Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Mene Ne Za Ka Gano a Taronmu na Kirista?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
    • DARASI NA 5

      Mene Ne Za Ka Gano a Taronmu na Kirista?

      Shaidun Jehobah a Majami’ar Mulkin da ke ƙasar Ajantina

      Ajantina

      Taron Shaidun Jehobah a ƙasar Saliyo

      Saliyo

      Taron Shaidun Jehobah Belgium

      Belgium

      Taron Shaidun Jehobah a ƙasar Malesiya

      Malesiya

      Mutane da yawa sun daina zuwa wuraren bauta domin sun kasa samun amsoshin tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa. Amma, me ya sa ya kamata ka halarci taron Kirista da Shaidun Jehobah suka tsara? Mene ne za ka shaida a wurin?

      Za ka yi farin ciki domin kana tsakanin mutanen da suke ƙaunar juna kuma suna kula da juna. A ƙarni na farko, an rarraba Kiristoci zuwa ikilisiyoyi dabam-dabam, kuma suna taro don su bauta wa Allah, su yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma su ƙarfafa juna. (Ibraniyawa 10:24, 25) Saboda ƙaunar da suke nuna wa juna, sun ji kamar suna tsakanin abokansu na gaskiya, wato, ’yan’uwansu Kiristoci maza da mata. (2 Tasalonikawa 1:3; 3 Yohanna 14) Irin misalin da muke bi ke nan a yau, kuma muna farin ciki kamar Kiristoci na ƙarni na farko.

      Za ka koyi yadda za ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Kamar yadda aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki, maza da mata da kuma yara suna haɗuwa a wuri guda. Ƙwararrun malamai suna amfani da Littafi Mai Tsarki don su taimaka mana mu san yadda za mu bi ƙa’idodinsa a rayuwarmu ta yau da kullum. (Kubawar Shari’a 31:12; Nehemiya 8:8) Dukan waɗanda suka halarci wannan taron za su iya yin waƙa da furuci sa’ad da aka gayyaci masu sauraro su yi hakan, kuma wannan yana ba mu damar furta begenmu na Kirista.—Ibraniyawa 10:23.

      Bangaskiyarka ga Allah za ta ƙara ƙarfi. Manzo Bulus ya gaya wa wata ikilisiya a zamaninsa cewa: “Ina marmarin ganinku, . . . mu sami ƙarfafawa a wurinku, kowannenmu ta wurin bangaskiyar junanmu, taku da tawa kuma.” (Romawa 1:11, 12) Kasancewa tare da ’yan’uwa Kiristoci a wajen taronmu a kai a kai yana ƙarfafa bangaskiyarmu da ƙudurinmu na ci gaba da bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

      Me zai hana ka karɓi wannan gayyatar na halartar taronmu na gaba don ka ga waɗannan abubuwan da kanka? Za a marabce ka da hannu bibiyu. Ba a karɓan ko sisi a wajen taronmu.

      • Bisa wane gurbi ne aka tsara taronmu?

      • Ta yaya za mu amfana idan muka halarci taron Kirista?

      KA ƘARA BINCIKE

      Idan kana so ka ga yadda cikin Majami’ar Mulki take kafin ka halarci taronmu, ka gaya wa wani Mashaidin Jehobah ya kai ka don ya nuna maka yadda wurin yake.

  • Yaya Yin Tarayya da ’Yan’uwanmu Kiristoci Zai Amfane Mu?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
    • DARASI NA 6

      Yaya Yin Tarayya da ’Yan’uwanmu Kiristoci Zai Amfane Mu?

      Shaidun Jehobah suna tarayya

      Madagaska

      Wani Mashaidi yana taimakawa wani ɗan’uwa

      Norway

      Dattawa sun ziyarci ’yan’uwa

      Labanan

      Shaidun Jehobah suna tarayya

      Italiya

      Muna halartan taron Kirista babu fashi, ko da za mu bi kurmi ne don mu isa wurin, ko ana ruwa ko ana rana. Amma, me ya sa Shaidun Jehobah suke ƙoƙartawa sosai su kasance tare da ’yan’uwansu masu bi a taro, duk da matsaloli na rayuwa da kuma gajiyar aiki?

      Yana taimaka mana mu jimre da matsaloli. Sa’ad da Bulus yake magana game da waɗanda muke cuɗanya da su a cikin ikilisiya, ya ce “mu lura da juna.” (Ibraniyawa 10:24) Abin da wannan furucin yake nufi shi ne, muna bukatar mu san juna sosai. Saboda haka, kalmomin manzon nan suna ƙarfafa mu ne mu riƙa kula da ’yan’uwanmu masu bi. Idan muka ƙoƙarta muka san sauran ’yan’uwanmu Kiristoci da ke cikin ikilisiya, hakan zai sa mu ga cewa wasu daga cikinsu sun taɓa fama da irin matsalar da muke fuskanta, kuma za su iya taimaka mana mu warware namu matsalolin.

      Yana ƙarfafa abotar da ke tsakaninmu. Waɗanda muke cuɗanya da su a wajen taronmu, ba waɗanda muka yi wa sanin shanu ba ne, amma abokanmu ne na kud da kud. A wasu lokatai, muna yin nishaɗi mai kyau tare. Wane amfani ne muke samu daga irin wannan cuɗanyar? Tana sa mu ƙara riƙe juna hannu bibiyu, kuma hakan yana ƙarfafa ƙaunar da ke tsakaninmu. Sa’ad da ’yan’uwanmu maza da mata suke fuskantar matsaloli, muna taimaka musu nan da nan saboda abota mai kyau da ke tsakaninmu. (Misalai 17:17) Domin muna tarayya da dukan waɗanda suke cikin ikilisiyarmu, mu nuna cewa muna yi “wa juna tattali ɗaya.”—1 Korintiyawa 12:25, 26.

      Muna ƙarfafa ka ka ƙulla abota da waɗanda suke yin nufin Allah. Za ka samu irin waɗannan abokan a tsakanin Shaidun Jehobah. Don Allah kada ka bari wani abu ya hana ka yin tarayya da mu.

      • Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci taro tare da ’yan’uwanmu?

      • A yaushe ne za ka so ka halarci taro don ka san Shaidun da ke cikin ikilisiyarmu sosai?

  • Yaya Ake Gudanar da Taronmu?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
    • DARASI NA 7

      Yaya Ake Gudanar da Taronmu?

      Taron Shaidun Jehobah a ƙasar New Zealand

      New Zealand

      Taron Shaidun Jehobah a ƙasar Jafan

      Jafan

      Wani Mashaidi matashi yana karanta Littafi Mai Tsarki a Yuganda

      Yuganda

      Wasu Shaidu biyu suna gwaji na tattauna Littafi Mai Tsarki a Lithuania

      Lithuania

      A dukan taron da Kiristoci na farko suka yi, sun yi waƙoƙi da addu’o’i, sun karanta Nassi kuma sun tattauna shi. (1 Korintiyawa 14:26) Irin abin da muke yi a wajen taronmu a yau ke nan.

      An ɗauko abin da ake koyarwa a taron ne daga Littafi Mai Tsarki kuma hakan yana da amfani. A ƙarshen mako, ’yan’uwanmu a kowace ikilisiya suna yin taro don su saurari jawabin da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki na minti 30, a kan yadda Nassi ya shafi rayuwarmu da kuma zamanin da muke ciki a yau. Ana ƙarfafa dukanmu mu buɗe namu Littafi Mai Tsarki sa’ad da ake karantawa. Bayan an kammala jawabin, ana yin Nazarin “Hasumiyar Tsaro” na tsawon awa guda, kuma ana ba masu sauraro damar yin furuci sa’ad da ake tattauna talifin da aka ɗauko daga Hasumiyar Tsaro. Wannan tattaunawar tana taimaka mana mu yi amfani da shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu. Ana nazarin talifi iri ɗaya a ikilisiyoyi sama da 110,000 a faɗin duniya.

      Ana taimaka mana mu kyautata yadda muke koyarwa. Muna kuma gudanar da taro mai sassa uku da yamma a tsakiyar mako mai jigo Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu da ke Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Sashe na farko, wato Darussa Daga Kalmar Allah yana taimaka mana mu tattauna wasu surorin Littafi Mai Tsarki waɗanda ’yan’uwa sun riga sun karanta kafin su zo taron. Sashe na biyu kuma shi ne, Ka Yi Wa’azi da Ƙwazo, kuma a wannan sashen za a yi gwaji da suke taimaka mana mu kyautata yadda muke wa mutane wa’azi. Akwai mashawarci da zai ba mu shawara da za ta taimaka mana mu kyautata yadda muke karatu da kuma ba da jawabi. (1 Timotawus 4:13) Sashe na ƙarshe shi ne Rayuwar Kirista, wannan sashen na taimaka mana mu san yadda za mu yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu na yau da kullum. Kuma ana tattauna wasu tambayoyi da amsoshi da suke taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki sosai.

      Babu shakka, idan ka halarci taronmu, za ka ji daɗin koyarwa mai kyau da muke yi daga Littafi Mai Tsarki.—Ishaya 54:13.

      • Mene ne za ji sa’ad da ka halarci taron Shaidun Jehobah?

      • Wanne cikin taronmu na mako-mako za ka so ka halarta a nan gaba?

      KA ƘARA BINCIKE

      Ka bincika wasu abubuwan da za a tattauna a nan gaba a taronmu. Ka rubuta abin da za ka so ka koya daga Littafi Mai Tsarki wanda zai amfane ka a rayuwarka ta yau da kullum.

Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba