuna Yesu kamar ‘dutse.’ 1Ko 10:4
Bitrus ya nuna Yesu kamar tushe. 1Bi 2:4, 6-8; Ay Ma 4:8-12
14. Dawowar Kristi
A. Zai dawo yadda yan-Adam ba za su gan shi ba
Ya gaya ma almajirai cewa duniya ba za ta gan shi kuma ba. Yo 14:19
Almajirai ne kaɗai suka gan hawan; hakanan ma dawowar. Ay Ma 1:6, 10, 11
A cikin sama, ruhu mara-ganuwa ne. 1Ti 6:14-16; Ibr 1:3
Zai dawo cikin ikon Mulki na samaniya. Da 7:13, 14
B. Ana ganewa ta wurin abubuwan da ake gani
Almajirai sun nemi alamar bayanuwa. Mt 24:3
Kiristoci suna ‘ganin’ bayanuwar ta wurin ganewa. Afi 1:18
Aukuwa da yawa sun nuna tabbacin bayanuwar. Lu 21:10, 11
Magabta za su ‘gani’ yayinda hallaka zai faɗa masu. R. Yo 1:7
15. Duniya
A. Nufin Allah ga duniya
An yi aljanna a duniya don kamiltattun mutane. Fa 1:28; 2:8-15
Nufin Allah tabbatacce ne. Ish 55:11; 46:10, 11
Za a cika duniya da kamiltattun mutane, masu-salama. Ish 45:18; Za 72:7; Ish 9:6,7
Za a maido da Aljanna ta wurin Mulkin. Mt 6:9, 10; R. Yo 21:3-5
B. Ba za a taɓa hallakar ko kuma yi rashin mutane a cikinta ba
Duniya ta zahiri za ta zama har abada. Mai-Wa 1:4; Za 104:5
Mutane na lokacin Nuhu aka hallakas, ba duniya ba. 2Bi 3:5-7; Fa 7:23
Misali ya bada begen tsira a lokacinmu. Mt 24:37-39
Za a hallakar da miyagu; “taro mai-girma” za su tsira. 2Ta 1:6-9; R. Yo 7:9, 14
16. Dunƙulin-Alloli-Uku
A. Allah, Uban, Mutum guda ne, shine mafi-girma cikin sararin halitta
Allah ba mutum uku ba ne. K. Sha 6:4; Mal 2:10; Mk 10:18; Ro 3:29, 30
An halicce ɗan; Allah shi kaɗai ne dā. R. Yo 3:14; Kol 1:15; Ish 44:6
Allah masaraucin sararin halitta ne tun dā. Fib 2:5, 6; Da 4:35
Allah ne za a ɗaukaka fiye da kowa. Fib 2:10, 11
B. Ɗan kasa da Uban yake kafin da kuma bayan wanzuwarsa a duniya
Ɗan yana biyayya cikin sama, Uban ne ya aiko shi. Yo 8:42; 12:49
Ya yi biyayya a duniya, Uban ne ya fi girma. Yo 14:28; 5:19; Ibr 5:8
An ɗaukaka shi a sama, har ila ƙarami ne shi. Fib 2:9; 1Ko 15:28; Mt 20:23
Jehovah shine kan Kristi da kuma Allah. 1Ko 11:3; Yo 20:17; R. Yo 1:6
C. Ɗayantakar Allah da Kristi
Kullum suna cikin cikakkiyar jituwa. Yo 8:28, 29; 14:10
Ɗayantaka, kamar yadda na miji da mata suke. Yo 10:30; Mt 19:4-6
Tilas ne dukan masu-bi su kasance da irin ɗayantakan nan. Yo 17:20-22; 1Ko 1:10
Sujada ɗaya na Jehovah ta wurin Kristi har abada. Yo 4:23, 24
D. Ruhu mai-tsarki na Allah ikon aikinsa ne
Iko ne, ba mutum ba. Mt 3:16; Yo 20:22; Ay Ma 2:4, 17, 33
Ba mutum ne cikin sama tare da Allah da kuma Kristi ba. Ay Ma 7:55, 56; R. Yo 7:10
Allah ne ya umurce shi ya cim ma nufe-nufensa. Za 104:30; 1Ko 12:4-11
Waɗanda suke bauta ma Allah suna samunsa, yana ja-gorance su. 1Ko 2:12, 13; Ga 5:16
17. Fansa
A. An bada ran Yesu na mutum kamar “fansa domin duka”
Yesu ya bada ransa fansa. Mt 20:28
