WAƘA TA 134
Yara Amana Ne Daga Allah
(Zabura 127:3-5)
1. In ma’aurata sun haihu
Sun sami gādo da kyauta babba.
Allah ne ya ba su amana
Don su kula da su sosai.
Su yi koyarwa cikin ƙauna
Kamar Jehobah Mahaliccinmu.
Shi ya ba iyaye umurni
Domin su koyar da ’ya’yansu.
(AMSHI)
Jehobah ne ya ba ku ’ya’ya,
Ku kula da ’ya’yan sosai.
Ku sa su san Kalmar Jehobah
Domin su amfana sosai.
2. Dukan dokokin Jehobah
Su kasance a cikin zucinku.
Ku koya wa ’ya’yanku duka,
Don su san dokokin sosai.
Allah ya ba ku su amana,
Ku koyar da su dare da rana.
Za su tuna da dokokin nan
Kuma su riƙe amincinsu.
(AMSHI)
Jehobah ne ya ba ku ’ya’ya,
Ku kula da ’ya’yan sosai.
Ku sa su san Kalmar Jehobah
Domin su amfana sosai.
(Ka kuma duba K. Sha. 6:6, 7; Afis. 6:4; 1 Tim. 4:16.)