Littattafan da Aka Ɗauko Bayanai Daga Cikinsu a Littafin Taro don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu
5-11 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 20-21
“Duk Wanda Yake So Ya Zama Babba A Cikinku, Dole Ne Ya Zama Mai Yi Wa Sauran Hidima”
(Matta 20:3) Wajen sa’a ta uku ga yini ya fita kuma, ya ga waɗansu suna tsayen banza cikin kasuwa;
nwtsty hotuna da bidiyo
Cikin Kasuwa
Kamar hoton da aka nuna a nan, wasu kasuwanni a bakin titi suke. ’Yan kasuwa sukan saka kayayyakin sayarwa da yawa a kan titi har su tare hanyar wucewa. Mutane a birnin sukan je su sayi wasu abubuwa kamar tukunya da kofuna masu tsada da kuma kayan miya. Tun da babu firiji a lokacin, mutanen suna zuwa kasuwa kusan kowace rana. A kasuwa ne mutane suke jin sabon labari daga wurin baƙi da suka zo cin kasuwa kuma a wajen ne yara suke yin wasa. Ban da haka, a kasuwa ne leburori suke tsayawa don a ɗauke su aiki. Yesu ya warkar da mara lafiya a kasuwa kuma Bulus ma ya yi wa’azi a cikin kasuwa. (A. M. 17:17) Amma malamai da Farisawa masu girman kai suna son mutane su riƙa daraja su da kuma gaishe su a irin wuraren nan.
(Matta 20:20, 21) Sa’an nan uwar ’ya’yan Zabadi ta zo wurinsa tare da ’ya’yanta, tana yi masa sujada, tana roƙon wani abu a gareshi. 21Ya kuwa ce mata, Me ki ke so? Ta ce masa, Ka umurta ’ya’yan nan nawa biyu su zauna, ɗaya ga hannun damanka, ɗaya ga hannun hagunka, cikin mulkinka.
nwtsty na nazarin Mt 20:20, 21
uwar ’ya’yan Zabadi: Ita ce mahaifiyar Yaƙubu da Yohanna. A littafin Markus, Yaƙubu da Yohanna ne da kansu suka gaya wa Yesu hakan. Su ne suka gaya wa mahaifiyarsu Salome ta je ta sami Yesu da wannan maganar kuma wataƙila ita ’yar’uwar mahaifiyar Yesu ce.—Mt 27:55, 56; Mk 15:40, 41; Yoh 19:25.
ɗaya ga hannun damanka, ɗaya ga hannun hagunka: Dukan hannayen na wakiltar babban gata da kuma iko amma a yawancin lokaci, an fi ɗaukan hannun dama da muhimmanci sosai.—Za 110:1; A. M. 7:55, 56; Ro 8:34.
(Matta 20:25-28) Amma Yesu ya kira su wurinsa, ya ce, Kun sani sarakunan Al’ummai suna nuna musu sarauta, manyansu kuma suna gwada musu iko. 26 Ba haka za ya zama a cikinku ba: amma dukan wanda yake so shi zama babba a cikinku, bawanku za ya zama; 27 kuma dukan wanda yake so shi zama nafari a cikinku, bawanku za ya zama: 28 kamar yadda Ɗan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu, shi ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.
nwtsty na nazarin Mt 20:26, 28
bawa: Ko “mai hidima.” Littafi Mai Tsarki yana yawan amfani da kalmar Helenancin nan di·aʹko·nos don ya kwatanta mutumin da yake yi wa mutane hidima da yardan rai. Ana amfani da kalmar don a kwatanta Yesu Kristi (Ro 15:8), ko ma’aikata ko bayin Kristi (1Ko 3:5-7; Kol 1:23), da masu hidima (Fib 1:1; 1Ti 3:8), da masu aikin gida (Yoh 2:5, 9) da kuma ma’aikatan gwamnati (Ro 13:4).
ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu: Ko “ba domin a yi masa hidima ba, amma domin ya yi wa waɗansu hidima.”
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 21:9) Taro fa da ke tafiya gabansa, da na biye da shi, suka tada murya, suka ce, Hosanna ga ɗan Dawuda: Mai-albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji; Hosanna cikin mafiya ɗaukaka!
nwtsty na nazarin Mt 21:9
Hosanna: Kalmar Helenancin nan tana nufin “ceto muke roƙa” ko kuma “ceto, don Allah.” Ana amfani da kalmar nan wajen roƙan Allah don ceto ko nasara. Tana kuma nufin “muna roƙo, Allah ka ceci.” Da shigewar lokaci, sai aka soma amfani da shi a addu’a da kuma waƙar yabo. Za mu iya ganin yadda ake kiran kalmar a Ibrananci a littafin Za 118:25 kuma ana yawan amfani da kalmar a lokacin Idin Ƙetarewa. Shi ya sa taron jama’ar suka ambaci hakan a wannan lokacin. Allah ya amsa addu’ar cewa ya ceci Ɗan Dauda sa’ad da ya ta da Yesu daga mutuwa. A littafin Mt 21:42, Yesu da kansa ya yi ƙaulin littafin Za 118:22, 23 kuma ya ce yana nuni ne ga Almasihu.
Ɗan Dauda: Wannan furucin yana nuna cewa Yesu zuriyar Dauda ne kuma shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa.
(Matta 21:18, 19, Littafi Mai Tsarki) Da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa. 19 Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.
jy 244 sakin layi na 4-6
Ya Yi Amfani da Itacen Ɓaure Don Ya Koyar da Darasi Game da Bangaskiya
Me ya sa Yesu ya sa itacen ya bushe? Ya faɗi dalilin sa’ad da ya ce: “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku. Kome kuka roƙa da addu’a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.” (Matta 21:21, 22, LMT) A ayoyin nan, Yesu yana maimaita darasin da ya taɓa koya musu cewa bangaskiya za ta iya ɗaga dutse.—Matta 17:20.
Da Yesu ya sa itacen ya bushe, ya nuna wa mabiyansa cewa suna bukatar su kasance da bangaskiya. Ya ce: “Dukan iyakar abin da kuke addu’a kuna roƙo kuma, ku ba da gaskiya kun rigaya kun karɓa, za ku samu fa.” (Markus 11:24) Wannan darasi ne mai muhimmanci! Manzannin suna bukatar su kasance da bangaskiya sosai musamman don jarrabawar da za su fuskanta a nan gaba. Ban da batun bangaskiya, akwai wani abin da Yesu yake koya wa mabiyansa.
Kamar wannan itacen ɓauren, al’ummar Isra’ila suna munafurci. Suna da dangantaka ta kud da kud da Allah kuma suna nuna cewa suna bin dokar da aka bayar ta hannun Musa. Amma al’ummar ba su kasance da bangaskiya ba kuma ba sa ba da ’ya’ya masu kyau. Sun ƙi amincewa da Ɗan Allah! Saboda halinsu ne Yesu ya nuna abin da zai faru da su a ƙarshe.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 20:1-19) “Gama mulkin sama yana kama da mutum da shi ke ubangida, wanda ya fita tun da sassafe garin ya yi ijara da ma’aikata su zo gonarsa. 2 Sa’an da ya shirya da ma’aikata a kan sule sule kowace rana, ya aike su cikin gonarsa. 3 Wajen sa’a ta uku ga yini ya fita kuma, ya ga waɗansu suna tsaye banza cikin kasuwa; 4 ga waɗannan kuma ya ce, Ku kuma ku tafi cikin gona, iyakar abin da wajaba, ni ba ku. Suka kama hanya. 5 Ya sake fita wajen sa’a ta shidda, da sa’a ta tara ga yini kuma, ya yi irin na dā. 6 Wajen sa’a ta goma sha ɗaya ga yini kuma ya fita, ya iske waɗansu a tsaye; ya ce musu, Don me kuke yini a nan tsaye banza? 7 Suka ce masa, Domin babu wanda ya yi ijara da mu. Ya ce musu, Ku kuma ku tafi cikin gona. 8 Sa’and da maraice ta yi, ubangijin gona ya ce wa wakilinsa, kirawo ma’aikatan, ka biya masu hakinsu, ka soma da na ƙarshe har zuwa na fari. 9 Sa’and da waɗannan suka zo da aka yi ijara da su wajen sa’a ta goma sha ɗaya, kowane ya karɓi sule guda. 10 Sa’and da na fari suka zo, suna tsammani abin da za su karɓa ya fi haka; amma su ma, kowane mutum ya karɓi sule guda. 11 Sa’and da suka karɓa, suka yi wa ubangiji gunaguni, 12 suka ce, waɗannan na ƙarshe sa’a guda kawai suka yi, har ka daidaita su da mu, mu da muka sha wahalar yini da zafin rana. 13 Amma ya amsa, ya ce wa ɗaya a cikinsu, aboki, ban zalunce ka ba: ba ka shirya da ni a kan sule guda ba? 14 Ɗauki abin da ke naka, ka yi tafiyarka; nufina ne in ba na ƙarshen nan daidai da kai. 15 Ba halal ne ba a gareni in yi abin da na nufa da abina? Ko kuwa idonka mugu ne saboda ni nagari ne? 16 Hakan nan na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma na ƙarshe. 17 Yesu yana cikin tafiya za shi Urushalima, sai ya ɗauki almajiran goma sha biyu, ya ware su waje ɗaya, a kan hanya kuwa ya ce musu, 18 Ga shi za mu Urushalima; kuma za a ba da Ɗan mutum ga hannun manyan malamai da marubuta; za su hukumta masa mutuwa, 19 su bashe shi ga Al’ummai domin su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su giciye shi kuma: rana ta uku kuma za a tashe shi.”
MARCH 12-18
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 22-23
“Ku Riƙa Bin Umurnin Dokoki Biyu Mafi Girma”
(MATTA 22:36-38) Malam, wace ce babbar doka a cikin Attaurat? 37 Ya ce masa, Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. 38 Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari.
nwtsty na nazarin Mt 22:37
zuciya: Idan aka yi amfani da ita a alamance tana nufin mutumin gabaki ɗaya. Amma idan aka yi amfani da wannan kalmar tare da “rai” da “azanci,” tana nufin wani abu ne takamamme kamar yadda mutum yake ji da kuma abubuwan da yake sha’awa. Waɗannan kalmomi uku da aka yi amfani da su a nan (zuciya da rai da kuma azanci) suna nufin abu ɗaya; ana amfani da su tare don a nanata yadda muke bukata mu ƙaunaci Allah sosai.
rai: Ko “dukan gaɓoɓin mutum.”
azanci: Yana nufin tunaninmu. Dole ne mutum ya yi amfani da azancinsa ko kuma tunaninsa kafin ya koyi abubuwa game da Allah kuma ya ci gaba da ƙaunarsa. (Yoh 17:3; Ro 12:1) A rubutun Ibrananci na asali, an yi amfani da kalaman nan, ‘zuciya da rai da kuma ƙarfi’ a littafin K. Sh 6:5. Amma a Linjilar da Matta ya rubuta a yaren Helenanci, an yi amfani da “azanci” maimakon “ƙarfi.” Akwai dalilai da yawa da suka sa aka yi amfani da kalmomi dabam-dabam wajen nuni ga abu ɗaya. Na farko, ko da yake babu kalmar nan “azanci” a Ibrananci, amma ma’anarsa ɗaya ne da kalmar nan “zuciya.” Idan aka yi amfani da kalmar nan a alamance, tana nufin mutum gabaki ɗaya da tunaninsa da halinsa da ra’ayinsa da kuma yadda yake ji. (K. Sh 29:4; Za 26:2; 64:6; ka duba sakin layi na baya da ya yi magana a kan zuciya.) Don haka, a duk inda aka yi amfani da kalmar nan zuciya a “Ibrananci,” juyin Septuagint na Helenanci yakan yi amfani da kalmar nan da ta yi daidai da ita, wato “azanci.” (Fa 8:21; 17:17; Mis 2:10; Ish 14:13) Wani dalili kuma da wataƙila ya sa Matta ya yi amfani da kalmar Helenancin nan “azanci,” wato tunani, maimakon “ƙarfi” sa’ad da yake ƙaulin K. Sh 6:5 shi ne, kalmar Ibranancin nan “ƙarfi” ta ƙunshi ƙarfi na zahiri da kuma azanci na mutum. Ko da mene ne dalilin, yadda aka bayyana ma’anar kalmar Helenancin nan “azanci,” wato tunani, da kuma na Ibranancin nan “ƙarfi” ya taimaka mana mu san dalilin da ya sa wataƙila marubutan Linjila suka yi ƙaulin Kubawar Shari’a ba tare da yin amfani da ainihin kalmar da take wurin ba.
(Matta 22:39) Wata kuma ta biyu mai kamaninta ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.
nwtsty na nazarin Mt 22:39
Ta biyu: A Mt 22:37, an rubuta amsar da Yesu ya ba wa Bafarisin nan, kuma Yesu bai ba da amsar kawai ba amma ya yi ƙaulin doka ta biyu (Le 19:18), don ya koyar da cewa dokoki biyun suna da alaƙa da juna kuma ya nuna cewa a kan dokoki biyun nan ne duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.—Mt 22:40.
maƙwabci: Kalmar Helenancin nan “maƙwabci” (a zahiri “wanda yake kusa”) ba ta nufin waɗanda suke zama kusa da kai kawai, amma ta haɗa da duk wani mutum da kuke sha’ani ko ma’ammala da shi.—Lu 10:29-37; Ro 13:8-10.
(Matta 22:40) “Ga waɗannan doka biyu dukan Attaurat da Annabawa suke ratayawa.”
nwtsty na nazarin Mt 22:40
doka . . . annabawa: ‘Dokar’ tana nuni ne ga littattafan Farawa zuwa Kubawar Shari’a. ‘Annabawan’ yana nuni ne ga littattafan annabci da ke Nassosin Ibrananci. Amma idan aka ambaci kalmomin nan tare, hakan yana nufin duka Nassosin Ibrananci.—Mt 7:12; 22:40; Lu 16:16.
ratayawa: An yi amfani da kalmar aikatau na Helenancin nan “a rataye” a alamance da ke nufin “dogara ga ko kuma jingina bisa.” Yesu ya nuna cewa Dokar, wato dokoki goma har da dukan Nassosin Ibrananci an kafa su ne bisa ƙauna.—Ro 13:9.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 22:21) “Suka ce masa, Na Kaisar ne. Sa’an nan ya ce musu, Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.”
nwtsty na nazarin Mt 22:21
Kaisar abin da ke na Kaisar: Amsar da Yesu ya bayar a nan da kuma abin da ke Mk 12:17 da Lu 20:25, su ne kawai wuraren da Yesu ya yi magana game da sarkin Roma. “Abin da ke na Kaisar” ya ƙunshi kuɗin da muke biya don wasu abubuwan da gwamnati take tanadarwa da daraja da muke ba su daidai wadaida.—Ro 13:1-7.
Allah kuma abin da ke na Allah: Hakan ya ƙunshi ibadar da mutum yake yi da zuciya ɗaya da ƙaunar Allah da yake yi sosai da kuma bin dukan umurnin Allah.—Mt 4:10; 22:37, 38; A. M. 5:29; Ro 14:8.
(Matta 23:24, Littafi Mai Tsarki) “Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!”
nwtsty na nazarin Mt 23:24
kukan tace sauro, ku haɗiye raƙumi: Ƙwaro da rakumi suna cikin dabbobi mafi ƙanƙanta da kuma manya da ba su da tsarki a wurin Isra’ilawa. (Le 11:4, 21-24) Yesu ya yi amfani da kwatancin abin da ba zai yiwu a zahiri ba don ya nuna cewa malaman addinai sukan tace ruwan anab da suke sha don kada ƙwaro ya shiga kuma su zama marasa tsarki. Amma sukan yi banza da abubuwa masu muhimmanci na Dokar, wadda yake kama da haɗiye rakumi.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 22:1-22) Yesu ya amsa ya koma yi musu zance da misalai, ya ce, 2 Mulkin sama yana kama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa bikin anganci, 3 ya kuma aike bayinsa su kira waɗanda aka faɗa musu bikin angonci: suka ƙi zuwa. 4 Ya sāke aika waɗansu bayi, ya ce, Ku faɗa wa waɗanda an kira, Ga shi, na shirya abinci: an yanka shanuna da kiyayayyuna, abubuwa duka a shirye yake: ku zo bikin angonci. 5 Amma suka wāƙala shi, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya wajen cinikinsa: 6 sauran suka kama bayinsa, suka yi musu wulakanci, kāna suka kashe su. 7 Amma sarkin ya hasala; ya aike rundunansa, ya hallakar da waɗannan masu-kisa, ya ƙone garinsu. 8 Sa’an nan ya ce wa bayinsa, Bikin angoncin shiryayye ne, amma wadanda aka gayyace su ba su cancanta ba. 9 Ku tafi fa zuwa mararrabar hanyoyi, iyakar waɗanda kuka iske, ku kirawo su zuwa bikin angoncin. 10 Waɗannan bayi fa suka tafi zuwa cikin hanyoyi, suka tattara dukan iyakar waɗanda suka iske, da munana da masu-kyau: bikin angoncin kuwa ya cika da baƙi. 11 Amma sa’anda da sarki ya shigo garin duban baƙin, ya ga wani mutum a wurin, wanda ba shi sanye da rigar angonci: 12 ya kuwa ya masa, Aboki, kaka ka shigo wurin nan ba ka da rigar angonci? Sai ya yi shiru. 13 Sa’an nan sarki ya ce wa bayinsa, Ku daure shi hannu da kafa, ku jefar da shi waje cikin baƙin duhu; can za a yi ta kuka da cizon haƙora. 14 Gama kirayayyu da yawa suke, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne. 15 Sa’an nan Farisawa suka tafi, suka yi shawara yadda za su yi masa tarko cikin zancensa. 16 Suka aike masa almajiransu, tare da Hirudiyawa, suka ce, Malam, mun sani kai mai-gaskiya ne, kana kuwa koyarwar tafarkin Allah cikin gaskiya, ba ka kula da kowa ba: gama ba ka tāran mutane ba. 17 Ka faɗa mana fa, me ka gani? Halal ne a ba da gandu ga Kaisar, ko kuwa ba haka ba? 18 Amma Yesu ya gane muguntarsu, ya ce, don me kuke gwada ni, ku munafukai? 19 Nuna mini kuɗin gandun. Suka kawo masa kuɗin. 20 Ya ce masu, Wannan sura da rubutun nan na wane ne? 21 Suka ce masa, Na Kaisar ne. Sa’an nan ya ce musu, Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah. 22 Sa’anda suka ji, suka yi mamaki, suka bar shi, suka kama hanyarsu.
19-25 GA MARIS
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 24
“Ka Ci gaba da Yin Ƙwazo a Wannan Kwanaki na Ƙarshe”
(Matta 24:12) Saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.
it-2 279 sakin layi na 6
Ƙauna
Ƙaunar da Muke da Shi Za Ta Iya Yin Sanyi. Sa’ad da Yesu yake gaya wa almajiransa abubuwan da za su faru a nan gaba, ya gaya musu cewa ƙaunar (a·gaʹpe) mutanen da ke da’awa cewa suna bauta wa Allah za ta yi sanyi. (Mt 24:3, 12) Manzo Bulus ya ce ɗaya daga cikin alamun kwanakin ƙarshe shi ne, mutane za su zama “masu son kuɗi.” (2Ti 3:1, 2) Shi ya sa zai iya yi wa mutum wuya ya bi ƙa’idodin da suka dace kuma ƙaunarsa za ta iya yin sanyi. Hakan ya nuna cewa yana da muhimmanci mutum ya ci gaba da ƙarfafa ƙaunarsa ta wajen karanta Kalmar Allah da yin bimbini da kuma bin abin da ya karanta.—Afi 4:15, 22-24.
(Matta 24:39) Ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su duka; hakanan kuma bayanuwar Ɗan mutum za ta zama.
(Matta 24:44) Ku fa ku zama da shiri: gama cikin sa’ar da ba ku sa tsammani ba Ɗan mutum yana zuwa.
jy 259 sakin layi na 5
Manzannin Suna So Su San Alamar Bayyanuwar Kristi
Ya ce mabiyansa suna bukatar su yi tsaro kuma su kasance a shirye. Yesu ya yi amfani da wani kwatanci don ya nuna musu dalilin da ya sa ya gaya musu hakan. Ya ce: ‘Amma dai ku sani, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida. Don haka, ku ma sai ku zauna da shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.’—Matta 24:43, 44, Littafi Mai Tsarki.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 24:8) Amma dukan waɗannan al’amura mafarin wahala ne.
nwtsty na nazarin Mt 24:8
wahala: Kalmar Helenancin nan tana nufin wahalar da mace take sha a lokacin haihuwa. Ko da yake a ayar nan an yi amfani da kalmar don a kwatanta wahalar da mutane suke sha gabaki ɗaya, kalmar tana kuma nuna cewa kamar yadda zafin haihuwa yake, haka ma matsaloli da wahala za su yi tsanani kafin ma a fara ƙunci mai girma da aka ambata a littafin Mt 24:21.
(Matta 24:20) Ku yi addu’a fa kada gudunku ya zama a cikin damuna, ko kuwa a ran assabbaci:
nwtsty na nazarin Mt 24:20
a cikin damuna: Yana da wuya mutum ya yi tafiya ko ya sami abinci da masauƙi a lokacin da ake ruwan sama da kuma sanyi.—Ezr 10:9, 13.
a ran assabbaci: A Yahuda, dokar Assabbaci ta haramta mutane daga yin wasu abubuwa, shi ya sa zai yi wa mutum wuya ya yi tafiya mai nisa ko ya ɗau kaya a ranar Assabbaci. Ban da haka ma, ana rufe kofar garin a ranar Assabbaci—Ka duba A. M. 1:12 da kuma Ratayen da ke B12.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 24:1-22) Yesu ya fita daga haikali, yana cikin tafiya; sai almajiransa suka zo wurinsa domin su gwada masa ginegine na haikali. 2 Amma ya amsa, ya ce masu, Ba ku ga waɗannan abubuwa duka ba? hakika, ina ce maku, Ba za a rage wani dutse bisa wani, da ba za a rushe ba. 3 Yana nan yana zaune bisa dutsen Zaitun, sai almajiran suka zo wurinsa waje ɗaya, suka ce, Ka faɗa mana, yaushe waɗannan abubuwa za su zama? me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani? 4 Yesu ya amsa, ya ce masu, Ku yi lura kada kowa ya ɓashe ku. 5 Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, su ce, Ni Kristi ne; za su kuwa ɓadda mutane da yawa. 6 Kuma za ku ji labarin yaƙoƙi da zizar yaƙi: ku lura kada hankalinku ya tashi: gama waɗannan al’amura dole za su faru; amma matuƙa ba ta yi ba tukuna. 7 Gama al’umma za ta tasar wa al’umma, mulki kuma za ya tasa wa mulki: za a yi yunwa da rayerayen duniya wurare dabam dabam. 8 Amma dukan waɗannan al’amura mafarin wahala ne. 9 Sa’annan za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana. 10 Sa’annan mutane dayawa za su yi tuntuɓe, za su bada juna, za su ƙi juna kuma. 11 Kuma masu ƙaryan annabci da yawa za su tashi, su ɓad da mutane da yawa. 12 Saboda yawaita da mugunta za ta yi kuma, ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi. 13 Amma wanda ya jimre har matuƙa shi ne za ya tsira. 14 Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo. 15 Sa’anda fa kun ga ƙyamar lalata, wadda aka ambace ta ta bakin annabi Daniyelu, tana tsaye a cikin tsatsarkan wuri (bari mai-karantawa shi fahimta), 16 sa’annan waɗanda ke cikin Yahudiya su gudu zuwa duwatsu: 17 Wanda yake a kan bene kada ya sauko garin shi kwashe kayan da ke cikin gidansa: 18 kuma wanda ke cikinsaura kada shi komo garin shi amso mayafinsa. 19 Amma kaitonsu, masu-juna biyu da masu-bada mama cikin waɗannan kwanaki! 20 Ku yi addu’a fa kada gudunku ya zama a cikin damuna, ko kuwa a ran assabbaci: 21 gama sa’annan za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba dadai. 22 Kuma da ba domin an gajartar da waɗannan kwanaki ba, da ba mai-rai da za ya tsira ba: amma sabili da zaɓaɓɓu za a gajartar da su.
26 GA MARIS–1 GA AFRILU
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 25
“Ku Yi Tsaro”
(Matta 25:1-6) Sa’annan za a iske mulkin sama yana kama da budurwai goma, waɗanda suka ɗauki fitilunsu, suka fita garin su tarbi ango.2 Biyar daga cikinsu marasa-azanci ne, biyar masu-hikima ne. 3 Gama marasa-azancin nan, da suka ɗauki fitilunsu, ba su ɗauka duk da mai ba: 4 amma masu-hikima suka ɗauki mai cikin santulansu tare da fitilunsu. 5 Ana nan sa’anda ango ya yi jinkiri, dukansu suka yi rurrumi, suka yi barci. 6 Amma da tsakiyar dare sai aka ji murya, Ga ango! Ku fito, ku tarbe shi.
(Matta 25:7-10) Sa’an nan dukan waɗannan budurwai suka tashi, suka yi ta gyartan fitilunsu. 8 Marasa-azancin suka ce wa masu-hikiman, Ku ɗibo mana daga cikin manku: gama fitilunmu suna mutuwa. 9 Amma masu-hikiman suka amsa, suka ce, Wataƙila ba za ya ishe mu duk da ku ba: gwamma ku tafi wurin masu-sayarwa, ku sayo ma kanku. 10 Sa’anda suna cikin tafiya garin saye, ango ya zo; waɗanda suna nan a shirye suka shiga tare da shi wurin anganci: aka rufe ƙofa.
(Matta 25:11, 12) Daga baya kuma waɗancan budurwai suka zo, suka ce, Ubangiji, Ubangiji, ka buɗe mana. 12 Amma ya amsa, ya ce, Hakika, ina ce muku, Ban san ku ba.
Neman Abubuwa Masu Tamani
(Matta 25:31-33) Amma sa’an da Ɗan mutum za ya zo cikin darajarsa, da dukan mala’iku tare da shi, sa’annan za ya zauna bisa kursiyin darajarsa: 32 a gabansa kuma za a tattara dukan al’ummai: shi kuwa za ya rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi yakan rarraba tumaki da awaki: 33 kuma za ya sanya tumaki ga hannun damansa, amma awaki ga hagu
(Matta 25:40) Sarki kuma za ya amsa, ya ce masu, Hakika ina ce muku, Da shi ke kuka yi wannan ga guda ɗaya a cikin waɗannan ’yan’uwana, ko waɗannan mafiya ƙanƙanta, ni kuka yi wa.
Karatun Littafi Mai Tsarki
(Matta 25:1-23) Sa’annan za a iske mulkin sama yana kama da budurwai goma, waɗanda suka ɗauki fitilunsu, suka fita garin su tarbi ango. 2 Biyar daga cikinsu marasa-azanci ne, biyar masu-hikima ne. 3 Gama marasa-azancin nan, da suka ɗauki fitilunsu, ba su ɗauka duk da mai ba: 4 amma masu-hikima suka ɗauki mai cikin santulansu tare da fitilunsu. 5 Ananan sa’anda ango ya yi jinkiri, dukansu suka yi rurrumi, suka yi barci. 6 Amma da tsakiyar dare sai aka ji murya, Ga ango! Ku fito, ku tarbe shi. 7 Sa’annan dukan waɗannan budurwai suka tashi, suka yi ta gyartan fitilunsu. 8 Marasa-azancin suka ce wa masu-hikiman, Ku ɗibo mana daga cikin manku: gama fitilunmu suna mutuwa. 9 Amma masu-hikiman suka amsa, suka ce, Wataƙila ba za ya ishe mu duk da ku ba: gwamma ku tafi wurin masu-sayarwa, ku sayo ma kanku. 10 Sa’anda suna cikin tafiya garin saye, ango ya zo; waɗanda suna nan a shirye suka shiga tare da shi wurin anganci: aka rufe ƙofa. 11 Daga baya kuma waɗancan budurwai suka zo, suka ce, Ubangiji, Ubangiji, ka buɗe mana. 12 Amma ya amsa, ya ce, Hakika, ina ce muku, Ban san ku ba. 13 Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba. 14 Gama yana kama da mutum, da za shi wata ƙasa, ya kira bayinsa, ya damƙa musu dukiyarsa. 15 Ga wani ya ba da talent biyar, ga wani kuma biyu, ga wani ɗaya; kowa ya ba shi gwargwadon iyawarsa; kāna ya yi tafiyarsa. 16 Nan da nan shi wanda ya karɓi talent biyar ya tafi ya yi ciniki da su, ya ci ribar waɗansu talent biyar. 17 Hakanan kuma shi wanda ya karɓi biyu, ya ci ribar waɗansu biyu. 18 Amma shi wanda ya karɓi ɗayan, ya je ya yi haƙi a ƙasa, ya ɓoye azurfar ubangijinsa. 19 Ananan bayan da aka jima, ubangijin waɗannan bayi ya zo, ya yi lissafi da su. 20 Wanda ya karɓi talent biyar ya zo ya kawo waɗansu talent biyar kuma, ya ce, Ubangiji, talent biyar ka ba ni: ga shi, na sami waɗansu talent biyar riba. 21 Ubangijinsa ya ce masa, Madalla, kai bawan kirki, mai-aminci: ka yi aminci cikin matsaloli kaɗan, zan sanya ka a bisa mai-yawa: ka shiga cikin farin zuciyar ubangijinka. 22 Shi kuma wanda ya karɓi talent biyu, ya zo ya ce, Ubangiji, talent biyu ka ba ni: ga shi, na sami waɗansu talent biyu riba. 23 Ubangijinsa ya ce masa, Madalla, kai bawan kirki mai-aminci; ka yi aminci cikin matsaloli kaɗan, ni sanya ka bisa mai-yawa: ka shiga cikin farin zuciyar ubangijinka.