Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
5-11 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 12-13
“Kwatancin Alkama da Zawan”
(Matta 13:24-26) “Ya kawo masu wani misali, ya ce, Mulkin sama yana kama da mutum wanda ya shuka iri mai-kyau cikin gonarsa: 25 amma lokacin da mutane suna barci, maƙiyinsa ya zo, ya shuka zawan kuma a tsakanin alkama, ya tafi. 26 Amma sa’anda hatsi ya yi girma, har ya yi ƙwaya, sa’annan zawan kuma suka bayyana.”
(Matta 13:27-29) Sai bayin mai-gidan suka zo, suka ce masa, Malam, ba iri mai-kyau ba ka shuka a gonarka? Ina fa ta sami zawan? 28 Ya ce masu, Wani waƙiyi ya yi wannan. Bayin suka ce masa, Kana so mu tafi mu tumɓuke su? 29 Amma ya ce, A’a; kada ya zama lokacin da kuke tumɓuken zawan, ku tumɓuke alkama tare da su.
(Matta 13:30) Bar su duka biyu su yi girma tare har kaka: lokacin kaka kuma in ce wa masu-girbi, Ku tattara zawan tukuna, a ɗaure su cikin kaya, domin a ƙone su: amma ku tattara alkama, ku kai rumbuna.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 12:20) Rarraunan kara ba za ya karye ta ba, Atafa mai-hayaƙi kuma ba za ya ɓiche ta ba, har shi aike shari’a zuwa nasara.
nwtsty na nazarin Mt 12:20
Atafa mai-hayaƙi: Fitila ce da aka yi da taɓo kuma ana saka mān zaitun a ciki. Atafar, wato lagwanin ne ake cinna masa wuta. Furucin nan Atafa mai-hayaƙi a Helenanci na iya nufin lagwanin fitillar da aka kashe amma wutar da ke lagwanin ba ta gama mutuwa ba. Annabcin da ke Ishaya 42:3 ya nuna cewa Yesu zai zama mai tausayi sosai, ya ce ba za ya ɓice, wato kashe begen da talakawa suke da shi ba.
(Matta 13:25) Amma lokacin da mutane suna barci, maƙiyinsa ya zo, ya shuka zawan kuma a tsakanin alkama, ya tafi.
12-18 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 14-15
“Yesu Yana Ciyar Da Jama’a Ta Hannun Mutane Ƙalilan”
(Matta 14:16, 17) Amma Yesu ya ce masu, kada ku salame su haka; amma ku ba su abinci. 17 Suka ce masa, ba mu da komai nan sai burodi biyar, da kifi biyu
(Matta 14:18, 19) Ya ce, ku kawo su nan wurina. 19 Ya umurci taro su zauna bisa ɗanyar ciyawa; ya ɗauko dunƙulen nan biyar, da kifi biyu, ya ta da idanu sama, kāna ya albarkace su, ya kakkarya, ya ba da dunƙulen nan ga almajiransa, almajiran kuwa suka ba taron.
(Matta 14:20, 21) Dukansu suka ci, suka ƙoshi: aka tattara abin da ya rage a wajen gutsatsari, kwando goma sha biyu cike da su. 21 Waɗanda suka ci maza wajen dubu biyar ne, ban da mata da yara.
nwtsty na nazarin Mt 14:21
ban da mata da yara: Matta ne kawai ya ambata cewa akwai mata da yara a cikin mutanen da Yesu ya ciyar a mu’ujizar da ya yi. Don haka, wataƙila yawan mutanen da ya ciyar sun fi dubu 15,000.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 15:7-9) Ku masu-riya, daidai Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce, 8 Wannan al’umma tana girmamana da leɓunansu; Amma zuciyarsu tana nesa da ni. 9 Amma banza su ke yi mani sujada, koyarwa da su ke yi dokokin mutane ne.
nwtsty na nazarin Mt 15:7
masu-riya: Kalmar Helenancin hy·po·kri·tesʹ da farko tana nuni ne ga masu wasan kwaikwayo na Helas. Amma daga baya, an yi amfani da ita wajen kwatanta ’yan wasan kwaikwayon Roma waɗanda suke rufe fuskarsu kuma su canja muryarsu. Bayan haka, an yi amfani da kalmar a alamance sa’ad da ake magana game da mutanen da suke ɓoye kamaninsu ko kuma manufarsu don su yi wasa ko cim ma wani abu. A nan Yesu ya yi amfani da wannan furucin “munafukai” yin nuni ga malaman addinan Yahudawa.—Mt 6:5, 16.
