Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/13 p. 3
  • Ku Yi Amfani da Bidiyo Wajen Koyarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Amfani da Bidiyo Wajen Koyarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Karin Bayanai
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Nuna Yadda Ake Nazari da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 5/13 p. 3

Ku Yi Amfani da Bidiyo Wajen Koyarwa

Sa’ad da Jehobah yake bayyana wa Ibrahim da Irmiya wasu abubuwa masu muhimmanci, bai faɗa musu da baki kawai ba, amma ya yi amfani da abubuwan da mutane za su iya gani wajen yi musu koyarwa don su fahimci abin da yake faɗi cikin sauƙi. (Far. 15:5; Irm. 18:1-6) Za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su fahimci kuma su amfana daga koyarwar Littafi Mai Tsarki ta wajen yin amfani da abin da za su iya gani, kamar su bidiyon da muke da su. Shawarwarin da ke gaba za su iya taimaka mana mu san lokacin da ya kamata mu nuna wa ɗalibanmu wasu bidiyonmu. Amma ku tuna cewa ba dole ba ne sai an yi amfani da waɗannan shawarwari, domin kowane ɗalibi yana da nasa bukata.

Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

◻ Babi na 1: Bayan kun yi nazarin sakin layi na 17, ku kalli bidiyon The Wonders of Creation Reveal God’s Glory a Turanci.

◻ Babi na 2: Bayan kun gama nazarin babin, ku kalli bidiyon Mankind’s Oldest Modern Book a Turanci.

◻ Babi na 9: Bayan kun yi nazarin sakin layi na 14, ku kalli bidiyon Jehovah’s Witnesses—Organized to Share the Good News a Turanci.

◻ Babi na 14: Bayan kun gama nazarin babin, ku kalli bidiyon The Bible—Its Power in Your Life a Turanci.

◻ Babi na 15: Bayan kun yi nazarin sakin layi na 10, ku kalli bidiyon Our Whole Association of Brothers a Turanci.

Littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”

◻ Babi na 3: Bayan kun yi nazarin sakin layi na 15, ku kalli bidiyon Young People Ask—How Can I Make Real Friends? a Turanci.

◻ Babi na 4: Bayan kun gama nazarin babin, ku kalli bidiyon Respect Jehovah’s Authority a Turanci.

◻ Babi na 7: Bayan kun yi nazarin sakin layi na 12, ku kalli bidiyon No Blood—Medicine Meets the Challenge a Turanci.

◻ Babi na 9: Bayan kun gama nazarin sakin layi na 6, ku kalli bidiyon Warning Examples for Our Day a Turanci.

◻ Babi na 17: Bayan kun gama nazarin babin, ku kalli bidiyon ‘Walk by Faith, Not by Sight’ a Turanci.

Shin akwai wasu bidiyo dabam da ɗalibanku za su amfana daga kallon su? Alal misali, ɗalibanku da ake tsananta musu za su iya samun ƙarfafa daga kallon bidiyon Faithful Under Trials—Jehovah’s Witnesses in the Soviet Union ko kuma Jehovah’s Witnesses Stand Firm Against Nazi Assault duka a Turanci. Matasa za su iya amfana daga kallon bidiyon Pursue Goals That Honor God da kuma Young People Ask—What Will I Do With My Life? duka a Turanci. Ku saka maki a jikin sakin layi ko babin waɗannan littattafan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kuma Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah a inda ya dace, don ku tuna lokacin da ya kamata ku kalli bidiyon tare da ɗalibanku ko kuma ku yi musu aron bidiyon don su kalla da kansu. Yayin da ake fitar da sababbin bidiyo, ku shirya yadda za ku yi amfani da su wajen taimaka wa ɗalibanku su kyautata dangantakarsu da Jehobah.—Luk 24:32.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba