Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
1-7 GA JANAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 1-3
“Mulkin Sama Ya Kusa”
(Matta 3:1, 2) A cikin waɗannan kwanaki Yohanna Mai-yin baftisma ya zo, yana wa’azi cikin jeji na Yahudiya, 2 yana cewa, Ku tuba; gama mulkin sama ya kusa.
nwtsty na nazarin Mt 3:1, 2
wa’azi: Kalmar Helenanci da aka fassara wa’azi, ainihi tana nufin “yin shela a matsayin jakada na al’umma.” Ƙari ga haka, tana nuna yadda ake yin shela: musamman ma ga al’umma ko ga kowa ba jawabi ga taron jama’a ba.
Mulki: Kalmar Helenancin nan ba·si·leiʹa, da aka fassara zuwa mulki, da farko an yi amfani da ita wajen nuni ga gwamnati wadda sarki ne yake sarautarta da talakawan gwamnatin da kuma yankin da sarkin yake mulka. Kalmar ta bayyana sau 162 a cikin Nassin Helenanci na Kirista kuma 55 daga ciki da suka bayyana a littafin Matta, suna nufin Mulkin Allah da ke sama. Matta ya yi amfani da kalmar sosai shi ya sa ana iya kiran littafinsa, Bisharar Mulki.
Mulkin Sama: Wannan furucin ya bayyana wajen sau 30 kuma a littafin Matta ne kawai ya bayyana. A littafin Markus da Luka, an yi amfani da furucin nan “Mulkin Allah” kuma sun nuna cewa a sama ne “Mulkin Allah” yake kuma daga wurin yake mulki.—Mt 21:43; Mk 1:15; Lu 4:43; Da 2:44; 2Ti 4:18.
ya yi kusa: Wannan yana nufin cewa Sarkin Mulkin sama ya kusa ya bayyana.
(Matta 3:4) Yohanna fa da kansa tufafinsa na gashin raƙumi ne, da ɗamara ta fata a gindinsa; abincinsa kuwa fara ne da zuma ta jeji.
nwtsty hotuna da bidiyo
Tufafin Yohanna da Kuma Shigarsa
Yohanna yana saka tufafin da aka yi da gashin rakumi kuma yana yin ɗamara da leda da ake amfani da shi wajen ɗaukan abun da ba shi da nauyi. Irin tufafin ne annabi Iliya yake sakawa. (2 Sarakuna 1:8) Talakawa ne suke yawan saka tufafin da aka saƙa da gashin rakumi. Akasin haka, masu kuɗi ne suke saka tufafin da aka yi da auduga. (Mt 11:7-9) Tun da yake Yohanna Ba-nazari ne, zai yiwu ba a taɓa aske sumarsa ba. Shigarsa da kuma tufafinsa sun nuna cewa ya sauƙaƙa rayuwarsa don ya iya yin nufin Allah.
Fari
Kamar yadda aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar ta ƙunshi kowane irin “fari” har da waɗanda suke da guntun ƙaho, musamman ma waɗanda suke yawan tafiya dami-dami. Binciken da aka yi a Urushalima sun nuna cewa farin jeji suna ɗauke da sinadarin furotin da yawansa ya kai kashi 75. A yau kafin mutane su ci fari, suna yawan cire kan da ƙafar da cinyoyin da kuma cikin. Sai su dafa sauran kafin ko kuma su ci ɗanye. An ce fari suna da ɗanɗano kamar ƙaguwa kuma suna da sinadarin furotin sosai.
Zuma
Wannan hoton gidan zuma ne (1) da kuma inda suke saka ruwansu (2). Wataƙila zuman nan da ake kira Apis mellifera syriaca, ne Yohanna yake shan ruwansu, domin irin zuman ne aka fi sani a yankin. Irin wannan zuman da ke yawan harbi sun fi son zama a jejin Yahudiya inda akwai zafi sosai, shi ya sa mutum ba zai iya yin kiwon su ba. Amma, tun a ƙarni na tara kafin haihuwar Yesu ne mutane suke yin kiwon zuma a cikin randa. Masu bincike sun gano gidajen zuma da yawa a birnin dā da ke tuddan Yahudiya (yanzu ana kiran wurin Tel Rehov). Masu binciken sun gano cewa ainihin zuma da suka zuba ruwa da aka gano a garin, an sayo su ne daga ƙasar da yanzu aka fi sani da Turkiya.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 1:3) Yahuda ya haifi Parisa da Zaraha daga wurin Thamara; Parisa ya haifi Hasruna; Hasruna ya haifi Arama;
nwtsty na nazarin Mt 1:3
Tamar: Ita ce mace ta farko da aka fara ambatawa a tarihin Almasihu da Matta ya rubuta. Sauran mata huɗun su ne Rahila da Ruth, kuma su ba Isra’ilawa ba ne (aya 5); da kuma Bath-sheba, “matar Uriya” (aya 6); da Maryamu (aya 16). An ambata waɗannan matan a tarihin Yesu domin dukansu sun yi abubuwa masu muhimmanci da ya sa suka zama kakannin Yesu.
(Matta 3:11) Ni dai ina yi maku baftisma da ruwa zuwa tuba: amma shi wanda ke zuwa bayana ya fi ni iko, ko takalmansa ban isa in ɗauke su ba: shi za ya yi maku baftisma da Ruhu Mai-tsarki da wuta kuma.
nwtsty na nazarin Mt 3:11
maku baftisma: Ko kuma “tsoma.” Kalmar Helenancin nan ba·ptiʹzo tana nufin “nitsarwa.” A wasu Littafi Mai Tsarki, an bayyana cewa baftisma ta ƙunshi nitsar da mutum cikin ruwa gabaki ɗaya. Akwai lokacin da Yohanna yake yi wa mutane baftisma a wani waje kusa da Salima da ke Kwarin Urdun domin akwai “ruwa da yawa” a wurin. (Yoh 3:23) A lokacin da Filibus yake so ya yi wa wani Ba-kushi baftisma, dukansu biyun sun “shiga ruwa.” (A. M. 8:38) A cikin juyin Septuagint, an yi amfani da wannan kalmar Helenancin a littafin 2Sa 5:14 don a nuna cewa Na’aman ya “nutsa so bakwai cikin Urdun.”
8-14 GA JANAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 4-5
“Darussan da Muka Koya Daga Huɗubar Yesu a kan Dutse”
(Matta 5:3) “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah, domin za su gāji mulkin sama.”
nwtsty na nazarin Mt 5:3
Farin ciki: Ba kawai irin farin cikin da mutum yake yi sa’ad da yake jin daɗi ba ne. A maimakon haka, idan aka yi amfani da shi sa’ad da ake magana game da mutane, hakan yana nuna irin farin cikin da mutum yake yi don Allah ya albarkace shi kuma ya nuna masa alheri. Ana amfani da wannan furucin wajen kwatanta yanayin Allah da kuma Yesu a sama.—1Ti 1:11; 6:15.
waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah: Furucin Helenanci da aka fassara zuwa “waɗanda suka san,” a zahiri yana nufin, “talakawa (masu roƙo ko neman taimako),” amma a wannan mahallin, hakan yana nufin waɗanda suke da bukata kuma suka san da hakan. Ƙari ga haka, an yi amfani da wannan furucin a Lu 16:20, 22 sa’ad da ake magana game da wani “maroƙi” mai suna Li’azaru. Furucin Helenancin nan da wasu mafassara suka fassara zuwa “san talaucinsu na ruhu” yana nufin mutanen da suka san cewa suna bukatar Allah don su ƙulla dangantaka da shi.
(Matta 5:7) “Masu-albarka ne masu-jin ƙai: gama su za su sami jin ƙai.”
nwtsty na nazarin Mt 5:7
jin ƙai: Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furucin nan “nuna jin ƙai” da kuma “jin ƙai” ba kawai don ya kwatanta gafarta wa ko kuma nuna tausayi sa’ad da ake shari’a ba ne. A yawancin lokaci, yana nufin tausayi da yake sa mutum ya ɗauki matakin taimaka ma waɗanda suke da bukata.
(Matta 5:9) “Farin ciki ya tabbata ga masu son zaman lafiya, domin za a ce da su ’ya’yan Allah.”
nwtsty na nazarin Mt 5:9
masu son zaman lafiya: Ba kawai waɗanda suke son zaman lafiya ba amma waɗanda suke iya ƙoƙarinsu don su ga cewa sun yi zaman lafiya da kowa har da magabtansu.
Ka Koyar da Yaronka Ya So Zaman Lafiya
Kiristoci suna son koyar da yaransu ‘su nemi salama, su bi ta kuma.’ (1 Bitrus 3:11) Idan muka yi ƙoƙari muka guji yin shakkar mutane da ƙiyayya don mu zauna lafiya da kowa, za mu yi farin cikin sosai.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 4:9) Ya ce masa, Dukan waɗannan ni ba ka, idan ka fāɗi, ka yi mani sujada.
nwtsty na nazarin Mt 4:9
yi mani sujada: Kalmar aikatau na Helenanci da za a iya fassara zuwa “yi sujada” tana nufin abu da yake faruwa. Yadda aka fassara ta zuwa “yi mani sujada” ya nuna cewa Shaiɗan bai bukaci Yesu ya ci gaba da yi masa sujada ba, amma ya so ya yi masa “sujada” sau ɗaya ne kawai.
(Matta 4:23) Yesu kuwa ya yi yawo cikin dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin bishara ta mulkin, yana warkar da kowace irin cuta da kowane irin rashin lafiya a cikin mutane.
nwtsty na nazarin Mt 4:23
koyarwa . . . wa’azi: Koyarwa ba ɗaya yake da yin wa’azi ba domin malamin ba shela kawai yake yi ba amma yana ba su umurni da bayyanai da ba su misalai da kuma tabbatar musu da abin da yake faɗa.
15-21 GA JANAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 6-7
“Ku Saka Mulkin Allah Farko a Rayuwarku”
(Matta 6:10) Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.
(Matta 6:24) “Ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu: gama ko shi ƙi ɗayan, shi ƙaunaci ɗayan: ko kuwa shi lizimci ɗayan, shi rena ɗayan. Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya ba.”
nwtsty na nazarin Mt 6:24
bauta: Kalmar Helenancin nan tana nufin yi wa wani aiki a matsayin bawansa. A ayar nan, Yesu yana faɗan cewa Kirista ba zai iya bauta wa Allah da dukan zuciyarsa da kuma biɗan abubuwan duniya a lokaci ɗaya ba.
(Matta 6:33) “Amma ku fara biɗan mulkinsa, da adalcinsa; waɗannan abubuwa duka fa za a ƙara maku su.”
nwtsty na nazarin Mt 6:33
Ku . . . biɗi: Furucin Helenancin nan yana nuna cewa mutum yana bukatar ya ci gaba da yin wani abu, don haka za a iya fassara shi “Ku ci gaba da biɗan.” Mabiyan Yesu ba sa bukatar su biɗi Mulkin Allah na ƙaramin lokaci, bayan hakan sai su daina ba. Amma suna bukatar su ci gaba da biɗansa farko a rayuwarsu.
Mulkin: A wasu rubuce-rubucen Helenanci na dā, an fassara shi “Mulkin Allah.”
sa: Hakan na nuni ga Allah, “Uba na sama” kamar yadda aka ambata a Mt 6:32.
adalci: Waɗanda suke biɗan adalcin Allah suna son yin nufinsa da bin ƙa’idodinsa game da mugunta da nagarta. Wannan koyarwar ta yi dabam da na Farisawa, waɗanda suke son bin dokokin da suka kafa wa kansu na adalci.—Mt 5:20.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 7:12) “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma: gama Attaurat ke nan da Annabawa.”
(Matta 7:28, 29) Ana nan sa’anda Yesu ya gama waɗannan zantattuka, taron mutane suka yi mamaki da koyarwarsa: 29 gama ya koya masu kamar mai-hukunci, ba kamar marubutansu ba.
nwtsty na nazarin Mt 7:28, 29
suka yi mamaki: Furucin aikatau na Helenancin da aka yi amfani da shi a nan yana nufin “mutum ya sha mamaki sosai har ya manta da kansa.” Furucin aikatau da aka yi amfani da shi ya nuna cewa taron jama’a da suka saurare shi ba za su taɓa manta da abin da ya koyarwarsa ba.
koyarwarsa: Wannan furucin yana nufin yadda Yesu ya koyar da mutane, wato hanyoyin koyarwarsa. Kuma hakan ya ƙunshi abin da ya koya musu, wato duk abubuwan da ya koya musu a Huɗubarsa a Kan Dutse.
ba kamar marubutansu ba: Maimakon Yesu ya yi ƙaulin abin da Farisawa suka ce kamar yadda marubuta suka saɓa yi, Yesu ya yi magana a matsayin wakilin Jehobah, wato, kamar wanda yake da iko sosai. Kuma duk wani abin da ya koyar daga Kalmar Allah ne.—Yoh 7:16.
22-28 GA JANAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 8-9
“Yesu Ya Ƙaunaci Mutane”
(Matta 8:1-3) Sa’ad da ya gangaro daga dutsen, taron jama’a mai-yawa suka bi shi. 2 Sai wani kuturu kuma ya zo wurinsa, ya yi masa sujada, ya ce, Ubangiji, idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni. 3 Ya miƙa hannuwansa, ya taɓa shi, ya ce, Na yarda; ka tsarkaka. Nan da nan fa kuturtarsa ta tsarkaka.
nwtsty na nazarin Mt 8:3
ya taɓa shi: Dokar da aka ba da ta hannun Musa ta umurta cewa a keɓe kutare a wani wuri don kada su ƙazantar da jama’a. (Le 13:45, 46; L. Li 5:1-4) Amma Yahudawa sun ƙara gishiri a kan dokokin. Alal misali, sun ce mutane su nisanci kutare har nisan kafa shida. Kuma idan ana iska, su guje su nisan kafa 150. Waɗannan dokokin sun sa ana ta wulaƙanta kutare. Al’adarsu ta yaba ma wani Ba-farise da yake ɓoye wa kutare da kuma wanda ya jefe su don kada su ƙazantar da shi. Amma Yesu ya ji tausayin kutare sosai shi ya sa ya taɓa ɗayansu. Wasu Yahudawa ba za su taɓa yin hakan ba. Yesu ya yi hakan ko da yake yana da ikon warkar da shi ta magana kawai.—Mt 8:5-12.
Na yarda: Yesu bai amsa roƙon da kuturun ya yi masa kawai ba amma ya nuna cewa yana ƙaunarsa sosai shi ya sa ya warkar da shi.
(Matta 9:9-13) Daga can sa’anda Yesu yana wucewa, ya ga wani mutum, sunansa Matta, yana zaune wurin karɓan haraji, ya ce masa, Ka biyo ni. Sai ya tashi, ya bi shi. 10 Ana nan yana zaune cikin gida, wurin abinci, sai ga masu-karɓan haraji da yawa da masu-zunubi suka zo, suka zauna tare da Yesu da almajiransa. 11 Sa’anda Farisawa suka ga wannan, suka ce wa almajiransa, don me Malaminku yana ci tare da Masu-karɓan haraji da masu-zunubi. 12 Amma sa’anda ya ji, ya ce, Lafiyayyu ba su da bukatar mai-magani, sai masu-ciwo. 13 Amma ku tafi ku koya azancin wannan, Ni, jinƙai ni ke so, ba hadaya ba: gama na zo ba domin in kira masu adalci ba, amma masu-zunubi.
nwtsty na nazarin Mt 9:10
wurin cin abinci: Ko kuma “zama a kan teburi.” Idan ka zauna da wani a kan teburi don ku ci abinci, hakan ya nuna cewa da akwai mutunci a tsakaninku. Amma Yahudawa a zamanin Yesu ba sa yarda su zauna ko su ci abinci tare da waɗanda ba Yahudawa ba.
masu-karɓan haraji: Yahudawa da yawa suna wa gwamnatin Roma aikin karɓan haraji. Mutane sun tsane su domin suna wa wata gwamnati dabam aiki da kuma karɓan kuɗin haraji fiye da yadda ya kamata su karɓa. Yahudawa sun tsani ’yan’uwansu Yahudawa da suke aikin karɓan haraji, kuma suna ɗaukansu yadda suke ɗaukan masu zunubi da kuma karuwai.—Mt 11:19; 21:32.
(Matta 9:35-38) Yesu ya yi yawo cikin dukan birane da ƙauyuka, yana koyarwa cikin majami’unsu, yana wa’azin bishara ta mulkin, yana warkar da kowace irin cuta da kowane irin rashin lafiya. 36 Amma sa’anda ya ga taron, ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi. 37 Sa’annan ya ce wa almajiransa, Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38 Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aiko ma’aikata cikin girbinsa.
nwtsty na nazarin Mt 9:36
ya yi juyayi: Furucin aikatau na Helenancin nan splag·khniʹzo·mai da aka fassara zuwa wannan furucin yana da a’laka da kalmar nan “hanjin ciki” (splagʹkhna), kuma hakan na kwatanta yadda mutum yake ji a cikin jikinsa. Wannan kalmar tana cikin kalmomin Helenanci da ake amfani da ita don a kwatanta yawan tausayin da mutum ya nuna.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 8:8-10) Jarumin ya amsa, ya ce, Ubangiji, ban isa ba da za ka shiga ƙarƙashin rufina: amma ka yi magana kaɗai, yarona kuma za ya warke. 9 Gama ni wa mutum ne ƙarƙashin iko, ina kuwa da yan yaƙi a ƙarƙashina: ni kan ce wa wannan, jeka, sai ya tafi; in ce wa wani, yaka, sai ya zo; in ce wa bawana, Ka yi kaza, sai shi yi. 10 Sa’anda Yesu ya ji wannan, ya yi mamaki, ya ce wa waɗanda suke bin baya, gaskiya ina ce muku, ko cikin Isra’ila ban iske bangaskiya da girma haka ba.
(Matta 9:16, 17) Kuma ba wanda za ya yi fyacin tsohuwar tufa da sabon yadi; gama tsohuwar tufar za ta kece fyacin, sai yagewa ta karu. 17 Ba kuwa za a sa sabon ruwan anab cikin tsofaffin salkuna ba: gama hakanan sai salkuna su fashe, ruwan anab shi zube, salkuna su lalace: amma a kan sa sabon ruwan anab cikin sababbin salkuna, duka fa sun kiyayu.
jy 70 sakin layi na 6
Me Ya Sa Mabiya Yesu Ba Sa Azumi?
Yesu yana son mabiyan Yohanna mai baftisma su san cewa bai kamata mutane su bukaci mabiyansa su riƙa bin tsofaffin dokokin Yahudawa ba, kamar na yin azumi. Yesu bai zo don ya sa a ci gaba da bin tsofaffin dokokin da an riga an daina amfani da su ba. Kuma ibadar da Yesu yake so a riƙa yi ba wadda ta ƙunshi dokokin Yahudawa na zamaninmu ko kuma al’adar mutane ba. A’a, bai zo don ya saka sabuwar ruwan anab a cikin tsohuwar randa ba.
29 GA JANAIRU–4 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 10-11
“Yesu Ya Ƙarfafa Mutane Kuma Ya Sa Sun Sami Kwanciyar Hankali”
(Matta 10:29, 30, Littafi Mai Tsarki) Ashe, ba gwara biyu ne kobo ba? Ba kuwa ɗayarsu da za ta mutu, ba da yardar Ubanku ba. 30 Ai, ko da gashin kanku ma duk a ƙidaye yake.
nwtsty na nazarin Mt 10:29, 30
gwara: Wannan kalmar Helenancin nan strou·thiʹon tana nufin ƙaramin tsuntsu, amma tana yawan nuni ga gwara domin ita ce tsuntsuwa mafi araha da ake sayarwa.
bakin kobo guda: Wannan kuɗin ne ake biyan mutumin da ya yi aiki na minti 45. (ka duba sgd sashe na 18.) A karo na uku da Yesu ya je Galili, ya ce ana sayar da gwara guda biyu kobo ɗaya. A wani lokaci kuma da yake Yahudiya, wato bayan ya yi shekara ɗaya da hidima, ya ce ana sayar da gwara guda biyar kobo biyu. (Lu 12:6) Idan muka yi la’akari da ayoyin nan, za mu ga cewa tsuntsayen ba su da muhimmanci, shi ya sa na biyar ɗin kamar gyara ne aka yi da shi.
gasussuwan kanku dukansu an ƙididdige su: Masu bincike sun ce iyakar sumar da ke kanmu sun fi 100,000. Jehobah mai hikima ya san kome game da wannan ƙananan abubuwan kuma hakan ya nuna cewa ya damu da dukan bayinsa.
nwtsty hutuna da bidiyo
Gwara
A cikin duka tsuntsaye da ake sayarwa, gwara ne tsuntsu mafi araha. Mutum zai iya sayan guda biyu da kuɗin da ya samu daga yin aikin minti 45. Kalmar Helenancin nan da aka yi amfani da ita ta ƙunshi kowace irin ƙananan tsuntsaye kamar gwara da ake kira common house sparrow (Passer domesticus biblicus) da Spanish sparrow (Passer hispaniolensis), kuma har yanzu akwai irin waɗannan tsuntsayen a Isra’ila.
(Matta 11:28) Ku zo gareni, dukanku da kuke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa.
nwtsty na nazarin Mt 11:28
masu-nauyin kaya: Waɗanda Yesu yake kira su zo suna fama da alhini da ke kama da “nauyin kaya” a gare su. Bautarsu ga Jehobah ta zama masu kamar kaya mai nauyi domin an haɗa al’adar ’yan Adam a cikin Dokar da aka bayar ta hannun Musa. (Mt 23:4) Ko ma ranar Assabaci da ta kamata ta zama ranar hutu ta zama musu kamar kaya mai nauyi.—Fit 23:12; Mk 2:23-28; Lu 6:1-11.
in ba ku hutawa: Kalmar Helenancin nan tana nufin mutum ya huta (Mt 26:45; Mk 6:31) ko kuma ya wartsake don ya sami ƙarfi (2Ko 7:13; Fil 7). Amma a ayar nan, ɗaukan ‘karkiyar’ Yesu (Mt 11:29) ba ta nufin mutum ya huta, maimakon haka, tana nufin mutum ya riƙa yin hidima. Wannan kalmar Helenancin tana nuna cewa Yesu yana ƙarfafa da kuma ba wa waɗanda suka gaji ƙarfi don su iya ɗaukan karkiyarsa.
(Matta 11:29, 30) Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. 30 Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.
nwtsty na nazarin Mt 11:29
Ku ɗaukar wa kanku karkiyata: Yesu ya yi amfani da kalmar nan ‘karkiya’ don ya kwatanta yin biyayya ga umurnin da aka bayar. Idan yana magana game da wata karkiya dabam ce, wato wadda Allah ya ba shi, hakan na nufin yana gaya wa mabiyansa su kasance a ƙarƙashin karkiyarsa don ya taimaka musu. Idan abin da Yesu yake nufi ke nan, za a fassara furucin zuwa: “Ku kasance a ƙarƙashin karkiyata.” Amma idan karkiyar da Yesu yake ba wa mutane ne, furucin na nufin cewa mabiyansa suna bukatar su riƙa yin biyayya ga umurninsa.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 11:2, 3) Amma Yohanna daga cikin kurkuku sa’ad da ya ji labarin ayyukan Kristi, ya aika ta bakin almajiransa, 3 ya ce masa, Kai ne mai-zuwan nan, ko muna sauraron wani?
jy 96 sakin layi na 2-3
Yohanna Yana So Ya Ji Daga Wurin Yesu
Shin wannan tambayar ta ba ka mamaki ne? Yohanna mutum ne mai ibada sosai, kuma sa’ad da yake wa Yesu baftisma, ya ga ruhun Allah ya sauko a kan Yesu. Kari ga haka, ya ji muryar Allah da ta nuna cewa ya amince da Yesu. Don haka, bai kamata mu ɗauka cewa bangaskiyar Yohanna ta yi sanyi ba. Domin Yesu da kansa ma ya yabi Yohanna sosai har ma a wannan lokacin da mabiyan Yohanna suka zo su yi masa tambaya. Amma idan Yohanna bai soma shakkar Yesu ba, me ya sa ya yi wannan tambayar?
Wataƙila Yohanna yana son Yesu da kansa ya tabbatar masa da cewa shi ne Almasihu. Kuma tun da Yohanna yana cikin kurkuku, hakan zai ƙarfafa shi sosai. Tambayar da Yohanna ya yi ta dace sosai. Ya san cewa annabawa sun annabta cewa Almasihu zai zama sarki kuma ya ceci mutane. Amma yanzu Yesu ya yi watanni da yawa da yin baftisma, kuma shi Yohanna na cikin kurkuku. Don haka, Yohanna yana so ya san ko akwai wani da zai zo bayan Yesu da zai cika sauran annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu.
(Matta 11:16-19) Amma da me zan kwatanta wannan tsara? Tana kama da yara waɗanda suke zaune cikin kasuwai, suna kira zuwa abokan wasansu, 17 suna cewa, Mun hura maku busa, ba ku yi rawa ba; muka yi kuka, ba ku buga ƙirji ba. 18 Gama Yohanna ya zo, ba da ci ba, ba da sha ba, suna kuwa cewa, Yana da aljan. 19 Ɗan mutum ya zo, yana ci yana sha, suna kuwa cewa, Ga mutum mai-zarin ci, mai-zarin sha, masoyin masu-karɓan haraji da masu-zunubi! Hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.
jy 98 sakin layi na 1-2
Wahala Za Ta Auko wa Mutanen da Ba Sa Biyayya
Yesu yana daraja Yohanna sosai, amma yaya mutane suka ɗauki Yohanna? Yesu ya ce: ‘Zamanin nan kamar yara ne da ke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa, ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba, Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.’—Matta 11:16, 17.
Mene ne Yesu yake nufi? Ya bayyana abin da yake nufi da cewa: “Yohanna ya zo, ba da ci ba, ba da sha ba, suna kuwa cewa, Yana da aljan. Ɗan mutum ya zo, yana ci yana sha, suna kuwa cewa, Ga mutum mai-zarin ci, mai-zarin sha, masoyin masu-karɓan haraji da masu-zunubi!” (Matta 11:18, 19) Yohanna Ba-nazari ne kuma ya sauƙaƙa rayuwarsa, ba ya shan ruwan inabi, amma mutane sun ce yana da aljan. (Littafin Lissafi 6:2, 3; Luka 1:15) Da Yesu ya zo, ya yi rayuwa yadda ’yan Adam ya kamata su yi. Ya ci, ya sha tare da mutane, amma aka ce wai yana wuce gona da iri. Hakan ya nuna cewa mutum ba zai iya faranta ran ’yan Adam gabaki ɗaya ba.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 1:1-17) Litafin asalin Yesu Kristi, ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim. 2 Ibrahim ya haifi Ishaƙu; Ishaƙu ya haifi Yaƙub; Yaƙub ya haifi Yahuda da ’yan’uwansa; 3 Yahuda ya haifi Parisa da Zaraha daga wurin Thamara; Parisa ya haifi Hasruna; Hasruna ya haifi Arama; 4 Arama ya haifi Amminadaba; Amminadaba ya haifi Nahashuna; Nahashuna ya haifi Salmuna; 5 Salmuna ya haifi Boaz daga wurin Rahab; Boaz ya haifi Obida daga wurin Ruth; sai Obida ya haifi Jessi; 6 Yessi kuwa ya haifi Dawuda sarki. Dawuda ya haifi Solomon daga wacan mata ta Uriya. 7 Solomon ya haifi Rahobowam; Rahobowam ya haifi Abija; Abija ya haifi Asa; 8 Asa ya haifi Jehoshafat; Jehoshafat ya haifi Joram; Joram haifi Uzza; 9 Uzzaja ya haifi Yuthama; Yuthama ya haifi Ahaza; Ahaza ya haifi Hizƙiya; 10 Hezekiya ya haifi Manassa; Manassa ya haifi Amuna; Amuna ya haifi Yushiya; 11 Yushiya ya haifi Yakunya da ’yan’uwansa, kwanakin kwasa zuwa Babila. 12 Bayan kwasa zuwa Babila, Yakunya ya haifi Sha’altiila; Sha’altiila ya haifi Zarubbabila; 13 Zarubbabila ya haifi Abihuda; Abihuda ya haifi Aliyaƙima; Aliyaƙima ya haifi Azura;14 Azura ya haifi Saduƙa; Saduƙa ya haifi Ahima; Ahima ya haifi Aliyuda; 15 Aliyuda ya haifi Ali’azara; Ali’azara ya haifi Mattana; Mattana ya haifi Yaƙub; 16 Yaƙub ya haifi Yusufu mijin Maryamu, wadda aka haifi Yesu daga wurinta, wanda ana kiransa Kristi. 17 Dukan tsararakin fa daga Ibrahim zuwa Dawuda goma sha huɗu ne; daga Dawuda kuwa zuwa kwasa cikin Babila tsara goma sha huɗu ne; daga kwasa cikin Babila zuwa Kristi tsara goma sha huɗu ne.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 5:31-48) Kuma aka faɗi, Dukan wanda za ya saki matatasa sai shi ba ta takarda ta saki. 32 Amma ni ina ce maku, Kowanene ya saki matatasa, im ba domin fasikanci ba, yana sa ta ta zama mazinaciya: kuma dukan wanda ya amre sakakkiya, zina ya ke yi. 33 Kuma, kun ji aka faɗa ma mutanen dā, Ba za ka yi rantsuwa da ƙarya ba, amma sai ka cika wa’adodinka ga Ubangiji. 34 amma ni ina ce maku, Ba za ku yi rantsuwa ko kaɗan ba; ko bisa sama, gama kursiyin Allah ce; 35 ko kuwa bisa duniya, gama matashin sawayensa ce; ko kuwa wajen Urushalima, gama birnin maɗaukakin Sarki ce. 36 Ba kuwa za ka yi rantsuwa bisa kanka ba, gama ko gashi guda ɗaya ba ka da iko ka maishe shi fari ko baƙi. 37 Amma bari zancenku ya zama, I, i; da A’a, a’a: abin da ya wuce waɗannan duka daga wurin Mugun ne. 38 Kun ji aka faɗi, Ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori. 39 amma ni ina ce muku, Ba za ku yi tsayayya da wanda shi ke mugu ba: amma iyakar wanda ya mare ka a kumatu na dama, juya masa wancan kuma. 40 Idan kuma wani yana so ya kai ka shari’a, shi karɓe maka rigarka, bar masa mayafinka kuma. 41 Kuma dukan wanda ya tilasta maka tafiya mile ɗaya, tafi tare da shi har biyu. 42 Ka bayas ga wanda ya roƙe ka, wanda yana so ya yi ramce a wurinka kuma, kada ka ba shi baya. 43 Kun ji aka faɗi, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka, ka ƙi magabcinka: 44 amma ni ina ce muku, Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda sukan tsananta muku, ku yi musu addu’a; 45 domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama: gama ya kan sa ranarsa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci. 46 Gama idan kuna ƙaunar masu ƙaunarku kaɗai, wace lada ke gareku? ko masu-karɓan haraji ba haka su ke yi ba? 47 Idan kuwa kuna gaida ’yan’uwanku kaɗai, ina fifikonku waɗansu? ko al’ummai ma ba haka su ke yi ba? 48 Ku fa za ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 6:1-18) Ku yi lura kada ku yi marmarin nuna adalcinku a gaban mutane, domin su gani: in ba haka ba, ba ku da lada a wurin Ubanku wanda ke cikin sama. 2 Sa’anda fa kake yin sadaka, kada ka busa ƙaho a gabanka, kamar yadda munafukai ke yi cikin majami’u da hanyoyi, domin su sami daraja a wurin mutane. Gaskiya ina ce muku, Sun rigaya sun karɓi ladarsu. 3 Amma sa’anda kake yin sadaka, kada ka bar hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama ke yi: 4 domin sadakarka ta kasance a ɓoye: gama Ubanka kuwa wanda ya ke gani daga cikin ɓoye za ya sāka maka a gaban kowa. 5 Sa’an da kuke yin addu’a kuma, kada ku zama kamar munafukai: gama su suna so su tsaya su yi addu’a a cikin majami’u da ƙusurwoyin karabku, domin mutane su gan su. Gaskiya ni ke ce muku, sun rigaya sun karɓi ladarsu. 6 Amma kai, lokacin da kake yin addu’a, shiga cikin lolokinka, bayan da ka rufe ƙofarka kuma, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ke cikin ɓoye, Ubanka kuwa wanda yake gani daga cikin ɓoye za ya sāka maka. 7 Garin yin addu’a kuma kada ku yi ta maimaitawa ta banza, kamar yadda arna suke yi: gama suna tsammani bisa ga yawan maganarsu za a amsa masu. 8 Kada ku zama kamarsu fa: gama Ubanku ya san abin da kuke bukata, tun ba ku roƙe shi ba. 9 Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka. 10 Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama. 11 Ka ba mu yau abincin yini. 12 Ka gafarta mana laifofinmu, kamar yadda mu kuma muke gafarta wa waɗanda suka yi mana laifi. 13 Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga mugun. 14 Gama idan kuna gafarta wa mutane laifofinsu, Ubanku na sama shi ma za ya gafarta muku. 15 Amma idan ba ku gafarta wa mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba za shi gafarta naku laifofin ba. 16 Kuma lokacinda ku ke yin azumi, kada ku ƙwansare fuskarku, kamar yadda masu-riya ke yi: gama suna ɓata fuskokinsu, domin mutane su gani suna azumi. 17 Amma kai, lokacinda ka ke yin azumi, shafe kanka da mai, ka wanke fuskarka. 18 Domin kada ka bayana ga mutane kana azumi, sai Ubanka wanda ke cikin ɓoye ya gani: Ubanka da ke gani daga cikin ɓoye kuwa, za ya sāka maka.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 8:1-17) Sa’ad da ya gangaro daga dutsen, taron jama’a mai-yawa suka bi shi. 2 Sai wani kuturu kuma ya zo wurinsa, ya yi masa sujada, ya ce, Ubangiji, idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni. 3 Ya miƙa hannuwansa, ya taɓa shi, ya ce, Na yarda; ka tsarkaka. Nan da nan fa kuturtarsa ta tsarkaka. 4 Yesu ya ce masa, Lura kada ka faɗa wa kowa; amma ka yi tafiyarka, ka nuna kanka ga malamai, kuma ka ba da baiko wanda Musa ya umurta, domin shaida garesu. 5 Sa’anda ya shiga Kafarnahum, wani jarumi ya zo wurinsa, yana roƙonsa, 6 yana cewa, Ubangiji, yarona yana ƙwance a gida, yana ciwon inna, yana shan azaba ƙwarai. 7 Ya ce masa, zan zo in warkar da shi. 8 Jarumin ya amsa, ya ce, Ubangiji, ban isa ba da za ka shiga ƙarƙashin rufina: amma ka yi magana kaɗai, yarona kuma za ya warke. 9 Gama ni wa mutum ne ƙarƙashin iko, ina kuwa da yan yaki a ƙarƙashina: ni kan ce wa wannan, jeka, sai ya tafi; in ce wa wani, yaka, sai ya zo; in ce wa bawana, Ka yi kaza, sai shi yi. 10 Sa’anda Yesu ya ji wannan, ya yi mamaki, ya ce wa waɗanda suke bin baya, gaskiya ina ce muku, ko cikin Isra’ila ban iske bangaskiya da girma haka ba. 11 Kuma ina ce maku, mutane da yawa daga gabas da yamma za su zo, su zauna tare da Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, cikin mulkin sama. 12 amma za a fitarda ’ya’yan mulki cikin baƙin duhu: can za a yi kuka da taunar haƙora. 13 Yesu ya ce wa jarumin, Yi tafiyarka; kamar da ka ba da gaskiya, haka nan shi zama maka. Yaron kuma ya warke cikin wannan sa’a. 14 Sa’ad da Yesu ya shiga gidan Bitrus, ya ga surukuwarsa tana ƙwance, da ciwon zazzaɓi. 15 Ya taɓa hannunta, sai zazzaɓin ya sake ta; ta tashi, kuma ta yi masa hidima. 16 Sa’anda maraice ya yi, suka kawo masa masu-aljanu dayawa: da magana kuwa ya fitarda ruhohi, ya warkadda masu-ciwo duka: 17 domin a cika magana da aka faɗi ta bakin annabi Ishaya, cewa, Shi da kansa ya karɓi kumamancinmu, ya ɗauki cututtukanmu.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 11:1-19) Ananan sa’anda Yesu ya gama ba almajiransa goma sha biyu umurni, ya tashi daga wurin, domin ya yi koyaswa da wa’azi a cikin biranensu. 2 Amma Yohanna daga cikin kurkuku sa’ad da ya ji labarin ayyukan Kristi, ya aika ta bakin almajiransa, 3 ya ce masa, Kai ne mai-zuwan nan, ko muna sauraron wani? 4 Yesu ya amsa, ya ce musu, Ku yi tafiyarku, ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji da abin da kuka gani: 5 makafi suna samun ganin gari, guragu suna tafiya, kutare suna tsarkaka, kurame suna ji, ana tada matattu, ana yi wa talakawa wa’azin bishara. 6 Mai albarka ne wanda bai yi tuntube saboda ni ba. 7 Sa’ad da waɗannan suka kama hanyarsu, Yesu ya soma yin magana da taron jama’a a kan Yohanna, ya ce, me kuka tafi cikin jeji garin ku duba? Kāra ce wadda iska take rarrawar da ita? 8 Amma garin duban mene ne kuka tafi? Ko mutum mai-yafe da tufafi masu-tabshi? Ku duba, waɗanda suke yafe da tufafi masu-tabshi a cikin gidajen sarakuna suke. 9 Amma don me kuka fita? Garin duban annabi ne? I, ina ce muku, har ya fi gaban annabawa da yawa. 10 Shi ne wannan wanda aka rubuta a kansa, Duba, ina aika manzona a gaban ka, wanda za shi shirya tafarkinka a gabanka. 11 Hakika ina ce maku, A cikin waɗanda an haifa daga wajen mata ba wanda ya tashi wanda ya fi Yohanna Mai-yin baptisma girma: duk da haka, wanda shi ke ƙanƙani a cikin mulkin sama ya fi shi girma. 12 Daga zamanin Yohanna Mai-yin baftisma har yanzu kuma mulkin sama yana shan gwagwarmaya, masu-gwagwarmaya kuwa su kan ci shi da ƙarfi. 13 Gama dukan annabawa da attaurat suka yi annabci har zuwa kwanakin Yohanna. 14 Idan kuwa kuna nufin karɓa, wannan shi ne Iliya mai-zuwan nan. 15 Wanda yake da kunnuwa na ji, bari shi ji. 16 Amma da me zan kwatanta wannan tsara? Tana kama da yara waɗanda suke zaune cikin kasuwai, suna kira zuwa abokan wasansu, 17 suna cewa, Mun hura maku busa, ba ku yi rawa ba; muka yi kuka, ba ku buga ƙirji ba. 18 Gama Yohanna ya zo, ba da ci ba, ba da sha ba, suna kuwa cewa, Yana da aljan. 19 Ɗan mutum ya zo, yana ci yana sha, suna kuwa cewa, Ga mutum mai-zarin ci, mai-zarin sha, masoyin masu-karɓan haraji da masu-zunubi! Hikima kuwa ta barata bisa ga ayyukanta.