(Matta 15:26) Ya amsa, ya ce, Bai da kyau a ɗauki abincin ’ya’ya a jefa wa karnuka.
nwtsty na nazarin Mt 15:26
’ya’ya . . . ’yan karnuka: Da yake dokar da aka bayar ta hannun Musa ta nuna cewa karnuka ba su da tsarki, Littafi Mai Tsarki yana yawan kwatanci da su a hanya marar kyau. (Le 11:27; Mt 7:6; Fib 3:2; R. Yoh 22:15) Amma a labarin da Markus ya rubuta (7:27) da kuma na Matta game da zancen da Yesu ya yi, an yi amfani da kalmar da ke nufin “ɗan kare” ko “karen gida”, don a sauƙaƙa munin kwatancin da aka yi. Wataƙila Yesu yana nuni ne ga dabbobin da mutane waɗanda ba Yahudawa suke kiwon su a gidajensu. Kuma yadda Yesu ya kwatanta Isra’ilawa da “’ya’ya” sa’an nan waɗanda ba Yahudawa ba da ‘’yan karnuka,’ wataƙila yana son ya nuna waɗanda su ne ainihi aka turo shi wurinsu. In akwai karnuka da kuma yara a gida, sai an ba yara abinci da farko kafin a ciyar da karnuka.
19-25 GA FABRAIRU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 16-17
“Ra’ayin Wa Kake da Shi?”
(Matta 16:21, 22) Daga loton nan Yesu ya soma bayyana wa almajiransa dole shi tafi Urushalima, shi sha wahala dayawa ga hannun datiɓai da manyan malamai da marubuta, a kashe shi, rana ta uku kuma ya tashi. 22 Amma Bitrus ya ɗauke shi, ya fara tsauta masa, ya ce, Allah shi sawwaƙa maka, Ubangiji: wannan ba za ya same ka ba daɗai.
(Matta 16:23) Amma ya waiwaya, ya ce ma Bitrus, Ka koma bayana, Shaiɗan: abin tuntuɓe ka ke a gareni; gama ba ka yi tattalin abin da ke na Allah ba, sai na mutane.
(Matta 16:24) Sa’annan Yesu ya ce wa almajiransa, Idan kowane mutum yana da nufi shi bi bayana, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki giciyensa, shi biyo ni.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 16:18) Kuma ina ce maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse kuma zan gina ikilisiyata; ƙyamaren Hades kuma ba za su rinjaye ta ba.
nwtsty na nazarin Mt 16:18
Kai ne Bitrus, a kan wannan dutse kuma: Kalmar Helenancin nan peʹtros a jinsin namiji tana nufin “ƙaramin dutse.” A ayar nan, an yi amfani da ita a matsayin suna (Bitrus), wato sunan Helenancin da Yesu ya ba wa Siman. (Yoh 1:42) Amma a jinsin mace na kalmar nan peʹtra tana nufin “babban dutse.” An yi amfani da kalmar nan ma a littafin Mt 7:24, 25; 27:60; Lu 6:48; 8:6; Ro 9:33; 1Ko 10:4; 1Bi 2:8. Bitrus bai ɗauki kansa a matsayin dutsen da Yesu zai gina ikilisiyarsa a kai ba domin ya rubuta a littafin 1Bi 2:4-8 cewa Yesu ne “dutse magabaci” da Allah ya zaɓa da kansa. Kuma manzo Bulus ma ya nuna cewa Yesu ne “tushi” da kuma dutse na ruhu. (1Ko 3:11; 10:4) Don haka, za mu iya cewa abin da Yesu yake nufi shi ne: ‘Kai da nake kira Bitrus da ke nufin Dutse, ka fahimci wane ne ainihin Kristi, “wato wannan dutsen,” wanda zai zama tushen da za a gina ikilisiyar Kirista.’
ikilisiya: Wannan ne lokacin na farko da kalmar Helenancin nan ek·kle·siʹa ta bayyana a Littafi Mai Tsarki. An samo ta ne daga kalmomi biyu na Helenanci, wato ek, da ke nufin “fita,” da kuma ka·leʹo, da ke nufin “a kira.” Kalmar tana nufin wasu rukunin mutane da aka kira su don su yi wani aiki. (Ka Duba Ƙarin Bayani.) A wannan ayar, Yesu yana magana ne a kan ikilisiyar Kirista da za a soma da ta ƙunshi shafaffun Kiristoci, kuma su ne “dutsen gini mai rai” da aka gina a kan “gida irin na ruhu.” (1Bi 2:4, 5, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) An yi amfani da kalmar Helenancin nan sosai a juyin Septuagint maimakon kalmar Ibrananci da ke nufin “ikilisiya,” domin yana wakiltar duka mutanen Allah. (K. Sh 23:3; 31:30) A littafin A. M. 7:38, an kira Isra’ilawan da suka fito daga Masar “ikilisiya.” Haka ma, Kiristocin da aka kira “daga cikin duhu” kuma aka ‘zaɓa daga cikin duniya’ ne “ikilisiya ta Allah.”—1Bi 2:9; Yoh 15:19; 1Ko 1:2.
(Matta 16:19) Kuma zan ba ka maƙullai na mulkin sama: dukan iyakar abin da ka ɗaure a duniya a ɗaure za ya zama a sama: kuma dukan abin da ka kwance a duniya a kwance za ya zama a sama.
nwtsty na nazarin Mt 16:19
maƙullin Mulkin sama: A cikin Littafi Mai Tsarki, duk waɗanda aka ba su maƙullin wani abu suna da babban gata ko kuma aiki. (1Lab 9:26, 27; Ish 22:20-22) Don haka, kalmar nan “maƙulli” tana wakiltar iko ko kuma gata. Bitrus ya yi amfani da wannan “maƙullin” don ya ba wa Yahudawa (A. M. 2:22-41) da Samariyawa (A. M. 8:14-17) da mutanen Al’umma (A. M. 10:34-38) ruhu mai tsarki da kuma gatan yin sarauta a Mulkin sama.
26 GA FABRAIRU–4 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 18-19
“Ka Guji Sa Kanka da Kuma Wasu Yin Tuntuɓe”
(Matta 18:6, 7) Amma dukan wanda za shi sa guda ɗaya a cikin ƙanƙananan nan masu-bada gaskiya gareni shi yi tuntuɓe, gwamma dai a gareshi a rataya ma wuyansa babban dutsen niƙa, a nutsadda shi cikin zurfin teku. 7 Kaiton duniya saboda dalilan tuntuɓe! Gama ba makawa dalilai su zo; amma kaiton wannan mutum wanda dalili ya zo ta wurinsa!
nwtsty na nazarin Mt 18:6, 7
babban dutsen niƙa: A zahiri yana nufin “dutsen da ake ɗaura wa jaki.” Irin wannan dutsen yana da girman kafa 4-5 kuma yana da nauyi sosai, shi ya sa jaki ne yake jan sa.
tuntuɓe: Kalmar Helenancin nan skanʹda·lon, da aka fassara zuwa “tuntuɓe,” tana nufin tarko; wasu sun ce shi ne tsinke da aka saka a jikin tarkon. Kuma yana iya nufin abin da aka saka don ya sa wani ya faɗi. A alamance, yana nufin wasu abubuwan da za su sa wani ya yi abin da bai kamata ba ko kuma ya yi zunubi. A littafin Mt 18:8, 9, an yi amfani da kalmar aikatau nan skan·da·liʹzo, da aka fassara zuwa “sa tuntuɓe,” kuma yana iya nufin “sa ka yi zunubi.”
nwtsty hotuna da bidiyo
Babban dutse
Ana amfani da wannan dutsen wajen niƙa hatsi ko kuma fitar da mān da ke cikin ’ya’yan zaitun. Wasu duwatsun za a iya jan su da hannu don ba su da nauyi, wasu kuma suna da nauyi sosai da sai jaki ne zai iya jan su. Wataƙila wannan dutsen iri ɗaya ne da babban dutsen da Filistiyawa suka tilasta wa Samson ya riƙa ja. (Alƙ 16:21) Ba a Isra’ila ne kawai aka san da wannan babban dutsen ba, amma har a wurare da dama a Daular Romawa.
Babba da Kuma Ƙaramin Dutse
Jaki ne zai iya jan babban dutsen da aka nuna a nan don a niƙa hatsi ko kuma ’ya’yan zaitun. Babban dutsen yana da girman kusan kafa 5 kuma ana iya amfani da ƙaramin dutse don a niƙa shi.
(Matta 18:8, 9) Kuma idan hannunka ko ƙafarka ya sa ka yi tuntuɓe, ka yanke ka yasda shi; gwamma a gareka ka shiga cikin rai da dungu ko gurgu, da a jefa ka cikin wuta ta har abada da hannunka biyu ko ƙafarka biyu. gāba da 9Kuma idan idonka ya sa ka ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar da shi: Gwamma a gareka ka shiga cikin rai da ido ɗaya, da a jefa ka cikin Jahannama ta wuta da idonka biyu.
nwtsty na nazarin Mt 18:9
Jahannama: an samo kalmar nan daga kalmar Helenancin nan geh hin·nomʹ, da ke nufin “Dutsen Hinnom,” kuma dutsen yana ta Yammaci da Kudancin Urushalima ta dā. (Ka kuma duba ƙarin bayani da ke B12, da taswirar da ke nuna “Urushalima da kuma Yankunanta.”) A zamanin Yesu, an mai da dutsen nan wurin ƙona shara, don haka kalmar nan “Jahannama” tana nufin wurin hallaka.
nwtstg Ƙarin Bayani
Jahannama
Shi ne sunan da ake kirar Dutsen Hinnom da ke Kudancin Urushalima ta dā a Helenanci. (Irm 7:31) An annabta cewa wurin zai zama wajen da za a riƙa zubar da gawawwaki. (Irm 7:32; 19:6) Babu inda aka ce wai za a riƙa zubar da dabbobi da kuma mutane da rai a Jahannama don a ƙona su har abada. Don haka, wurin ba ya wakiltar inda za a riƙa ƙona mutane a wuta har abada. Maimakon haka, Yesu da mabiyansa sun yi amfani da kalmar Jahannama ne don su kwatanta halaka mutane da za a yi a “mutuwa ta biyu.”—R. Yoh 20:14; Mt 5:22; 10:28.
(Matta 18:10) Ku yi hankali kada ku rena wani a cikin waɗannan ƙanƙanana; gama ina ce maku, cikin sama kullum mala’ikunsu suna duban fuskar Ubana wanda ke cikin sama.
nwtsty na nazarin Mt 18:10
duban fuskar Ubana: Ko kuma “samun zarafin zuwa wurin Ubana.” Mala’iku ne kawai suke iya ganin fuskar Allah domin suna da zarafin zuwa gaban Allah.—Fit 33:20.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 18:21, 22) Sa’annan Bitrus ya zo, ya ce masa, Ubangiji, so nawa ɗan’uwana za ya yi mani zunubi, in gafarta masa? har so bakwai? 22 Yesu ya ce masa, Ban ce maka, Har so bakwai ba; amma, Har bakwai bakwai sau saba’in.
nwtsty na nazarin Mt 18:22
bakwai bakwai sau saba’in: A zahiri yana nufin, “saba’in sau bakwai.” Wannan furucin Helenancin nan yana iya nufin “saba’in da kuma bakwai” (bakwai bakwai sau saba’in) ko kuma “saba’in sau bakwai” (ɗari huɗu da casa’in ke nan). A juyin Septuagint an yi amfani da kalmar Helenancin nan “bakwai bakwai sau saba’in” a littafin Fa 4:24. Amma ko da yaya mutane suka fahimci batun, maimaita lambar da aka yi tana wakiltar “har abada” ko kuma “babu iyaka.” Da Yesu ya gaya wa Bitrus bakwai sau saba’in da bakwai, yana gaya wa mabiyansa cewa suna bukatar su riƙa gafartawa babu iyaka. Amma littafin Talmud na Babiloniyawa (Yoma 86b) ya ce: “Idan mutum ya yi laifi har sau uku, a yafe masa amma idan ya yi na huɗun, kada a yafe masa.”
(Matta 19:7) Suka ce masa, Don menene fa Musa ya hukumta a bada takarda ta kisan aure, a sake ta kuma?
nwtsty na nazarin Mt 19:7
takarda ta kisan aure: Doka ta dokaci duk mutumin da yake so ya saki matarsa da ya rubuta takardar saki kuma ya nemi shawara daga wurin dattawa. An yin hakan ne don mutumin ya yi tunani sosai a kan abin da yake so ya yi. Ainihin dalili da ya sa aka kafa wannan Dokar shi ne don a rage yawan saki da mutane suke yi ba gaira ba dalili kuma a kāre mata. (K. Sh 24:1) Amma a zamanin Yesu, malaman addinai sun sa mutane suna kashe aure yadda suka ga dama. Ga abin da wani ɗan tarihi na ƙarni na farko mai suna Josephus, wanda Ba-farisi ne kuma ya kashe aurensa ya ce, za a iya kashe aure “a kan kowane irin dalili (kuma maza ne yawanci suke yin hakan).”
nwtsty hotuna da bidiyo
Takardar Kashe Aure
An rubuta wannan takardar kashe aure a shekara 71 ko kuma 72 bayan haihuwar Yesu a Aramaic. An samo shi ne a arewacin Wadi Murabbaat, wani waje a Hamadar Yahuda. Takardar ta ce, a ƙarni na shida sa’ad da Yahudawa suka soma tawaye, Yusufu ɗan Naqsan, ya saki Miriam, ’yar Jonathan, wanda yake zama a garin Masada.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 12:1-21) A cikin loton nan a kan ran assabbaci Yesu yana tafiya yana ratsa gonakin hatsi; almajiransa fa suna jin yunwa, suka soma karya zangarkun hatsi suna ci. 2 Amma Farisawa, sa’anda suka ga wannan, suka ce masa, ga almajiranka suna yin abin da ba ya halalta a yi bisa ran assabbaci ba. 3 Amma ya ce musu, Ba ku karanta abin da Dauda ya yi ba, sa’anda ya ji yunwa, da waɗanda ke tare da shi; 4 da ya shiga gidan Allah, ya ci gurasa ta ajiya, wadda cin ta ba ya halalta gare shi ba, ko waɗanda ke tare da shi, sai ga malamai kaɗai? 5 Ko ba ku karanta a cikin Attaurat ba, bisa ran assabbaci malamai a cikin haikali suna ɓata assabbaci, su kan kuwa barata? 6 Amma ina ce maku, wanda ya fi haikali girma yana nan. 7 Amma da kun san ma’anar wannan, Jinƙai ni ke biɗa, ba hadaya ba, da ku ku kaˉda marasa-laifi ba. 8 Gama Ɗan mutum ubangijin assabbaci ne. 9 Sai ya tashi daga can, ya shiga majami’arsu: 10 Sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. Suka tambaye shi, suka ce, Ya halalta a yi warkaswa a kan ran assabbaci? domin su sare shi. 11 Ya ce masu, Wane mutum ne daga cikinku, kadan yana da tunkiya daya, ita kuwa ta fada cikin rami a kan ran assabaci, ba za ya kama ta ya ciro ta ba? 12 Ina misalin fifikon darajar mutum fa bisa ga ta tunkiya! Domin wannan ya halalta a yi alheri a kan ran assabaci. 13 Sa’annan ya ce wa mutumin, miko hannunka. Ya mika; sai ya komo lafiyayye kamar wancan. 14 Amma Farisawa suka fita, suka yi shawara a kansa yadda za su hallaka shi. 15 Yesu kuwa da ya gane, sai ya janye daga can: mutane kuwa da yawa suka bi shi: shi kuwa ya warkar da su duka, 16 ya kuwa dokace su kada su bayyana ko wane ne shi: 17 domin a cika abin da aka faɗi ta bakin annabi Ishaya, cewa, 18 Ga barana wanda na zaɓa; ƙaunatacena wanda raina ya ji daɗinsa sarai: zan sa Ruhuna a bisansa, za shi furtar da shari’a ga al’ummai. 19 Ba za shi yi husuma ba, ba kuwa za shi ta da murya ba; Babu wanda za ya ji muryarsa cikin karabku 20 Rarraunan kara ba za ya karye ta ba, Atafa mai-hayaƙi kuma ba za ya ɓiche ta ba, har shi aike shari’a zuwa nasara. 21 A cikin sunansa kuma Al’ummai za su kafa bege.
Karatun Littafi Mai Tsarki:
(Matta 15:1-20) Sa’an nan wasu Farisawa da marubuta daga Urushalima suka zo wurin Yesu, suka ce, 2 Don me almajiranka suke ketare takalidai na tsofofi? Gama ba su kan wanke hannuwansu lokacin da suke cin gurasa ba. 3 Ya amsa ya ce musu, Don me ku kuma kuna ketaren dokar Allah saboda takalidinku? 4 Gama Allah ya ce, Ka ba da girma ga ubanka da uwarka: kuma, wanda ya zagi ko uba ko uwa, shi mutu lallai. 5 Amma ku kuna cewa, Dukan wanda za shi ce wa ubansa ko uwarsa, Moriya wadda za ka samu a gareni, an bayar ga Allah; 6 ba za shi bada girma ga ubansa ba. Kun maida maganar Allah wofi ke nan saboda takalidinku. 7 Ku masu-riya, daidai Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce, 8 Wannan al’umma tana girmamana da leɓunansu; Amma zuciyarsu tana nesa da ni. 9 Amma banza su ke yi mani sujada, koyarwa da su ke yi dokokin mutane ne. 10 Ya kirawo taron, ya ce masu, Ku ji, ku fahimta kuma: 11 Abin da ya shiga ta baki, ba shi ne ya kan ƙazantadda mutum ba; amma abin da ke fitowa daga baki, shi ke ƙazantadda mutum. 12 Sa’an nan almajiran suka zo, suka ce masa, ko ka sani Farisawa suka ji haushi, sa’an da suka ji wannan batu? 13 Amma ya amsa, ya ce, kowane dashe wanda Ubana na sama ba ya dasa ba, za a tumbuke shi. 14 Ku bar su: majayan hanya ne makafi. Idan kuwa makaho ya ja ma makaho gora, duka biyu za su faˉɗa cikin rami. 15 Bitrus ya amsa ya ce masa, Ka bayyana mana misalin nan. 16 Ya ce, Har kuwa ba ku da fahimi tukuna? 17 Ba ku gâne ba, iyakar abin da ya shiga ta baki, yakan wuce har ciki, akan iza shi zuwa waje? 18 Amma abubuwan da ke fita daga baki, daga zuciya su ke fitowa; su ne masu ƙazamtar da mutum. 19 Gama daga cikin zuciya miyagun tunani ke fitowa, kisan kai, zina, fasiƙanci, sata, shaidar zur, alfasha: 20 su ne masu ƙazantar da mutum: amma ci da hannuwa marasa-wanki ba shi ƙazantar da mutum ba.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 16:1-20) Farisawa da Saddukiyawa suka zo kuma, suna gwada shi, suna bida gareshi shi nuna musu alama daga sama. 2 Amma ya amsa, ya ce masu, sa’ad da maraice ta yi, kukan ce, Gari za ya yi sarari: gama sama ta yi jaja. 3 Da safe kuwa, Yau gari za ya ruɗe: gama sama ta yi jaja da gama-gira. Kun iya ku rarrabe fuskar sama; amma ba ku iya rarrabe alamun zamanu. 4 Tsara mai-mugunta mazinaciya tana biɗan alama; ba kuwa za a bata alama ba, sai alama ta Yunana. Ya bar su, ya tashi. 5 Almajiran suka zo wancan ketare, amma suka manta, ba su ɗauko gurasa ba. 6 Yesu kuwa ya ce masu, Ku lura, ku yi hankali kuma da yeast na Farisawa da na Saddukiyawa. 7 Suka yi bincike tsakanin junansu, suka ce, Domin ba mu ɗauko gurasa ba 8 Yesu kuwa domin ya gane tunaninsu ya ce, Ya ku masu ƙanƙantar bangaskiya, don menene kuke bincike a tsakanin junanku, domin ba ku da gurasa? 9 Har yanzu ba ku gaˉne ba, ba ku kuwa tuna da dunƙulen nan biyar ba, kwanduna nawa kuka tara daga baya? 10 Da kuma dunƙulen nan bakwai wajen dubu huɗun nan, kwando nawa kuwa kuka tara? 11 Me ya sa ba ku gane ba zancen gurasa ni ke yi maku? Amma ku yi hankali da yeast na Farisiyawa da na Sadukiyawa. 12 Sa’annan suka gane ba yeast na gurasa ne ya faɗa musu su yi hankali da shi ba, amma koyarwa ta Farisawa da ta Saddukiyawa. 13 To, da Yesu ya shiga ƙasar Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane ke cewa Ɗan Mutum yake?” 14 Suka ce, Waɗansu suna cewa Yohanna Mai-yin baftisma ne; waɗansu, Iliya; waɗansu kuma, Irmiya ne, ko ɗaya daga cikin annabawa. 15 Ya ce musu, Amma ku kuna ce da ni wanene? 16 Siman Bitrus ya amsa, ya ce, Kai Kristi ne, Ɗan Allah mai-rai. 17 Yesu ya amsa, ya ce masa, Mai-albarka ne kai, Siman ɗan Yunana: gama nama da jini ba ya bayyana maka wannan ba, amma Ubana wanda ke cikin sama. 18 Kuma ina ce maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse kuma zan gina ikilisiyata; ƙyamaren Hades kuma ba za su rinjaye ta ba. 19 Kuma zan ba ka wuƙublai na mulkin sama: dukan iyakar abin da ka ɗaure a duniya a ɗaure za ya zama a sama: kuma dukan abin da ka kwance a duniya a kwance za ya zama a sama. 20 Sa’an nan ya dokaci almajiran kada su faɗa wa kowa shi Kristi ne.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 18:18-35) Hakika ina ce maku, Dukan abin da za ku ɗaure a duniya, a ɗaure za su zama a sama: kuma dukan abin da za ku kwance a duniya, a kwance za su zama a sama. 19 Kuma ina ce maku, idan guda biyu a cikinku za su yi muwafaka a duniya a kan abin da za su roƙa duka, Ubana da ke cikin sama za ya yi masu shi. 20 Gama wurin da mutum biyu ko uku sun taru cikin sunana, nan ni ke a tsakiyarsu. 21 Sa’annan Bitrus ya zo, ya ce masa, Ubangiji, so nawa ɗan’uwana za ya yi mani zunubi, in gafarta masa? har so bakwai? 22 Yesu ya ce masa, Ban ce maka, Har so bakwai ba; amma, Har bakwai bakwai so saba’in. 23 Domin wannan za a kwatanta mulkin sama da wani sarki, wanda yana so ya yi lissafi da bayinsa. 24 Sa’anda ya soma lissafi, aka kawo masa wani, wanda ya ke mabarcinsa na talent dubu goma. 25 Amma da shi ke ba shi da abin biya, ubangijinsa ya umurta a sayasda shi, da matatasa, da ’ya’yansa, da dukan abin da ya ke da shi, a biya. 26 Bawan nan fa ya faɗi ya yi masa sujada, ya ce, Ubangiji, ka hanƙure mani, ni kuwa ni biya ka duka. 27 Ubangijin bawan nan, domin ya ji juyayi, ya kwance shi, ya gafarta masa bashin. 28 Amma wannan bawa ya fita, ya iske wani abokin bautansa, wanda shi ke mabarcinsa a bakin sule ɗari: ya damƙe shi, ya kama shi a makogoro, ya ce, Ka biya bashinka. 29 Shi abokin bautansa fa ya faɗi ya yi ta roƙonsa, ya ce, Ka hanƙure mani, ni kuwa ni biya ka. 30 Amma ya ƙi: ya kuwa tafi ya jefa shi cikin kurkuku, har sai ya biya abin da ke a kansa. 31 Sa’an da abokan bautansa fa suka ga abin da aka yi, zuciyarsu ta ɓaci kwarai, suka zo, suka fada wa ubangijinsu dukan abin da aka yi. 32 Sa’annan ubangijinsa ya kirawo shi, ya ce masa, Kai mugun bawa, na gafarta maka dukan bashin nan, domin ka roƙe ni: 33 ba ya kamata gareka ba kai kuma ka jiƙan abokin bautanka, kamar yadda ni na jiƙanka? 34 Ubangijinsa kuwa ya yi fushi, ya baˉshe shi ga masu-wulakantawa, har shi biya dukan abin da ke kansa. 35 Haka nan kuma Ubana na sama za ya yi muku, idan cikin zuciyarku ba ku gafarta wa ’yan’uwanku.