WAƘA TA 78
Mu Riƙa Koya wa Mutane Maganar Allah
Hoto
1. In duk muna yin wa’azi
Da kuma koyarwa,
Jehobah Allah mai ƙauna
Zai albarkace mu.
In muna koyi da Yesu
A duk koyarwarmu,
Mutanen da muke koyarwa
Za su bi Jehobah.
2. Mu da ke yin bisharar nan
Mu riƙa nagarta,
In muna nagarta sosai
Za mu ɗaukaka Shi.
Muna nazarin Kalmarka
Don mu san gaskiya.
Shi ya sa muke yin bishara
Da koyar da kanmu.
3. Allah na taimaka mana
Mu yaɗa bishara.
In mun nemi taimakonsa,
Zai ji addu’armu.
Muna son Kalmarsa sosai,
Kalmar gaskiya ce.
In muna ƙaunar ɗalibinmu
Zai ƙaunaci Allah!
(Ka kuma duba Zab. 119:97; 2 Tim. 4:2; Tit. 2:7; 1 Yoh. 5:14.)