Darajar jini da aka zubas ya tanadar da gafarar zunubi. Ibr 9:14, 22
Hadaya guda ta isa ga dukan lokaci. Ro 6:10; Ibr 9:26
Fa’idodi ba sua zuwa hakanan kawai; tilas mu yarda da haka. Yo 3:16
B. Madaidaicin farashi ne
An halicci Adamu kamiltacce. K. Sha 32:4; Mai-Wa 7:29; Fa 1:31
Ya yi hasarar kamiltawa na kansa da kuma na yaran ta wurin zunubi. Ro 5:12, 18
Yaran sun zama babu bege; ana bukatar daidai kamanin Adamu. Za 49:7; K. Sha 19:21
Kamiltaccen ran mutum na Yesu fansa ne. 1Ti 2:5, 6; 1Bi 1:18, 19
18. Giciye
A. An rataye Yesu bisa gungume na azaba kamar abin zargi
An rataye Yesu bisa gungumen kisa ko kuwa itace. Ay Ma 5:30; 10:39; Ga 3:13
Tilas ne Kiristoci su ɗauki gungume kamar zargi. Mt 10:38; Lu 9:23
B. Ba za a bauta masa ba
Rataye gungumen Yesu zargi ne. Ibr 6:6; Mt 27:41, 42
Yin amfani da giciye cikin sujada bautan gumaka ne. Fit 20:4, 5; Irm 10:3-5
Yesu ruhu ne, ba shi bisa gungume kuma. 1Ti 3:16; 1Bi 3:18
19. Haɗin Ɗarikoki
A. Ba hanyar Allah ba ce haɗa kai da wasu addinai
Hanya ɗaya ce kaɗai, ƙunƙunta ce, kaɗan ne ke samunta. Afi 4:4-6; Mt 7:13, 14
An gargaɗas cewa koyaswan ƙarya yana ƙazantarwa. Mt 16:6, 12; Ga 5:9
An umurce mu mu ware kanmu. 2Ti 3:5; 2Ko 6:14-17; R. Yo 18:4
B. Wai “dukan addinai suna da kyau” ba gaskiya ba ne
Wasu suna da himma amma ba daidai yake ga Allah ba. Ro 10:2, 3
Mummunan abu yakan ɓata abinda ke mai-kyau. 1Ko 5:6; Mt 7:15-17
Masu koyaswan ƙarya suna jawo hallaka. 2Bi 2:1; Mt 12:30; 15:14
Sujada mai-tsabta tana bukatar yin sujada na kaɗai. K. Sha 6:5, 14, 15
20. Halitta
A. Ya jitu da kimiyya na gaske; bai yarda da ra’ayin juyin rai ba
Kimiyya ya jitu da tsarin halitta. Fa 1:11, 12, 21, 24, 25
Dokar Allah na “iri” gaskiya ne. Fa 1:11, 12; Yaƙ 3:12
B. Kwanakin halitta ba kwanaki na awa 24 ba ne
“Kwana” zai iya nufin tsawon lokaci. Fa 2:4
Kwana a wurin Allah zai iya zama dogon lokaci. Za 90:4; 2Bi 3:8
21. Hamayya, Tsanani
A. Dalilin hamayya game da Kiristoci
An tsargi Yesu, ya annabta hamayya. Yo 15:18-20; Mt 10:22
Manne ma ƙa’idodi da ke daidai yana shar’anta duniya. 1Bi 4:1, 4, 12, 13
Shaitan, allah na wannan tsarin, yana hamayya da Mulkin. 2Ko 4:4; 1Bi 5:8
Kirista ba ya tsoro, Allah zai kiyaye. Ro 8:38, 39; Yaƙ 4:8
B. Kada mata ta yarda miji ya raba ta da Allah
Ta sani fa; wasu za su iya zuga shi. Mt 10:34-38; Ay Ma 28:22
Tilas ta dogara ga Allah da kuma Kristi. Yo 6:68; 17:3
Ta wurin amincinta za ta iya cetas da shi ma. 1Ko 7:16; 1Bi 3:1-6
Miji shine kan, amma ba shi zai zaɓi irin sujada da za a yi ba. 1Ko 11:3; Ay Ma 5:29
C. Kada miji ya yarda ma mata ta hana shi daga bauta ma Allah
Tilas ne ya yi ƙaunar mata da iyali, biɗi masu rai. 1Ko 7:16
Yana da nawayar tsai da shawara, yi tanadi. 1Ko 11:3; 1Ti 5:8
Allah yana ƙaunar mutum wanda ke tsayawa don gaskiya. Yaƙ 1:12; 5:10, 11
