Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 4/1 pp. 22-26
  • ‘Ku Tafi Fa, Ku Almajirtar, Kuna Yi Musu Baftisma’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ku Tafi Fa, Ku Almajirtar, Kuna Yi Musu Baftisma’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tuba da Kuma Keɓe Kai
  • Ka Zama Mashaidin Jehobah
  • Abin da Ya Sa Ake Yin Baftisma
  • Baftisma da Kuma Dangantakarka da Allah
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ya Sa Za Ka Yi Baftisma?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Cika Farillan Baftisma Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 4/1 pp. 22-26

‘Ku Tafi Fa, Ku Almajirtar, Kuna Yi Musu Baftisma’

“Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma . . . kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.”—MATTA 28:19, 20.

1. Wace shawara ce al’ummar Isra’ila ta yanke a ƙarƙashin Dutsen Sinai?

SHEKARA 3,500 da ta shige, wata al’umma ta yi wa Allah alkawari. Isra’ilawa suka taru a ƙarƙashin Dutsen Sinai suka ce: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.” Tun daga wannan lokacin, Isra’ila ta zama mutanen da aka keɓe wa Allah, wato, “keɓaɓiyar taska.” (Fitowa 19:5, 8; 24:3) Suna sa rai ga samun kāriya daga wurin Jehobah kuma zuriyoyinsu za su ci gaba da zama cikin ƙasa “mai-zuba da madara da zuma.”—Leviticus 20:24.

2. Wace dangantaka ce mutane a yau za su iya mora da Allah?

2 Kamar yadda mai zabura Asaph ya faɗa, Isra’ilawa “ba su kiyaye alkawarin Allah ba, suka ƙi yin tafiya cikin shari’assa.” (Zabura 78:10) Sun ƙi su cika alkawarin da kakanninsu suka yi da Jehobah. Daga bisani, al’ummar ta yi hasarar dangantaka mai tamani da take da shi da Allah. (Mai-Wa’azi 5:4; Matta 23:37, 38) Saboda haka, Allah ya “ziyarci al’ummai, domin shi ciro wata jama’a daga cikinsu domin sunansa.” (Ayukan Manzanni 15:14) A wannan zamani na ƙarshe, Allah yana tattara “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa, daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna,” waɗanda cikin farin ciki suke cewa: “Ceto ga Allahnmu ne wanda ya zauna bisa kursiyin, ga Ɗan ragon kuma.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10.

3. Waɗanne matakai ne ake bukatar a ɗauka don morar dangantaka da Allah?

3 Domin ya kasance cikin mutanen da za su more irin wannan dangantaka mai tamani da Allah, dole ne mutum ya keɓe kansa ga Jehobah kuma ya bayyana hakan a zahiri ta wajen yin baftisma. Wannan biyayya ce ga umurnin da Yesu ya ba almajiransa: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Isra’ilawa sun saurara sa’ad da ake karanta “litafin alkawari.” (Fitowa 24:3, 7, 8) Da haka, sun fahimci hakkinsu ga Jehobah. Hakazalika a yau, yana da muhimmanci a fahimci cikakken sanin nufin Allah kamar yadda yake a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, kafin a ɗauki matakin yin baftisma.

4. Menene mutum zai yi idan yana son ya yi baftisma? (Ka haɗa da akwatin da ke sama.)

4 Babu shakka, Yesu yana son almajiransa su kasance da bangaskiya mai ƙarfi kafin su yi baftisma. Ya umurci mabiyansa su je su almajirtar kuma su koyar da mutane su ‘kiyaye dukan iyakar abin da ya umurce su.’ (Matta 7:24, 25; Afisawa 3:17-19) Waɗanda suka cancanci su yi baftisma mutane ne da suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki na watanni ko kuwa shekara ɗaya ko biyu, saboda su yi tunani sosai game da baftismar da za su yi kuma su yanke shawara mai kyau. A lokacin baftisma kuma, waɗanda za su yi baftisma za su ce i ga muhimman tambayoyi biyu. Tun da yake Yesu ya nanata cewa ya kamata ‘I, ya kasance i; kuma A’a, a’a,’ zai dace idan dukanmu muka sake bincika muhimmancin waɗannan tambayoyin biyu na baftisma.—Matta 5:37.

Tuba da Kuma Keɓe Kai

5. Waɗanne muhimman matakai biyu ne tambayoyin farko na baftisma suka nanata?

5 Tambaya ta farko da ake yi wa wanda zai yi baftisma ita ce, ko ya tuba daga tafarkin rayuwarsa na dā kuma ya keɓe ransa ga yin nufin Jehobah. Wannan tambayar ta nanata matakai biyu da ake bukatar ɗauka kafin a yi baftisma, wato, tuba da kuma keɓe kai.

