Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
18-14 GA DISAMBA
Neman Abubuwa Masu Tamani
br1 24 sakin layi na 9-10
Babu Alatun da Aka Halitta Domin Ku da Zai Yi Nasara
9 Annabcin Zechariah ya ba da haske game da dalilin da ya sa al’ummai suke gāba da Kiristoci na gaskiya. Ka lura da abin da Zechariah 12:3 ta ce: “Za ya zama kuwa cikin ranan nan, zan maida Urushalima dutse mai-wuyan ɗauka ga dukan al’ummai.” Ga wane Urushalima wannan yake magana a kai? Annabcin Zechariah game da Urushalima yana magana ne game da “Urushalima ta sama,” Mulkin sama da aka kira Kiristoci shafaffu. (Ibraniyawa 12:22) Kaɗan daga cikin waɗannan masu sarauta a Mulkin Almasihu har yanzu suna duniya. Su da abokansu “waɗansu tumaki,” suna ariritar mutane su koma ga Mulkin Allah tun da sauran lokaci. (Yohanna 10:16; Ru’ya ta Yohanna 11:15) Yaya al’ummai suka karɓi wannan gayyatar? Ta yaya wannan shelar take shafan taimako da Jehobah yake bai wa masu bauta ta gaskiya a yau? Bari mu gani sa’ad da muka bincika ma’anar tabbacin Zechariah sura 12. Ta yin haka, za mu sami tabbacin cewa ‘babu makamin’ da zai yi nasara bisa shafaffu na Allah da kuma abokansu da suka keɓe kansu.
10 Zechariah 12:3 ta nuna cewa al’ummai sun sha “rauni mai zafi.” Ta yaya hakan ya faru? Allah ya umurta cewa bisharar Mulki dole ne a yi wa’azinta. Shaidun Jehobah sun ɗauki wannan hakki da muhimmanci. Amma, shelar cewa Mulkin ne kawai bege ga mutane ya zama “dutse mai-wuyan ɗauka” ga al’ummai. Suna so su ɗauke shi ta wajen ƙoƙarin hana wa’azin Mulki. Ta wajen yin haka, waɗannan al’umman sun “sha rauni mai-zafi.” Suka ɓata sunansu domin rashin nasara da suka yi. Ba za su iya rufe baƙin masu bauta ta gaskiya a, waɗanda suke son gatarsu ta shelar “bishara ta har abada” ta Mulkin Almasihu kafin ƙarshen wannan zamanin. (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Sa’ad da ya ga irin azaba da aka gana wa bayin Jehobah, wani mai gadi a wata ƙasa a Afrika ya ce: ‘Kuna ɓata lokacinku ne wajen tsanata wa waɗannan mutane. Ba za su taɓa yin ridda ba. Sai ƙaruwa za su riƙa yi.’
br1 27 sakin layi na 13
Babu Alatun da Aka Halitta Domin Ku da Zai Yi Nasara
13 Don Allah ka karanta Zechariah 12:7, 8. A Isra’ila ta dā, tanti abu ne na musamman a ƙasar Isra’ila da makiyaya da kuma manoma suke amfani da shi. Irin waɗannan mutanen ne za su bukaci kāriya da farko idan al’ummar abokan gāba ta kai wa Urushalima hari. ‘Furucin nan tanti na Yahuda’ ya nuna cewa raguwar shafaffu a zamaninmu kamar dai a fili suke ba a cikin birane masu kāriya ba. A nan suke kāre al’amuran Mulkin Almasihu babu tsoro. Jehobah mai runduna ‘za ya fara ceton tanti na Yahuda’ domin waɗannan su ne abin fako da farko na Shaiɗan.
25-31 GA DISAMBA
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MALAKAI 1-4
“Aurenku Na Faranta wa Jehobah Rai Kuwa?”
jd-E 125-126 sakin layi na 4-5
Ka Bi da Iyalinka a Yadda Allah Yake So
4 A lokacin da annabi Malakai ya yi rayuwa a ƙarni na biyar kafin haihuwar Yesu, Yahudawa suna yawan kashe aurensu. Shi ya sa Malakai ya ce musu: “Ubangiji ya zama shaida tsakaninka da matarka ta ƙuruciya, wadda ka ci amanarta.” Saboda yadda mazaje suke yawan cin amanar matansu, bagadin Jehobah ya rufu da hawayen matansu “da kuka, da ajiyar zuci” kuma wasu firistoci suna goyon bayan wannan cin amanar!—Malakai 2:13, 14.
5 Yaya Jehobah ya ji game da yadda Yahudawa suke cin amanar matansu a zamanin Malakai? Malakai ya rubuta cewa: “Gama ina jin ƙyamar kisan aure, in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila.” Ya kuma ƙara da cewa Jehobah ‘bai canja ba.’ (Malakai 2:16; 3:6) Shin ka lura cewa tun farko Allah ya tsani kisan aure? (Farawa 2:18, 24) Kamar yadda ya tsani kisan aure a zamanin Malakai, haka ma ya tsane shi a yau. Wasu sukan kashe aurensu kawai don ba sa jin daɗin zama da aboki ko kuma abokiyar aurensu. Suna yin hakan don mugunta da ke zuciyarsu amma Jehobah yana ganin zuciyarsu. (Irmiya 17:9, 10) Ko da mutum ya ɓoye wa wasu ainihin dalilin da ya sa ya kashe aure, ba zai iya ɓoye hakan wa Jehobah ba. Domin “abubuwa duka a tsiraice suke, buɗaɗu kuma gaban idanun wannan wanda muke gare shi.”—Ibraniyawa 4:13.
Neman Abubuwa Masu Tamani
br1 29 sakin layi na 1
Darussa Daga Littafin Malachi
1:10. Jehobah bai yi farin ciki ba da hadayar waɗannan firistoci masu haɗama, wanda za su nemi a biya su dukan wani aiki da suke yi har da rufe ƙofa da kuma hura wutar bagadi. Yana da muhimmanci cewa bautarmu, haɗe da abin da muka yi a hidimar Kirista ya kasance ƙauna ce marar son kai ga Allah da kuma maƙwabta take motsa mu, ba domin kuɗi ba!—Matta 22:37-39; 2 Korintiyawa 11:7.
br1 30 sakin layi na 2
3:10—Shin ba da “dukan zakka” yana nufi ne cewa mun ba wa Jehobah dukan abin da muke da shi? Mutuwar Yesu ta sa aka daina bin Dokar Musa, saboda haka ba da zakkan kuɗi ba farilla ba ce. Duk da haka, ba da zakka tana da ma’ana ta alama. (Afisawa 2:15) Ba ta nufin cewa mun ba da dukan abin da muke da shi. Ko da yake ana kai zakka shekara shekara, muna ba da dukan abin da muke da shi ne sau ɗaya kawai ga Jehobah, sa’ad da muka keɓe masa kanmu kuma muka nuna haka ta wajen yin baftisma cikin ruwa. Daga wannan lokacin zuwa gaba dukan wani abin da muke da shi na Jehobah ne. Duk da haka, ya ƙyale mu mu zaɓi ɓangaren abin da muke da shi, wato zakka ta alama, mu yi amfani da ita a hidimarsa. Dukan abin da yanayinmu ya ƙyale kuma zuciyarmu ta motsa mu mu yi amfani da shi ne. Abubuwa da muke ba wa Jehobah sun haɗa da abubuwa kamar su lokaci, ƙuzari, da kuma dukiya da ake amfani da shi wajen wa’azin Mulkin da kuma aikin almajirantarwa. Har ila sun haɗa da halartar taro, ziyarar majiyyata da tsofaffi ’yan’uwanmu masu bi, da kuma ba da taimakon kuɗi domin bauta ta gaskiya.