Karya ƙa’ida don samun salama baya kawo tagomashin Allah. Ibr 10:38
Bishe iyali zuwa farinciki cikin sabuwar duniya. R. Yo 21:3, 4
22. Iblis, Aljannu
A. Iblis mutum ne na ruhu
Ba wani mugunta ne cikin mutum ba amma mutum ne na ruhu. 2Ti 2:26
Iblis mutum ne kamar mala’iku. Mt 4:1, 11; Ayu 1:6
Ya mai da kansa Iblis ta wurin mugun sha’awa. Yaƙ 1:13-15
B. Iblis shine masaraucin duniya mara-ganuwa
Duniya tana ƙarƙashin sarrafawarsa kamar allah. 2Ko 4:4; 1Yo 5:19; R. Yo 12:9
An ƙyale shi har sai an warware muhawwaran. Fi 9:16; Yo 12:31
Za a sa shi a rami, sa’annan kuma hallakas da shi. R. Yo 20:2, 3, 10
C. Aljannu mala’iku ne da suka yi tawaye
Sun haɗa hannu da Shaitan kafin Rigyawa. Fa 6:1, 2; 1Bi 3:19, 20
An sauƙar da su, an yanke su daga dukan ganewa. 2Bi 2:4; Yah 6
Suna yaƙi da Allah, zalunta mutane. Lu 8:27-29; R. Yo 16:13, 14
Za a hallakas da su tare da Shaitan. Mt 25:41; Lu 8:31; R. Yo 20:2, 3, 10
23. Jehovah, Allah
A. Sunan Allah
“Allah” lakabi mara-taƙaici ne; Ubangijinmu yana da sunansa. 1Ko 8:5, 6
Mukan yi addu’a don a tsarkake sunansa. Mt 6:9, 10
Jehovah shine sunan Allah. Za 83:18; Fit 6:2, 3; 3:15; Ish 42:8
Sunan cikin KJ. Fit 6:3 (Dy sharhi na ƙarƙashin matani). Za 83:18; Ish 12:2; 26:4
Yesu ya sanas da sunan. Yo 17:6, 26; 5:43; 12:12, 13, 28
B. Wanzuwar Allah
Ba ya yiwuwa a ga Allah kuma rayu. Fit 33:20; Yo 1:18; 1Yo 4:12
Ba a bukatar ganin Allah kafin a gaskata da shi ba. Ibr 11:1; Ro 8:24, 25; 10:17
An san Allah ta wurin ayukansa da ake gani. Ro 1:20; Za 19:1, 2
Cikawar annabci yana tabbatar da wanzuwar Allah. Ish 46:8-11
C. Ingancin Allah
Allah ƙauna ne. 1Yo 4:8, 16; Fit 34:6; 2Ko 13:11; Mik 7:18
Mafifici ne cikin hikima. Ayu 12:13; Ro 11:33; 1Ko 2:7
Mai-gaskiya ne, mai-shari’ar adilci. K. Sha 32:4; Za 37:28
Maɗaukaki duka ne, yana da dukan iko. Ayu 37:23; R. Yo 7:12; 4:11
D. Ba Allah ɗaya ne duka ke yin masa sujada ba
Hanya da kamar mai-kyau ne ba daidai yake kullum ba. Mis 16:25; Mt 7:21
Hanyoyi biyu, ɗaya ce kaɗai ke bishe zuwa rai. Mt 7:13, 14; K. Sha 30:19
Akwai alloli da yawa amma Allah na gaskiya ɗaya ne tak. 1Ko 8:5, 6; Za 82:1
Sanin Allah na gaskiya yana da muhimmanci don samun rai. Yo 17:3; 1Yo 5:20
24. Jini
A. Haye jini yana ɓata tsarkin jini
An gaya ma Nuhu cewa jini da tsarki yake, rai ne. Fa 9:4, 16
Dokar alkawari ta haramta cin jini. Le 17:14; 7:26, 27
An maimaita haramtarwar ga Kiristoci. Ay Ma 15:28, 29; 21:25
B. Zancen cetas da rai ba hujjar taka dokar Allah ba ne
Yin biyayya ta fi bada hadaya. 1Sam 15:22; Mk 12:33
Sa ran mutum gaba da dokar Allah kasada ce. Mk 8:35, 36
25. Kaddara
A. Ba bisa kaddara mutum yake ba
Nufin Allah a tabbace yake. Ish 55:11; Fa 1:28
An ba kowa iya zaɓa bauta ma Allah. Yo 3:16; Fib 2:12
26. Kirgen kwanaki
A. 1914 (A.Z.) ya kawo ƙarshen Lokuttan Al’ummai
An katse wa jerin masu-sarauta, 607 K.Z. Eze 21:25-27
“Wokatai bakwai” za su shige har sai an maido da mulki. Da 4:32, 16, 17
Bakwai = wokatai 2 × 3 1/2, ko kuma kwanaki 2 × 1,260. R. Yo 12:6, 14; 11:2, 3
Kwana guda don shekara. [Shekaru 2,520 kenan] Eze 4:6; L. Lis 14:34
Zai kasance har sai kafawar Mulkin. Lu 21:24; Da 7:13, 14
27. Kurwa
A. Abinda kurwa take
Mutum kurwa ne. Fa 2:7; 1Ko 15:45; Jos 11:11; Ay Ma 27:37
Ana kiran dabobbi kurwa ma. L. Lis 31:28; R. Yo 16:3; Le 24:18
Kurwa tana da jini, tana ci, takan mutu. Irm 2:34; Le 7:18; Eze 18:4
Mutum, da ke da rai, ana ce wai yana da kurwa. Mk 8:36; Yo 10:15
B. Bambanci tsakanin kurwa da ruhu
Rai kamar mutum ko kuma halitta kurwa ne. Yo 10:15; Le 17:11
Ikon-rai da ke ba da ƙarfi ga kurwa ana kiransa “ruhu.” Za 146:4; 104:29
Yayinda mutum ya mutu, ikon-rai yakan koma wurin Allah. Mai-Wa 12:7
Allah ne kaɗai zai iya sa ikon-rai ya soma aiki. Eze 37:12-14
28. Kwanaki na Ƙarshe
A. Abinda ake nufi da ‘ƙarshen duniya’
Kawo ƙarshen tsarin abubuwa. Mt 24:3; 2Bi 3:5-7; Mk 13:4
Ba ƙarshen ƙasa ba, amma na mugunyar tsarin abubuwa. 1Yo 2:17
Hallaka zai zo bayan lokaci na ƙarshe. Mt 24:14
Tsira ga masu-adilci; sabuwar duniya zai biyo. 2Bi 2:9; R. Yo 7:14-17
B. Bukatar kasance a falke game da alamun kwanaki na ƙarshe
Allah ya tanadar da alamu don ja-gorance mu. 2Ti 3:1-5; 1Ta 5:1-4
Duniya ta kasa gane muhimmancin haka. 2Bi 3:3, 4, 7; Mt 24:39
Ba jinkiri Allah yake yi ba, amma yana faɗakadwa ne. 2Bi 3:9
Lada na kasancewa a falke, mu kula da shi. Lu 21:34-36
29. Lahira (Hades, Sheol)
A. Ba wani wurin azaban wuta na zahiri ba ne
Ayuba mai-shan wahala ya yi addu’a ya je wurin. Ayu 14:13
Wuri ne da ba a aiki. Za 6:5; Mai-Wa 9:10; Ish 38:18, 19
An tashe Yesu daga kabari, lahira. Ay Ma 2:27, 31, 32; Za 16:10
Lahira za ta fid da matattu da ke cikinta, za a hallakas da ita. R. Yo 20:13, 14
B. Wuta alamar hallaka ce
An alamta datsewa zuwa mutuwa ta wurin wuta. Mt 25:41, 46; 13:30
Miyagu da ba su tuba ba za a hallaka su har abada kamar da wuta. Ibr 10:26, 27
“Shan azabar” wuta na Shaitan shine mutuwa na har abada. R. Yo 20:10, 14, 15
C. Labarin mawadaci da Li’azaru ba tabbacin shan madawwamin azaba ba ne
Ba wuta na zahiri ba ne a ƙirjin Ibrahim. Lu 16:22-24
An kuma saɓa amincewar Ibrahim da duhu. Mt 8:11, 12
An kira hallakaswan Babila azaban wuta. R. Yo 18:8-10, 21
30. Littafi Mai-Tsarki
A. Kalmar Allah hurariya ce
Ruhun Allah ne ya motsa mutane su rubuta shi. 2Bi 1:20, 21
Yana ɗauke da annabci: Da 8:5, 6, 20-22; Lu 21:5, 6, 20-22; Ish 45:1-4
Littafi Mai-Tsarki sukutum hurare ne kuma yana da amfani. 2Ti 3:16, 17; Ro 15:4
B. Kariya ce mai-amfani ga kwananmu
Yin banza da ƙa’idodin Littafi Mai-Tsarki kasada ce. Ro 1:28-32
Hikimar mutane bata sauya ta. 1Ko 1:21, 25; 1Ti 6:20
Kariya ce daga magabci mafi-ƙarfi. Afi 6:11, 12, 17
Yana bishe mutum akan hanya da ke daidai. Za 119:105; 2Bi 1:19; Mis 3:5, 6
C. An rubuta shi don mutane na dukan al’ummai da kuma kabilai
A Gabas ne aka soma rubutun Littafi Mai-Tsarki. Fit 17:14; 24:12, 16; 34:27
Tanadin Allah ne ba ga Turawa kaɗai ba. Ro 10:11-13; Ga 3:28
Allah yana amince da kowane irin mutane. Ay Ma 10:34, 35; Ro 5:18; R. Yo 7:9, 10
31. Minista
A. Tilas ne dukan Kiristoci su zama ministoci
Yesu minista na Allah ne. Ro 15:8, 9; Mt 20:28
Kiristoci suna bin misalinsa. 1Bi 2:21; 1Ko 11:1
Tilas ne su yi wa’azi don cim ma hidimar. 2Ti 4:2, 5; 1Ko 9:16
B. Ingantawa don hidimar
Ruhun Allah da kuma sanin Kalmarsa. 2Ti 2:15; Ish 61:1-3
Bi tafarkin Kristi cikin yin wa’azi. 1Bi 2:21; 2Ti 4:2, 5
Allah yana koyaswa ta wurin ruhu, ƙungiya. Yo 14:26; 2Ko 3:1-3
32. Mugunta, Wahalar Duniya
A. Wanda ke da alhakin wahalar duniya
Mugun mulki ne dalilin lokutta masu-wuya a yau. Mis 29:2; 28:28
Masaraucin duniya magabcin Allah ne. 2Ko 4:4; 1Yo 5:19; Yo 12:31
Iblis ne yake jawo bala’i, lokacinsa kaɗan ne. R. Yo 12:9, 12
Za a ɗaure Iblis, salama mai-girma za ta biyo. R. Yo 20:1-3; 21:3, 4
B. Abinda ya sa aka kyale mugunta
Iblis ya zarge amincin halittu ga Allah. Ayu 1:11, 12
An ba masu aminci zarafin tabbatar da amincinsu. Ro 9:17; Mis 27:11
An tabbatas da Iblis maƙaryaci, za a warware muhawwaran. Yo 12:31
Za a albarkaci masu-aminci da rai na har abada. Ro 2:6, 7; R. Yo 21:3-5
C. Daɗewar lokaci na ƙarshe tanadin rahama na Allah ne
Kamar yadda yake cikin kwanakin Nuhu, yana ɗaukan lokaci kafin ya bada gargaɗi. Mt 24:14, 37-39
Allah ba ya jinkiri, amma yana nuna rahama ne. 2Bi 3:9; Ish 30:18
Littafi Mai-Tsarki ya taimake mu mu guje don kada a kama mu farat ɗaya. Lu 21:36; 1Ta 5:4
Biɗi tanadin Allah yanzu don kariya. Ish 2:2-4; Zep 2:3
D. Maganin wahalar duniya ba daga mutane ba ne
Mutane suna tsoro, sun rikice. Lu 21:10, 11; 2Ti 3:1-5
Mulkin Allah, zai yi nasara, ba mutane ba. Da 2:44; Mt 6:10
Don ka rayu, nemi salama da Sarkin yanzu. Za 2:9, 11, 12
33. Mulki
A. Abinda Mulkin Allah zai yi ma mutane
Zai cika nufin Allah. Mt 6:9, 10; Za 45:6; R. Yo 4:11
Gwamnati da ke da sarki da kuma dokoki. Ish 9:6, 7; 2:3; Za 72:1, 8
Kawas da mugunta, yi sarautan dukan duniya. Da 2:44; Za 72:8
Sarauta na shekaru 1,000 zai maido da mutane, Aljanna. R. Yo 21:2-4; 20:6
B. Sarautar zai soma yayinda magabtan Kristi suna kan mulki
Bayan an tashe Kristi ya jira da daɗewa. Za 110:1; Ibr 10:12, 13
Kwace iko, yaƙe Shaitan. Za 110:2; R. Yo 12:7-9; Lu 10:18
Ya kafa Mulkin a lokacin, yaƙoƙi na duniya sun biyo. R. Yo 12:10, 12
Wahala na yanzu yana nufin lokaci ya yi don goyi bayan Mulkin. R. Yo 11:15-18
C. Ba ‘cikin zukata,’ ba ta wurin ƙoƙarin mutane aka samo shi ba
Mulkin a cikin sama yake, ba a duniya ba. 2Ti 4:18; 1Ko 15:50; Za 11:4
Ba a ‘cikin zukata’ ba; cikin zancen Yesu da Farisawa. Lu 17:20, 21
Ba na wannan duniya ba. Yo 18:36; Lu 4:5-8; Da 2:44
Za a sake gwamnatoci, mizanan duniya. Da 2:44
34. Mutuwa
A. Dalilin mutuwa
Mutum yana da kamiltaccen masomi, da begen rayuwa mara-iyaka. Fa 1:28, 31
Rashin biyayya ya jawo hukuncin mutuwa. Fa 2:16, 17; 3:17, 19
Zunubi da mutuwa ya bi kan dukan ’ya’yan Adamu. Ro 5:12
B. Yanayin matattu
An yi Adamu ya zama kurwa ne, ba wai an ba shi kurwa ba. Fa 2:7; 1Ko 15:45
Mutum ne, watau kurwa, ne ke mutuwa. Eze 18:4; Ish 53:12; Ayu 11:20
Matattu ba su da rai, ba su san komi ba. Mai-Wa 9:5, 10; Za 146:3, 4
Matattu suna cikin barci suna jiran tashin matattu. Yo 11:11-14, 23-26; Ay Ma 7:60
C. Ba ya yiwuwa a yi magana da matattu
Matattu ba su rayuwa tare da Allah kamar ruhohi. Za 115:17; Ish 38:18
An faɗakad game da ƙoƙarin yin magana da matattu. Ish 8:19; Le 19:31
An hukunta, masu-duba, masu-faɗin gaba. K. Sha 18:10-12; Ga 5:19-21
35. Rai
A. An tabbatar da rai na har abada ga mutane masu-biyayya
Allah, wanda ba ya ƙarya, ya yi alkawarin rai. Tit 1:2; Yo 10:27, 28
An tabbatar da rai na har abada ma waɗanda suke bada gaskiya. Yo 11:25, 26
Za a hallakas da mutuwa. 1Ko 15:26; R. Yo 21:4; 20:14; Ish 25:8
B. Rai na samaniya ga waɗanda suke cikin jikin Kristi ne kaɗai
Allah ya zaɓi mambobi kamar yadda yake so. Mt 20:23; 1Ko 12:18
144,000 ne kaɗai aka kwasa daga duniya. R. Yo 14:1, 4; 7:2-4; 5:9, 10
Ko Yohanna Mai-yin Baftisma ma ba shi cikin Mulki na samaniya. Mt 11:11
C. An yi alkawarin rai a duniya ga adadi mara iyaka, “waɗansu tumaki”
Adadi mai-iyaka tare da Yesu cikin sammai. R. Yo 14:1, 4; 7:2-4
“Waɗansu tumaki” ba yan’uwan Kristi ba ne. Yo 10:16; Mt 25:32, 40
Ana tattara mutane da yawa yanzu don tsira zuwa duniya. R. Yo 7:9, 15-17
Za a tashe wasu zuwa rai bisa duniya. R. Yo 20:12; 21:4
36. Ranakun Hutu, Ranakun Haihuwa
A. Kiristoci na farko ba su kiyaye ranakun hutu, Kirsimati ba
Waɗanda ba masu-sujada na gaskiya ba ne ke kiyaye shi. Fa 40:20; Mt 14:6
Bikin tuna da mutuwar Yesu ne za a yi. Lu 22:19, 20; 1Ko 11:25, 26
Yin maye cikin bikin ba daidai ba ne. Ro 13:13; Ga 5:21; 1Bi 4:3
37. Ruhu, Sihiri
A. Abinda ruhu mai-tsarki yake
Ikon aiki na Allah ne, ba mutum ba ne. Ay Ma 2:2, 3, 33; Yo 14:17
An yi amfani da shi a halitta, hure Littafi Mai-Tsarki, da kuma sauransu. Fa 1:2; Eze 11:5
Yana haifa, shafe, mambobin jikin Kristi. Yo 3:5-8; 2Ko 1:21, 22
Yana bada ƙarfi, yana bishe mutanen Allah a yau. Ga 5:16, 18
B. Ana kiran ikon-rai ruhu
Yanayin rai, numfashi ne ke riƙe shi. Yaƙ 2:26; Ayu 27:3
Allah ne yake da ƙarfin ikon-rai. Zec 12:1; Mai-Wa 8:8
Ikon aiki na mutane, dabobbi, daga wurin Allah ne. Mai-Wa 3:19-21
Ruhun da ake bari ga Allah da begen tashin matattu ne. Lu 23:46
C. Tilas ne a ƙi da sihiri kamar aikin aljanu
Kalmar Allah ya haramta shi. Ish 8:19, 20; Le 19:31; 20:6, 27
Faɗin gaba aikin aljan ne; an haramta shi. Ay Ma 16:16-18
Yana kai ga hallaka. Ga 5:19-21; R. Yo 21:8; 22:15
An haramta irin duban masanan taurari. K. Sha 18:10-12; Irm 10:2
38. Sama
A. 144,000 ne kaɗai za su je sama
Kalilan adadi; za su zama sarakuna tare da Kristi. R. Yo 5:9, 10; 20:4
Yesu mai-jagora ne; an zaɓi wasu tun tuni. Kol 1:18; 1Bi 2:21
Wasu da yawa za su zauna a duniya. Za 72:8; R. Yo 21:3, 4
144,000 suna cikin matsayi na musamman da wasu ba su da shi. R. Yo 14:1, 3; 7:4, 9
39. Shaidun Jehovah
A. Tushen Shaidun Jehovah
Jehovah ya sakankance nasa shaidun. Ish 43:10-12; Irm 15:16
Jerin shaidu masu-aminci ya soma da Habila. Ibr 11:4, 39; 12:1
Yesu mashaidi ne mai-aminci mai-gaskiya. Yo 18:37; R. Yo 1:5; 3:14
40. Sifoffi
A. Yin amfani da sifoffi, gumakai, cikin sujada yana rena Allah
Ba shi yiwuwa a yi sifar Allah. 1Yo 4:12; Ish 40:18; 46:5; Ay Ma 17:29
An gargaɗe Kiristoci game da sifoffi. 1Ko 10:14; 1Yo 5:21
Tilas ne a bauta ma Allah da ruhu, da gaskiya. Yo 4:24
B. Bautar sifa ya jawo bala’i ga al’ummar Israila
An haramta Yahudawa su yi sujada ga sifoffi. Fit 20:4, 5
Ba su ji, yin magana; masu-ƙera su kamar su suke. Za 115:4-8
Ya zama tarko, na hallaka. Za 106:36, 40-42; Irm 22:8, 9
C. Ba a yarda da yin sujada ko “na ɗan kaɗan” ba
Allah ya ƙi yarda da yin sujada “na ɗan kaɗan” gareshi. Ish 42:8
Allah ne kaɗai “mai-jin addu’a.” Za 65:1, 2
41. Tashin Matattu
A. Bege ga matattu
Za a tashe dukan waɗanda suke cikin kabarbaru. Yo 5:28, 29
Tashin Yesu daga matattu tabbacin haka ne. 1Ko 15:20-22; Ay Ma 17:31
Ba za a tashe masu-zunubi ga ruhu ba. Mt 12:31, 32
Waɗanda suke nuna bangaskiya suna da tabbacin haka. Yo 11:25
B. Tashin matattu zuwa rai cikin sama ko kuwa a duniya
Duka suna mutuwa cikin Adamu; suna samun rai cikin Yesu. 1Ko 15:20-22; Ro 5:19
Akwai bambanci cikin halin waɗanda za a tasad. 1Ko 15:40, 42, 44
Waɗanda suke tare da Yesu za su zama kamar shi. 1Ko 15:49; Fib 3:20, 21
Waɗanda ba za su yi sarauta ba za su zauna a duniya. R. Yo 20:4b, 5, 13; 21:3, 4
42. Warkaswa, Harsuna
A. Warkaswa na ruhaniya yana da amfani na har abada
Ciwo na ruhaniya yana hallakaswa. Ish 1:4-6; 6:10; Ho 4:6
Warkaswa na ruhaniya shine muhimmin aiki. Yo 6:63; Lu 4:18
Yana kawas da zunubai; yana bada farinciki, rai. Yaƙ 5:19, 20; R. Yo 7:14-17
B. Mulkin Allah zai kawo warkaswan jiki na har abada
Yesu ya warkas da cututtuka, yi wa’azin albarkatai na Mulki. Mt 4:23
An yi alkawarin Mulki kamar warkaswa na har abada. Mt 6:10; Ish 9:7
Za a kawas da mutuwa ma. 1Ko 15:25, 26; R. Yo 21:4; 20:14
C. Warkaswan bangaskiya na zamani ba shi da tabbacin amincewar Allah
Almajiran ba su warkas da kansu ta wurin mu’ujiza ba. 2Ko 12:7-9; 1Ti 5:23
Kyautai na mu’ujiza sun ƙare a kwanan manzanni. 1Ko 13:8-11
Warkaswa ba tabbacin amincewar Allah ba ne. Mt 7:22, 23; 2Ta 2:9-11
D. Yin magana cikin harsuna dabam dabam tanadi ne na ɗan lokaci kawai
Alama ce; za a biɗi kyautai masu-girma. 1Ko 14:22; 12:30, 31
An annabta cewa kyautai na mu’ujiza na ruhu za su shuɗe. 1Ko 13:8-10
Ayuka na ban mamaki ba tabbacin amincewar Allah ba ne. Mt 7:22, 23; 24:24
43. Yesu
A. Yesu Ɗan Allah ne kuma Sarki wanda aka naɗa
Ɗan farin Allah, ya halicce dukan abubuwa. R. Yo 3:14; Kol 1:15-17
Ya zama mutum da mace ta haife shi, kasa da mala’iku. Ga 4:4; Ibr 2:9
Haifaffe daga ruhun Allah, da begen zama cikin sama. Mt 3:16, 17
An ɗaukaka shi da girma fiye da yadda yake dā a mutum. Fib 2:9, 10
B. Imani cikin Yesu Kristi yana da muhimmanci don ceto
Kristi Zuriyar alkawari ne na Ibrahim. Fa 22:18; Ga 3:16
Yesu shine kaɗai Babban Firist, fansa. 1Yo 2:1, 2; Ibr 7:25, 26; Mt 20:28
Rayuwa ta wurin sanin Allah da Kristi, biyayya. Yo 17:3; Ay Ma 4:12
C. Ana bukatar fiye da imani cikin Yesu
Tilas ne ayuka ta biyo bayan imani. Yaƙ 2:17-26; 1:22-25
Tilas ne mu yi biyayya ga umurnai, yi aikin da ya yi. Yo 14:12, 15; 1Yo 2:3
Ba dukan waɗanda ke yin amfani da sunan Ubangiji ne za su shiga Mulkin ba. Mt 7:21-23
44. Zunubi
A. Abinda zunubi yake
Karya dokar Allah, kamiltaccen mizanansa. 1Yo 3:4; 5:17
Mutum kamar halittan Allah, yana da bada lissafi gareshi. Ro 14:12; 2:12-15
Doka ta bada ma’anar zunubi, ta sa mutane su gane ta. Ga 3:19; Ro 3:20
Duka suna cikin zunubi, sun kasa ga kamiltaccen mizanan Allah. Ro 3:23; Za 51:5
B. Abinda ya sa duka suna shan wahalar zunubin Adamu
Adamu ya hayar da ajizanci, mutuwa ga duka. Ro 5:12, 18
Allah ya nuna rahama ta wurin yin haƙuri da mutane. Za 103:8, 10, 14, 17
Hadayar Yesu ya rufa zunubai. 1Yo 2:2
Za a kawas da zunubi da dukan wasu ayuka na Iblis. 1Yo 3:8
C. ’Ya’yan itace da aka haramta rashin biyayya ne, ba wani aika jima’i ba ne
An haramta itacen kafin a halicci Hawa’u. Fa 2:17, 18
An gaya ma Adamu da Hawa’u su haifi ’ya’ya. Fa 1:28
Yara ba sakamakon zunubi ba ne, amma albarkar Allah ne. Za 127:3-5
Hawa’u ta yi zunubi yayinda mijin ba shi nan; ta yi hanzari. Fa 3:6; 1Ti 2:11-14
Adamu, kamar kan, ya yi tawaye da dokar Allah. Ro 5:12, 19
D. Abinda zunubi ga ruhu mai-tsarki yake (Mt 12:32; Mk 3:28, 29)
Zunubin da aka gāda ba irin wannan ba ne. Ro 5:8 12, 18; 1Yo 5:17
Mutum zai iya baƙanta ma ruhu, amma kuma tuba. Afi 4:30; Yaƙ 5:19, 20
Aika zunubi na ganganci yana bishe zuwa mutuwa. 1Yo 3:6-9
Allah yana shar’anta irin waɗannan, fitar da ruhunsa. Ibr 6:4-8
Bai kamata mu yi addu’a ga irin waɗannan marasa tuba ba. 1Yo 5:16, 17