6, 7. (a) Me ya sa duka waɗanda suke son su yi baftisma suke bukatar su tuba? (b) Waɗanne canje-canje ne mutum yake bukatar ya yi bayan ya tuba?

6 Me ya sa mutum yake bukatar ya tuba kafin ya ba da kansa ga baftisma? Manzo Bulus ya yi bayani: “Mu duka muna zamanmu a dā a cikin sha’awoyin jikinmu.” (Afisawa 2:3) Kafin mu sami cikakken sanin nufin Allah, muna irin rayuwa ce da ta jitu da duniya, wato darajarta da kuma mizananta. Tafarkin rayuwarmu yana ƙarƙashin ikon allahn wannan zamanin, wato, Shaiɗan. (2 Korinthiyawa 4:4) Da muka fahimci nufin Allah, mun ƙudurta cewa ba za mu ƙara “sha’awoyin mutane, sai dai nufin Allah.”—1 Bitrus 4:2.

7 Wannan sabon tafarkin na kawo albarka mai yawa. Fiye da kome, yana ba mu zarafin ƙulla dangantaka mai tamani da Jehobah, wanda Dauda ya kwatanta hakan da gayyatar shiga ‘tanti’ na Allah da kuma ‘tudunsa mai-tsarki,’ wannan gata ce mai girma. (Zabura 15:1) Jehobah zai gayyaci waɗanda kawai ‘suke tafiya sosai, suna aika adalci, suna kuwa faɗin gaskiya cikin zuciyarsu.’ (Zabura 15:2) Domin yanayinmu kafin mu koyi gaskiya, wataƙila muna bukatar mu yi wasu canje-canje a halinmu da mutuntakarmu don mu cika waɗannan ƙa’idodin. (1 Korinthiyawa 6:9-11; Kolossiyawa 3:5-10) Abin da zai motsa mu mu yi irin waɗannan canje-canje shi ne tuba, wato, yin nadama domin tafarkin rayuwarmu na dā da kuma ƙudurta aniyar faranta wa Jehobah rai. Wannan na sa mu yi canji gabaki ɗaya, wato, yin watsi da hanyar rayuwa ta duniya ta son kai, kuma mu biɗi tafarkin yin nufin Allah.—Ayukan Manzanni 3:19.

8. Ta yaya muke keɓe kanmu, kuma wace nasaba ce ke tsakaninsu da baftisma?

8 Sashe na biyu na tambaya ta farko ta baftisma ya tambayi waɗanda suke son su yi baftisma ko sun riga sun keɓe kansu don yin nufin Jehobah. Keɓe kai mataki ne mai muhimmanci da ake bukatar a ɗauka kafin a yi baftisma. Ana yin sa ne a addu’a, a nan ne muke furta muradi na ba da rayuwarmu ga Jehobah ta wurin Kristi. (Romawa 14:7, 8; 2 Korinthiyawa 5:15) Da haka, Jehobah zai zama Ubangidanmu, kuma kamar Yesu muna murnan yin nufin Allah. (Zabura 40:8; Afisawa 6:6) Wannan alkawari sau ɗaya ake yin sa ga Jehobah. Tun da yake keɓe kai tsakaninmu ne da Allah, furtawa a fili a ranar da za mu yi baftisma na sa kowa ya sani cewa mun keɓe kanmu ga Ubanmu na sama.—Romawa 10:10.

9, 10. (a) Menene yin nufin Allah ya ƙunsa? (b) Ta yaya ne ma’aikatan Nazi suka fahimci keɓe kanmu?

9 Menene bin misalin Yesu na yin nufin Allah ya ƙunsa? Yesu ya gaya wa almajiransa: “Idan kowane mutum yana da nufi shi bi bayana, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki [gungumen azabarsa], shi biyo ni.” (Matta 16:24) A nan ya bayyana abubuwa uku da wajibi ne mu yi su. Na farko, mu yi “musun” kanmu. Wato, hakan na nufin mu ƙi son kai, tunaninmu na ajizanci, mu kuma amince da shawara da kuma ja-gorar Allah. Na biyu, mu ɗauki ‘gungumen azabarmu.’ A zamanin Yesu, gungumen azaba alama ce ta abin kunya da kuma wahala. Mu Kiristoci mun yarda cewa a wasu lokatai muna iya shan wahala domin bishara. (2 Timothawus 1:8) Ko da yake duniya tana iya yi mana ba’a ko ta la’ance mu, amma kamar Kristi, muna “rena kunya,” domin mun san cewa muna faranta wa Allah rai. (Ibraniyawa 12:2) Na ƙarshe shi ne, mu ci gaba da ‘bin’ Yesu.—Zabura 73:26; 119:44; 145:2.

10 Abin farin ciki, har wasu ’yan hamayya sun fahimci keɓe kai da Shaidun Jehobah suka yi ga Allah don su bauta masa shi kaɗai. Alal misali, a sansanin fursunan Buchenwald na Nazi da ke Jamus, an umurci Shaidun da suka ƙi yin musun imaninsu su cika kalaman da aka buga da suke gaba: “Har yanzu ni cikakken Ɗalibin Littafi Mai Tsarki ne, kuma ba zan taɓa karya alkawarin da na yi wa Jehobah ba.” Hakika, wannan ya bayyana halin dukan keɓaɓɓun bayin Allah masu aminci!—Ayukan Manzanni 5:32.

Ka Zama Mashaidin Jehobah

11. Wane gata ne wanda ya yi baftisma ke da shi?

11 Tambaya ta biyu da ake yi wa wanda zai yi baftisma ita ce, ko ya fahimci cewa baftismarsa ta nuna cewa shi Mashaidin Jehobah ne. Bayan baftismar, zai zama mai hidima da aka naɗa wanda ke ɗauke da sunan Jehobah. Wannan gata ne babba kuma hakki ne mai girma. Kuma hakan na sa wanda ya yi baftismar ya kasance da begen rai madawwami idan ya kasance da aminci ga Jehobah.—Matta 24:13.

12. Wane hakki ne ke tattare da gatar ɗaukan sunan Jehobah?

12 Hakika, gata ne mai girma mu kasance masu ɗauke da sunan Allah Maɗaukaki, Jehobah. Annabi Mikah ya ce: “Gama dukan kabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” (Mikah 4:5) Duk da haka, wannan gatan na ɗauke da hakki. Dole ne mu yi rayuwar da za ta ɗaukaka sunan da muke ɗauke da shi. Kamar yadda Bulus ya tuna wa Kiristocin da ke Roma, idan mutum bai aikata abin da yake wa’azinsa ba, ya yi “saɓon” sunan Allah ko kuwa ya sa an rena sunan.—Romawa 2:21-24.

13. Me ya sa keɓaɓɓun bayin Jehobah suke da hakkin yin shaida game da Allahnsu?

13 Idan mutum ya zama Mashaidin Jehobah, dole ne ya ɗauki hakkin yin wa’azi game da Allahnsa. Jehobah ya gayyaci keɓaɓiyar al’ummar Isra’ila ta zama shaidarsa domin ta tabbatar da Allahntakarsa na har abada. (Ishaya 43:10-12, 21) Amma al’ummar ta ƙi ta cika wannan hakkin, kuma daga bisani suka rasa tagomashin Jehobah gabaki ɗaya. A yau, Kiristoci na gaskiya suna alfaharin samun gatar yin shaida game da Jehobah. Muna yin haka ne domin muna ƙaunarsa kuma muna son a tsarkake sunansa. Ba za mu iya yin shuru ba domin mun san gaskiya game da Ubanmu na sama da kuma manufarsa. Muna ji kamar manzo Bulus sa’ad da ya ce: “Gama ya zama mini dole; kaitona fa in ban yi wa’azin bishara ba.”—1 Korinthiyawa 9:16.

14, 15. (a) Menene matsayin ƙungiyar Jehobah wajen ci gabanmu a ruhaniya? (b) Waɗanne tanadodi ne aka yi don a taimaka mana a ruhaniya?

14 Tambaya ta biyu tana tuna wa wanda zai yi baftisma game da hakkinsa na ba da haɗin kai ga ƙungiyar Jehobah da ruhunsa ke yi wa ja-gora. Ba mu kaɗai ba ne muke bauta wa Allah, kuma muna bukatar taimako, da ƙarfafa na ‘ ’yan’uwa.’ (1 Bitrus 2:17; 1 Korinthiyawa 12:12, 13) Ƙungiyar Allah tana da matsayi na musamman wajen ci gabanmu a ruhaniya. Tana yin tanadin isassun littattafai na Littafi Mai Tsarki da suke taimaka mana mu ƙara samun cikakken sani, mu aikata da hikima sa’ad da muka fuskanci matsaloli, mu kuma gina dangantaka ta kud da kud da Allah. Kamar uwar da take tabbatawa cewa ɗanta ya sami isashen abinci da kulawa, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” yana yin tanadin isashen abinci na ruhaniya a kan kari domin ci gabanmu a ruhaniya.—Matta 24:45-47; 1 Tassalunikawa 2:7, 8.

15 A taronsu na mako-mako, mutanen Jehobah suna samun koyarwa da kuma ƙarfafa da suke bukata don su kasance Shaidun Jehobah masu aminci. (Ibraniyawa 10:24, 25) Makarantar Hidima ta Allah tana koyar da mu mu yi magana a inda mutane suke, Taron Hidima kuma yana koyar da mu yadda za mu iya isar da saƙonmu a hanyar da ta dace. Ta taronmu da kuma nazarinmu na littattafai na Littafi Mai Tsarki, mun ga cewa ruhun Jehobah na aiki kuma yana yi wa ƙungiyar ja-gora. Ta wajen waɗannan tanadodin na kullum, Allah yake sanar da mu haɗarori, yake koyar da mu mu zama ƙwararrun masu hidima, kuma yake taimaka mana mu kasance a faɗake a ruhaniya.—Zabura 19:7, 8, 11; 1 Tassalunikawa 5:6, 11; 1 Timothawus 4:13.

Abin da Ya Sa Ake Yin Baftisma

16. Menene ke motsa mu mu keɓe kanmu ga Jehobah?

16 Tambayoyin biyu na baftisma suna tuna wa waɗanda za su yi baftismar muhimmancin baftisma da kuma hakkin da ke tattare da yin haka. Menene ya kamata ya motsa su su yanke shawarar yin baftisma? Mun zama almajiran da aka yi wa baftisma ba don wani ya matsa mana ba, amma domin Jehobah ya “jawo” mu. (Yohanna 6:44) Tun da yake “Allah ƙauna ne,” yana sarautar sararin samaniya cikin ƙauna, ba da matsi ba. (1 Yohanna 4:8) Muna kusantar Jehobah ne domin halayensa masu kyau da kuma yadda yake hulɗa da mu. Jehobah ya ba da Ɗansa makaɗaici dominmu, kuma ya yi alkawarin rayuwa mafi kyau a nan gaba. (Yohanna 3:16) Hakan ya motsa mu mu keɓe masa rayuwarmu.—Misalai 3:9; 2 Korinthiyawa 5:14, 15.

17. Ga menene ne ba mu keɓe kanmu ba?

17 Mun keɓe kanmu ga Jehobah ne kawai, ba ga wani tafarki ko aiki ba. Aikin da Allah ya ba mutanensa zai canja, amma keɓe kan da suka yi masa ba za ta canja ba. Alal misali, abin da Jehobah ya ce Ibrahim ya yi ya bambanta da wanda ya ce Irmiya ya yi. (Farawa 13:17, 18; Irmiya 1:6, 7) Duk da haka, waɗannan mutanen sun yi ainihin aikin da Allah ya ba su domin suna ƙaunar Jehobah kuma suna son su yi nufinsa cikin aminci. A wannan zamani na ƙarshe, duka mabiyan Kristi da suka yi baftisma suna ƙoƙarin cika umurnin Kristi na yin wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa. (Matta 24:14; 28:19, 20) Yin wannan aikin da zuciya ɗaya ita ce hanya mafi kyau da za mu iya bayyana ƙaunarmu ga Ubanmu na sama da kuma nuna cewa mun keɓe masa kanmu da gaske.—1 Yohanna 5:3.

18, 19. (a) Menene muke bayyanawa a fili sa’ad da muka yi baftisma? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?

18 Babu shakka, baftisma na ba mu damar samun albarkatu masu yawa, amma ba abu ba ne da ya kamata mu ɗauka da wasa. (Luka 14:26-33) Hakan na bayyana ƙudirin da ya kamata mu ɗauka da muhimmanci fiye da kowanne. (Luka 9:62) Sa’ad da muka yi baftisma, muna furtawa ne a fili cewa: “Gama wannan Allah Allahnmu ne har abada abadin: Za ya zama ja gabanmu har zuwa mutuwa.”—Zabura 48:14.

19 Talifi na gaba zai tattauna ƙarin tambayoyin da za su iya tasowa game da baftisma. Da wasu kyawawan dalilai ne da za su iya hana mutum yin baftisma? Shekaru na da muhimmanci? Ta yaya dukanmu za mu iya daraja wannan lokaci na baftisma?

Za Ka Iya Yin Bayani?

• Me ya sa kowane Kirista na bukatar ya tuba kafin ya yi baftisma?

• Menene keɓe kai ga Allah ya ƙunsa?

• Wane hakki ne ke tattare da gatar ɗaukar sunan Jehobah?

• Menene ya kamata ya motsa mu mu yanke shawarar yin baftisma?

[Box/Hoto a shafi na 23]

Tambayoyi Biyu na Baftisma

Bisa ga hadayar Yesu Kristi, kun tuba daga zunubanku kuma kun keɓe kanku ga Jehobah domin ku yi nufinsa?

Kun fahimci cewa keɓe kanku da kuma baftisma na nuna cewa ku Shaidun Jehobah ne cikin haɗin kai da ƙungiyar Allah da ruhu ke ja-gora?

[Hoto a shafi na 24]

Keɓe kai cikakken alkawari ne da ake yi wa Jehobah cikin addu’a

[Hoto a shafi na 26]

Wa’azinmu na bayyana keɓe kanmu ga Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba